*K'UDIRINA*
®
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION©
EASHA MDDedicated to Maryamerh Abdulrahman (kwaiseh)
24
Duk wani abu na al'ada Yaya Muhammad sun siya sun kai masu. Wanda duk ya zama abin tsegumi da nuna fa Fatima hantara.
Ya samu sunje sun samu gida a wani unguwa Kundila. Gida ne mai d'auke da gini biyu. D'ayar ginin mai gidan ce a ciki tsohuwa da take so ta samu abokin zama a ciki, d'anta d'aya Allah ya bata shi kuma baya k'asar sai dai suzo ganinta. Koda sunzo suna da nasu gidan da suke sauka. Shiyasa kad'aici ke damunta.
Shawartar d'an nata tayi a kan tana so ta samu abokan zama a gidan. Ganin kada kad'aicin ya dameta ya yarda ta samu wanda zata zauna dasu d'in sai gashi Allah ya kawo su Muhammad gidan. Yabawa da hankalinshi da tayi ba k'aramin dad'i taji ba.
"Gaskiya naji dad'i sosai, kaga kad'aici dama yana damuna. Daga ina kuke haka?"
"Muna a Kabuga ne."
Suka bata amsa.
"Allah Sarki.!""Sai dai bayan matata da zamu zauna harda k'anwata da nake rik'o."
"To ina iyayanku?"
"Allah ya masu rasuwa."
"Allah sarki! Allah yaji k'ansu da rahama. Idan ba damuwa ina so ku dawo gobe bayan nayi waya da d'ana."Sun yarda da haka akan goben zasu dawo duk yanda suka yi dashi zata fad'a masu.
Washegari kuwa suka koma dan jin yanda suka yi.
Gaidata suka yi cikin girmamawa."Kun dawo kenan? To munyi magana dashi yace ba damuwa.
Yanzu muje kuga tsarin d'akin. Binta suka yi har cikin d'akin. Palour ne madaidaici sai d'aki d'aya a k'asa mai d'auke da toilet a ciki sai sama shima dak'i ne shima da toilet.
Daga waje kuma d'an k'aramin d'aki ne da za a iya kiranshi da kitchen duk da ba wani abu a cikinshi da zai nuna anyi amfani dashi." To kaga tsarin wurin ko? Ina fatan ya maka ko?"
"Cikin girmamata yace.
"Sosai d'akin yayi ina so. Yanzu nawa zamu bada."
D'an jinjina maganarshi tayi tare da nisawa tace.
"Ka bari zanyi magana da d'ana duk yanda muka yi dashi zan sanar dakai. Dan maganar wuri ba matsala na baka, tunda dama abokan zama nake nema."
Bashir ne yace.
"Hajiya idan ba damuwa da kunyi maganar yanzu."
Macece mai sauk'in kai cewa tayi.
"To jikana bari na kirashi muji."
Wayarta dake hannunta ta duba, lalubo number d'inshi tayi. Har ta gama ringing bai d'auka ba, sai gashi ya kira. Tana d'agawa suka gaisa.
"Dama zan fad'a maka ne, maganar yaron nan maraya dana fad'a maka mai kirki d'in nan ne ya dawo shine yake so ya san nawa zai rink'a biya."
Daga can 'bangaran yace.
"Hajiya ba kince maraya bane kuma baida k'arfi? Ki fad'a masa mun yafe masa kud'in hayar ya zauna kyauta kinga sai muyi ta samun lada, tunda ba abinda kika nema kika rasa. Na d'auke maki komai, ni dai dama fatana in kyautata ma wanda baida shi."
Cikin farin ciki tace.
"Kai Amma naji dad'i! Allah ya maka Albarka Babana, Allah ya k'ara ma dukiya Albarka. Aci gaba da tainakon wanda baidashi. Yaushe zaka zo?"
"Ina nan zuwa k'arshen wata."
"To Allah ya kai mana lokacin. Na gode sosai da alkhairin da kake yawan yima mabuk'ata, aci gaba kada a fasa."
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.