46

2.1K 133 15
                                        

🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

  *NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

  _Sakon gaisuwa da fatan alheri a gareku_ *FARIDA KAKANGI,ASMAU IBRAHIM* *BELLO(MA'U),AISHA USMAN(DADA),FAEEZAH* *ISYAKU(FA'EEH)...* __son so fisabilillahi_💙💜
_
                    46

  Gyaran murya Mai martaba yayi hannunsa rike da hoton da yarima ya gabatar Masa ya dago kansa ya dubi kowa dake cikin fadar Sanan ya maida dubansa ga hoton dake hannunsa lokaci daya ya sauke ajiyar zuciya Sanan ya fara magana a nutse,

  "Dukkan yabo da godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wataala da ya bayyanar Mana da wani bakon al"amari Wanda bamusan dashi ba tun bayan shekaru da suka gabata,watakila ma mun cire Rai da cewa wata Rana wani bakon al'amari zai faru,hakika kabiru ya gabatarmun da wani hoto dazun dazun da wasu bayanai dangane da hoton da Kuma wani rubutu a bayan hoton dikda bamu da tabbas Akan hakan"

Murmushi hajiya babba tayi tana kada kai,

  "Saidai dik wani Mai hankali Wanda yasan marigayi abdallah yasan zahrau to tabbas wanan yarinya batada banbaci da iyayenta ko wajen kamanni,...na Dade Ina zargin wani Abu dangane da Fatima tun ranan da Allah ya jehota gidan Nan nagasa samun natsuwata narasa hankalina saboda tsananin Kama da itakeyi da ubanta ta wani bangare Kuma jini Yana nuna kamaninta da uwarta Dan haka yanzun da kabiru ya gabatar mun da abinda ya faru ban tsaya wani waswasiba na yanke shawara Akan Fatima diyar abdallah ce marigayi"

  Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci hajiya babba da rahina suka dago a lokaci daya suka kalli juna Sanan suka maida kansu suka sunkuyar,

  Juyowa Mai martaba yayi ya dubi waziri Wanda ke gurfane Yana jiniina Kai "waziri me kake gani dangane da abinda ya faru?maana ga Fatima Nan diyata ta bayyana kasan ubanta tun Yana Raye kakeyi Masa waziri to yanzun menene shawararka?"

  Gyaran murya waziri yayi "ni a ganina anawa tunanin ranka ya dade bazai yiwu ace daga ganin hoto da kamanni ace an amince da wanan yarinya a matsayin Yar marigayiba ya Dace ayi bincike kafin a tabbatar da hakan,abinda yasa nace haka shine hoto da kamanni suna iya yuwuwa ta ko wani yanayi,Sanan zamanine yanzun na computer zaa iya hada hoton Fatima da sarauniya zahrau data bace,gaskiya be kamata sarki yayi saurin karbar wanan maganar ba"..

  Wani mugun kallo yarima yake watsawa waziri lokacin da yake maganar,Sanan take ya juya ya maida dubansa ga hajiya rahina da hajiya babba wadanda suke faman jinjina Kai tunda waziri ya Soma magana,

  Shiru Mai martaba yayi Yana nazarin kalaman waziri wadanda yanada nashi point din a wanan lokacin,sai Mai martaba ya gyara zamansa kqdan yace "hakika kanada taka hujjar waziri duba da Babu wata kwakkwaran hujja da ya nuna cewa Fatima din diyar Mai martaba marigayi ce sai kamanni sai Kuma hoton da ya bayyana surar marigayiya zahrsu da ita Yar Tata zaa duba maganarka,..

  Ummu ce dake gefe bude baki muryarta a sarke "Niko a ganina tunda bayanai da hujjar hoto ya bayyana be kamata a tsaya jainja Akan yarda da maganar Fatima din diyarmu ce saboda idan akace bazaa yardabd da wanan hoto da bayanin da zahrau ta rubuta a baya to a Ina zaa samu ita zahraun ta bayyana abinda ya faru?...Niko xanso ace hajiya karama ta fito a gabanka ta fasa Kwan abinda ya faru tsakaninsu da zahrau da safiya da rahina"a tausashe ummu ta karasa bayanin ta Wanda hakan ne yayi sanadiyyar gigicewar hajiya babba da rahina .....

  "Hajiya karama menene boyayyen Al'amari daya faru a baya Wanda ni din bansan da zamansa ba?"

  Gurfanawa mama karama tayi "Allah ya taimaki Mai martaba,.....Nan ta kwashe dik abinda ya faru Wanda tabawa su Fatima labari ta Kara bayyanawa a gaban Mai martaba harda abinda ta boye da Bata fadaba dik ta fada na Hari da aka kaiwa zahrau Dan akasheta Wanda shine musababbin barinta gidan sarauta baasan inda take ba har yanzun,

Anyi Walk'iya.......Stories to obsess over. Discover now