*KUDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)
*48*
*Wattpad: Ayshatmadu*
Haka suka shigo gidan da kaya Inna matar Mallam Musa ta dubesu tare da cewa.
"Har ka d'aukosu?"
Yana Shirin zama yace.
"Eh Asabe, gasu nan marayu ne ki ri'kesu amana."
"To Allah ya bani ikon ri'kesu lafiya.
"To Amin ya rabbi."
Amsar yarinyar yayi ya dubi Muhammad had'i da cewa.
"Muhammad wane suna za a sa mata?"
Murya can 'kasa yace.
"Kasa mata Aminatu zan rin'ka ce mata Islam."
Haka kuwa aka yi, Mallam Musa ya mata hud'uba da sunan mamansu wato Aminatu.
Kayansu aka shigar masu dashi d'aki, wayar Mommy Amina kuwa cire sim d'in yayi, ya kasheta ya wurga 'kasan akwati.
*** ***
Haka rayuwarsu taci gaba a gidan Mallam Musa, shi kuma yaci gaba da zuwa makaranta wanda da 'kyar ake samu ya tafi, dan ko ya tafi hankalinshi na kan Aminatul'Islam.Haka Karime tana yawan zuwa dubasu akai akai.
Kayan Mommy kuwa haka ya d'iban ma Karime mai yawa, yaba ma matar Mallam Musa ma, sauran kuwa sawa yayi duk aka raba ma mabu'kata. In banda sababbin data d'inka yasa aka saida dan ya samu na kashewa a makaranta da kuma wasu hidindimu nasu.
Tun Muhammad na damuwa da halin da suka shiga, har yazo ya saba.
Damuwarshi d'aya idan ya tafi ya bar Islam sai yayi ta tunanin yanzu wane hali take ciki, 'kosawa yake a tashi da an tashi yake saurin dawowa gida, da ya dawo kuma shikenan rainonta ya dawo hannunshi kenan, bai ta'ba bari ya rabu da ita. A haka suka yi hutunsu na third term.
Gaba d'aya rainonta ya dawo wurinshi, wankanta kashinta abincinta bai bari kowa yayi.
Muhammad bai tashi shiga tashin hankali ba, sai da suka koma school ya juya yaga ba wanda zai biya mashi school fees, nan fa tashin hankalinshi ya taso, tun yana zuwa suna 'kyaleshi, 'karshe suka koreshi, yayi kuka kamar ranshi zai fita, haka har ya dawo ya mi'ka ma Allah lamuranshi. Cikin kud'innsu ya samu da taimakon Mallam Musa ya shiga government School, ganin 'kwazonshi yasa suka barshi a jss2.
Cikin haka duk kud'in dake hannunshi da ake saima Islam madara da Pampers ya 'kare, nan kuma hankalinshi ya tashi.
"Mallam Musa taya za ayi Islam ta rin'ka samu tana cin abinci?
Maganar yake cikin kuka da nuna tashin hankali.
Mallam Musa dafa kafad'arshi yayi yace.
"Muhammad ka kwantar da hankalinka, Islam ba zata zauna da yunwa ba. Kaga ga saniyata nan tunda bani da kud'in da zan rin'ka siyan mata madara, sai da safe a rin'ka tatsar mata nononta tana sha."
Damuwa ce 'karara ta bayyana a saman fuskar Muhammad yace.
"Mallam Musa taya zamu bama 'karamar yarinya wannan abin ta sha bana so"
"Kada ka damu ba abin tada hankali bane, ba kaga muma muna sha ba, bari kaga ta fara sha zaka ga yanda jikinta zaiyi kyau ta 'kara 'kiba, kai da kanga zaka ga yanda zata birgeka."
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.