*🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*
*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*
*NA SLIMZY*
*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*
02"Waini kam kuluwa tun jiya da muka tura yaran Nan nida shiru bamuga Fatima Zahra ta dawo ba gasu zainab da su hauwau dik sun dawo an caske Mana Yan canjin mu Amma har yanzun yarinyar Nan Bata dawoba Fatima Zahra Allah yasa dai ba taurin Kai tayiwa yarima ba Dan zata aika wanan shegiyar yarinyar Mai Kama da aljanu Mai shegen miskilancin tsiya da taurin Kai da kyar dakyar muka tura yarinyar Nan baason ranta ba Allah yasadai ba guduwa tayi ba Dan tabbas idan Fatima ta gudu daga gidan Nan kashina ya bushe a wajen yareemah kabir don Shi sonta yakeyi dagaske,Ni tsorona ma kada magana ta fito ya gane Dan uwansa aka turawa ita yayi lalata da ita Dan wallahi a tsorace nake"
Murmushi wadda aka Kira da kuluwa tayi tace "in Banda abinki hajiya me zai dameki bayan yarinyar Nan ko Bata tayi babu me nemanki tunda babu Wanda yasan kunayin wanna harkar ta tura marayu neman kudi,sanan ko baaga Fatima Zahra ba bawani Abu da zai faru tunda dama ba galihu garetaba marainiya CE fa ba uwa ba uwa babu dangi waya sani ma ko cikin shegece ita?"
Shekewa da dariya sukayi dukansu harda tafawa hajiya ta Nisa tace "ita tasani idan ma Bata yardaba yayi ta karfin tsiya ko a jikina nidai na caske yan canjina a aljihuna tunda ya Dade Yana kwadayim shegiya tanayi Mana bakin ciki Sai jiya Allah ya bamu saa akanta"
"Hajiya ai yarinyar CE ta wanku don wallahi ko zainab da manyan masu kudi da Yan siyasa keji da ita saboda diri da kyawu suke hutawa da ita batakai Fatima suffa ba,Fatima dabance Allah ya hore Mata kyau da zati da diri na tabbatar yarima Sai yadawo ya Kara Miki tukwici donshi zai baretq a Leda"
"Allah kuluwa?Allah yasa ya karamun tukwici kema Zan San Miki wani Abu don kema kina bamu babbar gudun mawa"
"Ameeen dai hajiya"
Nan suka cigaba da tattaunawa Akan yadda suke gudanar da rayuwar safarar Yan Mata a gidan marayu Wanda hakan ya zame musu babbar Sanaa da suke samun makudan kudi daga Mayan masu kudi da Yan siyasa...
*******
Tunda garin Allah ya waye take sintiri daga cikin inda suke zuwa bakin gate din gidan hankalinta a tsananin tashe,ita babban tashin hankalinta be wuce yau me zata cewa yarima khabir idan yazo neman Fatima ba tun jiya dasu hajiya suka fita da ita har yanzun baa dawo da ita ba tsoronta be wuce Allah yasa dai ba kaita sukayi a lalata taba kamar yadda ake daukarsu daidai da dai dai Ana rabasu da budurcinsu saboda Basu da gata a matsayinsu na marayu bayan Suma Yaya ne Amma bazasu gusheba suna addua Akan AYI WALK'IYA..halin kowa ya fito asirin masu wanan al'amari ya tonu dikda batajin akwai wanna ranan da wanan al'amari zai faru tunda Basu da gata Sai na Allah....wasu zafafan hawayene suka shiga gangarowa a kuncinta Wanda batasan Tana yinsuba tunda ta hada Kai da gate ta fada wanna duniyar tunaninAlamar zaa bude gate taji tayi kaza ta boye a jikin bishiyar da tayiwa gate din kawanya,Wanda ta gani ya shigo a furgice ne tabishi da kallon tsana hannunsa dauke da jarida zufa ta jikeshi sharkaf shaddarsa kamar an zuba Masa ruwa....bayansa tabi da sauri Dan shine ya fita dasu Fatima da yamma.
Wajen dasu hajiya da kuluwa ke zaune ya nufa da sauri itama Tana biye dashi a baya har suka kusa Isa wajen da suke kusa da kitchen ne ta ruga ta boye a bayan kofar kitchen...hajiya CE ta wurga mishi wani kallo irin na tsofaffim Yan duniya tace "Kai Kuma fa haruna kaketa mazurai kamar Mara gaskiya"
"Hajiya Dole inyi mazurai Dan muna cikin babban tashin hankalin da idan maganar Nan ta fito kashinmu ya bushe"
Saida hajiya ta girgiza da Jin abinda yace Amma saita dake ta yatsina fuska tace "meye Kuma ya faru?"
VOUS LISEZ
Anyi Walk'iya.......
Fiction HistoriqueBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...