'KUDIRINA Page 42

139 11 0
                                    

*'KUDIRINA*

®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*

©
*EASHA MD*

*Dedicated to maryamerh Abdurrahman* (kwaiseh)

*42*

Bayan taje ta siyo maganin, komawa tayi d'akin da yake kwance tayi, nan ta taddasu tsaye cirko cirko suna mai nuna alamun damuwa a fuskarsu kamar gaske.

Kallonsu kawai tayi ba tare data furta masu komai ba, samun bakin gadon tayi ta zauna idonta na kan Farouk.

Goggo ce ta iso asibitin buguzun-buguzun, cikin yanayi na nuna damuwa ta furta.

"Ya jikin nashi? Ashe ciwo har ya kai ga gadon asibiti, Allah dai ya tashi kafad'a."

"Amin dai Goggo."

Cewar Baba Salisu dake tsaye wanda idonshi 'kyam yake kan Farouk dake kwance yana barci yayin da numfashinshi ke fita sama sama. Ko tunanin mai yake haka daya kura mashi ido haka? Shi yaba ma kanshi sani.

Tunda Amina ta 'kura mashi ido, hawaye ke sauka akan fuskarta.

Goggo ce ta dubeta cikin nuna tsana, ta furta.

"Me kuma kukan me kika tashi haka kina mashi? Wannan kukan harda na funafurci, kinbi kinyi kane kane da dukiyarshi keba haihuwa ba."

Amina kallonta kawai tayi ba tare data ce mata komai ba.

Binta tayi da harara tare da sakin tsaki, yayin da ita kam Amina ba ta ita take yi ba, ta lafiyar mijinta take.

Idonshi ya fara bud'ewa a hankali, har ya gama bud'eshi, idonshi ne ya sauka kan Amina, wanda ta bishi da kallo, hawaye d'auke a fuskarta. Gaba d'aya suka 'karaso bakin gadon suna mashi sannu.

Murmushi ya sakar mata, tare da furta.

"Wannan hawayen na miye haka? Kin san na tsani hawayenki."

Goggo dubanshi tayi tare da ta'be baki.

"Haba Faruku! Kana fama da lalura daga tashinka ka fara magana."

"Goggo baki ga kuka take ba, kuma na tabbata kukanta yana da nasaba da ciwon da nake, ina Muhammad fa?"

Ya fad'a yana mai kallonta.

Amsa ta bashi.

"Yana gida saboda school shiyasa ban barshi a nan ba."

"Da kin sani kin bar min shi naji d'uminshi."

Murmushi tayi. Ji yake kamar ya share mata hawayen dake fuskarta, sai dai ba dama, su Goggo na wurin kada suce yayi rashin kunya.

Mi'kewa Goggo tayi cikin fad'a ta dubi 'ya'yanta tare da furta.

"Ku tashi mu bar asibitin nan, tunda baya bu'katar ganinmu a wurin, ya za'bi wad'anda yake son gani."

Baba Nasiru yace.

"A'a Goggo ba za ayi haka ba."

"Kai rufe min baki sakaran banza, baka ga abinda ya mana ba ya nuna bai damu damu ba, har zaka iya fad'in ba za ayi haka ba."

Farouk marairaicewa yayi kamar zaiyi kuka yace.

"Goggo kiyi ha'kuri bana so kina furta irin maganar nan, nima d'anki ne ke kika raine ni."

"A'a kai ba d'ana bane, kaga 'ya'yana dana haifa da cikina, ba zasu ta'ba fifita wata a kaina ba."

Runtse idanunshi yayi wanda hawaye mai zafi ya gangaro mashi, dafe 'kirjinshi yayi daya ji yana mashi zafi.

K'UDIRINAWhere stories live. Discover now