K'UDIRINA page 32

141 9 0
                                    

*K'UDIRINA*

        ®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

        ©
*EASHA MD*

*Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)

*Ana baya an samu matsala wurin 31 nasa 30 yanzu, yanzu dai a 32 zamu tashi.*

             *32*

Cikin kuka take magana.

"Aunty Fatima ki taimaka min"

Cikin damuwa da kulawa ta furta.

"Islam kiyi hak'uri! Kibi komai a hankali, na san d'aci da rad'ad'in a rabaka da masoyi, amma komai zaizo da sauk'i."

"Aunty Fatima yanzu Yaya Muhammad baya sona. Wallahi ya daina sona."

Ta fad'i haka tare da fashewa da kuka.

Isowa yayi wurin da take ya duk'a gabanta, magana ya fara a hankali.

"Islam bana jin akwai ranar da zan daina sonki, yanzu ma son da nake maki ne yasa bana so ki auri wannan mutumin wanda bai dace da rayuwarki ba."

"Ni Yaya ka barni kawai na aureshi, kome yake yi ina sonshi a haka."

Mik'ewa tayi da gudu ta fad'a d'aki ta maida k'ofar tasa key ta rufe. Fad'awa kan gado tayi, fashewa tayi da kuka mai ratsa zuciyar mai saurare, kuka take sai kace wadda ranta zai fita, ji tayi zuciyarta na mata zafi. Kuka take sosai wanda lokaci guda kanta ya sara, dafa kanta tayi da hannayenta biyu tana juya kanta tare da zubda hawaye.

Ji take tana son ta cire Abdallah a ranta amma ta kasa cireshi. Dama ai cire so ba zai yuwu a lokaci d'aya ba.

Yaya Muhammad ne ya iso bakin k'ofan yana bugawa, tare da umurtarta data bud'e,

"Ki bud'e Islam zan fad'a maki ko waye Abdallah."

Amma ko tunanin tashi ba tayi ba. Gajiya yayi da mata magiya ya bar wurin. Shima kanshi ji yake zuciyarshi na mashi zafi.

Cikin takaici yake magana da k'arfi.

"Mai yasa ka shigo rayuwarmu? Ka shigo cikinmu dan ka tarwatsa mana farin cikinmu."

Fatima ce ta dafashi cikin kulawa da damuwa ta furta.

"Kayi hak'uri! Dole sai ka kai zuciyarka nesa, sannan har zaka samu damar yanda Islam zata fahimci dalilinka na rashin son auran wanda take so."

"Hakane, zan samu na dai-daita kaina. Sai dai tak'i bud'e k'ofar. Gashi ta kusa fara exams bana so ta samu matsala."

"Yanzu abinda za ayi ka k'yaleta da maganar har mu samu ta gama."

"To shikenan, amma ina cikin damuwa sosai a kan Islam."

Ita kanta Fatima halin da taga duk sun shiga ba k'aramin tausayi suka bata ba.

*** ***
Kwance take wayanta ya fara k'ara, hannu tasa ta d'auko wayan yayin da take jin zafin kanta da yake mata ciwo, hatta idonta kanshi ji take ya mata nauyi, ganin wanda ya kirata yasa ta mik'e zaune ta, dai-daita natsuwarta da hankali ta wuri guda, d'auka tayi tare da sallama cikin sanyin murya. Amsawa yayi.

Gaidashi tayi cikin girmamawa. Bayan ya amsa yace.

"Islam ina so a yanzu muyi magana mai nuhimmanci dake, sai dai na san zaki yi tunanin yanda aka yi na samu number d'inki ko? Number d'inki ya dad'e a hannuna na amsa wurin class reps d'inku."

Ganin yanda yake da class reps d'insu baisa tayi mamakin samun number d'in da yayi ba.

"Ya naji kinyi shiru? Ko nayi laifi  hakan da nayi?"

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now