*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*55*
*Wattpad: Ayshatmadu*
D'an gyaran murya yayi kad'an kana yace.
"Islam Abdallah dai kike so ko? Shikenan zanbi za'binki ki fad'a mashi ya turo a sa ranarku, sai dai kuma auran ba zai wuce sati d'aya zuwa biyu ba..."
Ji tayi gabanta ya yanke ya fad'i, ci gaba yayi da maganarshi yana mai nunata da yatsa.
"Sai dai ina so ki sani Islam duk abinda ya biyo bayan auranki ke kika nema da kanki, ba wai na maki baki bane, amma ina mai tabbatar maki da duk ranar da suka san ke wacece ba zasu barki ba Islam."
Ya idasa maganar cikin damuwa yanda ka san zaiyi kuka. D'ago kanta tayi kad'an ta kalleshi ta maidashi 'kasa tare da cewa.
"Yaya ka daina fad'in haka, Insha Allah ba abinda zai biyo baya sai alkhairi."
"Ina fatan hakan ya kasance Islam. Zaki iya tafiya."
Mi'kewa tayi ta fara tafiya jikinta a sanyaye kamar wadda 'kwai ya fashe mawa a ciki.
Maida kanshi jikin kujera yana kallonta cike da mamaki, lokaci guda a kan soyayya ta rufe idonta ta manta marsayinshi a zuciyarta. Hawaye ne ya gangaro mashi, hannu yasa ya fara gogewa.
Ita ko tana shiga d'aki gaban madobi ta tsaya ta tsura ma kanta ido, sai kuma ta saki murmushi wanda ita kad'ai ta san dalilinta na yin wannan murmushin. Dawowa tayi ta fad'a kan gado tana mai ci gaba da murmushin.
Mi'kewa tayi ta zauna ta kuma rafka tagumi, lokaci guda kuma yanayin fuskarta ya sauya daga murmushin da take zuwa 'bacin rai.
Yaya Muhammad ne ya shigo d'akin ya taddata a haka, hannunshi yasa ya cire mata tagumin da tayi yace.
"Wannan tagumin fa na miye? Ko baki sonshi ne?"
Girgiza mashi kai tayi.
"To kada kisa ma kanki damuwa, ni dai ban maki dole ba, abinda kike so na tayaki so."
Fad'awa tayi kanshi ta saki kuka wanda ya rasa dalilinta na yin kukan alhalin yabi za'binta.
D'agota yayi yana share mata hawayen yace.
"Wannan kukan na miye? Ko na dad'i ne?"
Ya idasa maganar yana murmushin.
"Yaya kayi ha'kuri da abinda na maka, ni kaina ba a son raina hakan ya faru dani ba, na san kana fushi dani kana dai min dariya ne kawai."
Ya bata amsa cikin kulawa.
"A'a Islam bana fushi dake, duk abinda zai saki farin ciki shi nake so, ba abinda zaki nema a wurina da zan kasa yi maki koda kuwa hakan zai sa in rasa farin cikina."
'Kara ri'keshi tayi tana kuka iya cin 'karfinta tana jin tausayin d'an uwanta a cikn zuciyarta.
Ha'kuri yaci gaba da bata, zama yayi yana ta lallashinta har sai da yaga ta saki jikinta sannan ya bar d'akin. Binshi tayi da kallo cike da tausayi.
"Anya ko wannan abin dana aikata na kyauta kuwa? Nama Yayana adalci kuwa?"
Hawaye ne ya zubo mata. Hannu tasa ta goge hawayen.
Wayanta ne ya fara 'kara, dubawa tayi dan ganin waye ke kiranta. Sunan Abdallah ne ya bayyana. Hannu tasa ta d'auka ta karashi a kunnanta.
"Ranki ya dad'e yau mulkin ne ya motsa?"
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.