*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)
*33*
*Wattpad@ayshatmadu*
"Banso tuna wad'annan mutane ba a rayuwata, naso a ce yanda nake ganinsu a titi ya tsaya a haka, ba tare da sun san mu ko su waye ba. Sune wad'anda na tsana tun ina k'arami a rayuwata."
Hawaye ne ya gangaro mashi daga cikin idanunshi, wanda bai tunanin zai iya dakatar dasu ba.
Gaba d'aya d'akin kowa shiru yayi yana jin abinda ke fitowa daga bakin Yaya Muhammad.
Abdallah ya fito daga cikin tsatson lamid'o wanda bana son tunasu.
Asalinsu sun fito daga garin jigawa, fulanin jigawa ne, sai dai mahaifinsu mai suna mallam Ashiru Lamid'o ya shigo garin kano cirani, yayin daya taho da uwargidanshi mai suna Adama suna kiranta da Goggo nan garin suke da zama.
Tun yana zaune gidan haya, yazo ya gina nashi gidan babban gidane mai d'akuna da yawa saboda 'ya'yanshi maza idan sunyi aure.
Goggo ta kasance tana da 'ya'ya biyar uku maza biyu mata, Baba Salisu shine babba, sai Baba Nasiru, goggo Suwaiba, Baba Sani, sai autarsu Goggo Halima.
Wurin kasuwancinshi na zuwa k'asar nijar ne, ya samo 'yar can garin ya aura, mai suna Amina tana zaune a can nijar d'in, saboda yanayin halin rayuwa daya zo ya daina shiga garin nijar yasa ya dawo da ita nan Kano, tsangwama da hantara ba wanda bata sha ba wurin Goggo da 'y'ayanta, wanda basa ganin girmanta a matsayinta na matar mahaifinsu.
Hatta danginshi basa sonta, amma ita kullum burinta taga ta kyautata masu.
Ana nan cikin hukuncin Allah ta samu ciki ta haifi d'anta namiji, wanda yaci sunan Babansu Umar, suna kiranshi da farouk, duk da wannan tsangwama da suke mata, baisa ko sau d'aya ta ta'ba tanka masu ba, ko ta kaisu k'ara wurin Mallam Ashiru.
Sai dai idan yana wurin ya gani ya bata hak'uri, dan ta kasance mace mai hak'uri.
Farouk nada shekara uku ta sake haihuwan 'ya mace mai suna Zainabu. Ba tayi arba'in ba ciwon ajali ya kamata, sati d'aya tana ciwo Allah ya d'auki ranta.
Farouk yayi kuka kamar ranshi zai fita, haka shima Mallam Ashiru. 'Yan uwanta sunso da suka zo ko jaririyar ce a basu, amma Goggo tace ita zata raineta, ba yanda zasu yi dole suka hak'ura suka bar mata, yanayi na rashin iyaye da itama bata dashi, tunda suka tafi basu k'ara waiwayan 'ya'yan Amina ba. Rainon Zainabu ne ya dawo hannun Goggo, inda kwata-kwata bata samun kulawa daga gareta, har ta shekara biyu.
Ciwon yunwa ne ya kamata, yayin da take kwance take ciwo, haka itama Allah ya d'auki ranta, tunda Farouk yaga k'anwarshi ta rasu haka yaci kuka, ya dad'e yana kukan mutuwarta.
Haka yake rayuwa cikin k'unci da k'iyayyar 'yanuwanshi.
Bayan shekara goma da haihuwan Farouk ya fara shiga kwari dan naiman na kanshi, duk da haka bai hanashi zuwa makarantar boko dana Islamiyya ba, dan ya kasance mai son yaga yayi zurfi a duka ilimin addini dana boko.
A haka Allah ya had'a jininshi da wani bawan Allah, ya d'auki nauyin karatunshi duka, ba k'aramin dad'i yaji ba, har gida Mallam Ashiru yaje ya mashi godiya.
Bak'in ciki k'arara Goggo ta nuna a kan abinda Farouk ya samu, duk wani abu da suke mashi baya ta'ba d'aga kai ya dubesu, kuma duk da haka Allah ya d'aura mashi son 'yan uwanshi.
Bayan wasu shekaru ya zamto gaba d'ayansu sunyi aure, yayin da duk matansu suke zaune a gidan.
Goggo Suwaiba tana nan cikin Kano tana aure, Goggo Halima kuma tana garin jigawa.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.