K'UDIRINA page 58

85 11 0
                                    

*K'UDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

      *58*

*Wattpad: Ayshatmadu*

Washegari tunda ta idar da sallah take zaune kan sallaya ta rasa meke damunta, meke mata dad'i me zata yi taji dad'i a rayuwata.

In banda haniyar mutane 'yan biki dake ta kai kawo a cikin gidan suna aiki ba abinda take ji.

Komawa tayi ta kwanta ta rufe idonta koda zata samu tayi barci na 'yan mintuna.

Gaba d'aya Islam kwance take amma ta nemi barci ta rasa, ta rasa meke mata dad'i. Data tuna abinda take shirin yi sai taji gabanta ya yanke ya fad'i.

In banda hawaye ba abinda take zubdawa a idanunta, tana tunanin anya abinda ta d'auko mai 'bullewa ne kuwa? Taya zata fuskanci mutane da wannan al'amarin?

Runtse idanunta ta k'ara yi yayi da wasu zazzafan hawaye ya k'ara zubo mata. Hannu tasa ta share, Zarah dake tsaye kanta tace.

"Amarya ya kamata ki tashi hakanan fa."

D'agowa tayi da idanunta wanda tuni suka kad'a suka yi jawur.

Dubanta Zarah tayi tace.

"Kar dai kuka kika zauna kike tayi? Kinko ga yanda idanunki suka yi kuwa?"

Mi'kewa tayi ba tare da ta iya ce mata komai ba ta fad'a toilet, d'auraye fuskarta tayi kana ta fito.

Ayshat wadda ta shigo d'akin yanzu ta dubi Islam had'i da cewa.

"Ke Ke kuma lafiya idanunki suka kumbura haka? Ko har kin fara kukan rabuwa da gida ne? Ke kika ce kina so da baki ce kina so ba da ba a baki shi ba."

Islam ce ta kai mata duka had'i da cewa.

"Kede Ayshat haka kike baki da damuwa a rayuwarki, ina kula dake duk abinda ke ranki koda ko zai 'bata ma mutum rai baki damuwa."

"Hmm! Kin jiki da wata magana to damuwar mai zaiyi bayan ina ta ro'konki a kan ki fasa wannan auran da kike son yi."

"Uhumm! Ayshat kenan ba zaki gane ba."

D'an juyawa kad'an Ayshat tayi tare da fari da idanunta tace.

"Oh! da gaske ba zan gane ba? To tunda ke kin gane ai shikenan ni ba sai na gane ba."

Zarah dake zaune tana jinsu dariya take tayi tace.

"Wallahi idan kuna wannan dramer taku ba k'aramin dariya kuke bani ba. Yanzu dai amarya ya kamata ki tashi kiyi wanka ki d'anyi kwalliya ko."

Islam ta mi'ke had'i da cewa.

"Amarya ni kuma bari na d'auko maki gudunmuwata wanda dama sai ranar d'aurin aure zan baki."

Tana gama maganar ta fita ba tare da ta tsaya sauraran ko zata ce wani abu ba.

Mintuna kad'an ta shigo da jaka a hannunta da wata k'aramar jaka ta diresu a kan gado tare da fiddo dasu ta dubi Islam tace.

"To amarya ga nawa ba yawa kaya ne kala uku na maki kici biki dasu."

Islam kallonta taci gaba dayi da murmushi d'auke a fuskarta, ci gaba da kallon Ayshat taci gaba dayi ba tare da murmushin ya rabu da fuskarta ba.

Hura mata iska Ayshat tayi tare da cewa.

"Wannan kallon fa na miye haka?"

"Ayshat na gode sosai Allah ya bar zumunci."

"Kada ki damu Islam duk da ba son auran nan nake yi ba, amma ya zama dole in nuna tawa bajintar, tunda kin nace sai kin aureshi."

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now