Nagarta writers association
About Nagarta App
https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.com.nagartaMasu anfani da wayoyin Android OS version 6.0 and above ne kadai zasu iya installing akan wayarsu.
Wanda version nasa ke kasa da hakan playstore zai sanar da shi not compatible, wanda hakan na nufin sai ka yi updating wayarka zuwa sabuwar version nasu.
Ba laifinmu bane, doka ne daga playstore, a yi hakuri da hakan.
Bayan anyi downloading manhajar a kan waya a ka shiga ciki, a sama, bayan logo, Nagarta story ne rubuce, sai wurin nema wato Search, gefensa kuma settings, daga karshe kuma digo uku zaka gani a jere, wanda a nan ne zaka iya sanar da abokai da ‘yan uwa game da application namu, ko kuma dan ajiye mana sako cikin sauki.
A kasa kuwa, zaku ga Browse da recommended. Sai All da kuma jerin categories a kasa.
A takaice wannan shafin ya kunshi dukkan abunda application din ya kunsa.Daga karshe a kasa, zaku ci karo da Home, inda dukkan rubutun da na ambato yake kenan, daga gefensa akwai Authors, ma’ana Marubutan manhajar. Idan ka danna zaka ga all ta sama, gefensa zaka ga jerin sunayen Marubuta Nagarta, daga Shugaba Benaxir Omar, zuwa ga na’ibarta Lubbatu Maitafsir sai sauran officials da members.
A nan zaki iya zabar gwanarki, wanda kowacce littafanta na kasan sunanta idan kika taba.
Daga Authors sai categories, su ma kaman sunayen suke a jere, Romance, historical fiction da dai sauransu. Dukkan wanda kuka zaba zaku ga littafansu a karkashinsu.
Daga nan sai Saved, ma’ana ma’adani, wato wurin da littafan da ka ajje domin karatu zasu zauna.
Daga karshe sai User, wurin yin register dan samun daman comment da voting.
A kowani littafi da zaku shiga akwai summary, tsokaci ko abunda littafin ya kunsa.
Idan kuna son sanar da ‘yan uwa littafin da ka karanta dan su ma su karanta, bayan ka shiga cikin littafin, zaku ga alamar share a gefen dama, wanda in kuka danna zai tambayi inda zaka tura, whatsapp ne, ko Facebook ko wani app na daban.
Za a dauki summaryn littafin, da link na littafin a tura dan meshi ya samu saukin samu.
Daga karshe, bayan ka daura Application a kan wayarka, duk lokacin da a ka daura sabon littafi zaku samu sanarwa (notification) a saman wayarka, za a sanar da kai littafi kaza, daga marubuci kaza ya daura littafi cikin category kaza, sai ka danna ka shiga ciki kai tsaye don shan karatu.
Manhajarmu a yanzu playstore kawai yake, masu anfani da Iphone zasu iya shiga website namu kamar haka;-
www.nagartawriters.com.ng
Dukkan abunda yake app zaka samu a nan, sai dai saving littafi ne kawai bazaka iya ba.
A tuntubi wadan nan lambobin dan karin bayani, tsokaci, da duk wani abunda yakamata mu sani:-
08088929221
07037603276Babu Nagarta idan babu makaranta.
Mungode!
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.