🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
36Ta dauki kimanin minti goma cikin bayi Tana wanka sanan ta dauro alwala ta bude bayin ta fito Tana goge fuskarta Bata lura da ummu dake zaune gefen gado ba Saida ta juyo da nufin zuwa bakin gado ta dauki kayanta Sukai Ido hudu da ummu hannunta rike da turaren Tana jujjuyawa....ja da baya Fatima tayi hade da dafa kirji "ummu yaushe kika shigo?wallahi banji shigowarki ba"
"In Banda abinki Fatima keda kike wanka ya zaayi kiji shigowata?bayan tahowarki sadik yasamun rigima shi indomie zaici to bansamu me kawoshiba shine nazo kawoshi nadade Ina sallama waje naji Shiru shine Dana turo kofar naji a bude,sai Kuma naji karar ruwa a bayi nasan wanka kikeyi"....
Wucewa Fatima tayi wajen dressing mirrow ta dauki Mai Tana Shirin sharawa ummu ta watso Mata tambaya"Fatima me kikeyi da turaren Yan bori?turare Dan d'uri?"
Da sauri Fatima ta juyo Tana kallon turaren hannun ummu,sai ta danyi murmushi tace "wayyoo ummu turarena ne na ajiyene idan na fito wanka Nasa Kaya in shafa"
Takaicine ya lullube ummu tafara masifa Tana fadin "baki da hankali Amma,da ranki da lafiyarki Zaki shafa wanan turaren?Wanda idan kika shiga cikin jamaa na tabbatar da tushe hanci zaa rinkayi so kike ki janyowa kanki raini ma kenan cikin manyan mutane da ya'yan attajirai,to ki rufamin asiri ki rufawa kanki kar in kuskura inji kina kamshin wanan turaren Domin ni Zaki zubarwa da mutunci,ai kin wuce wanan lokacin Kuma Fatima,yanzun ke Yar gatace Yar ummu da abbah ko"...ta karashe maganar da sanyin murya yadda taga jikin Fatima na rawa,
Gyada Mata Kai Fatima tayi baki na rawa tace "insha Allah bazan shafaba ummu dama banida turarene"
Murmushi ummu ta sauke "nasani ai naji dazun kamshin turarena kikeyi koh?meyasa yanzun baki daukoshi kin Kara shafawa ba ai na mamanki ne koh"
Ta sunkuyar da kanta kasa "toh ummu"
"Kokefa yanzun gobe da wuri zansa akaiki kiyi siyayya hardasu turarruka da gyaluluwa da takalma da jakunkuna ko Yar ummu "
Dadi ne ya Kama Fatima Wanda har saida murmushi ya subuce Mata sanan ta rufe fuskarta Tana dariya,itama ummun dariya ta shigayi Tana fadin "ja'irar yarinya Zaki sa magauta suyi Mana kallon banza"
Itadai Fatima murmushi kawai take ta cigaba da shafa manta sannan ta dauki kayanta ta sanya, ta shimfida daddumarta ta tada sallahrta,bayan ta idar ne ta nade daddumar ta nufi kitchen sadik ya rufa Mata baya yayinda ummu ta Dan kishingida bacci ya dauketa....
********
Sashen hajiya karama ya sake shiga Yana dube dube ko zai ganta Amma be ganta ba ya dade ciki a zaune har kanwar hajiya ta gaji ta tambayeshi wa yake nema?ko Yana bukatar wani abune
Shafa keyarsa yayi sanan yace "dama ummu nake nema kuma bangantaba"....Nan ne ake sanar Masa da ta tafi gida,
Yana fitowa sauri sauri ya nufi sashen ummu yayinda rahane ta ruga aguje ta sanarwa da deejahmah taga yarima yayi sashen hajiya zainab da alama wajen Fatima zaije....hankalinta ba karamin tashi yayi ba tunanin yadda zaayi taje taga me sukeyi takeyi.....
Shikuwa yarima ya Dade tsaye Yana bugun kofa sanan sadik yazo ya bude Masa ya dauki sadik ya dagasa sama Yana fadin "oga sadik Kaine da bude kofa?rigima babu ko?"...ya karasa shigowa dakin Yana kalle kalle sanan ya dubi sadik yace "Ina ummu ne?"
"Tana dakin anty Fatima Tana bacci"...
"Owk Ina antyn naka?"
"Kitchen ta shiga Tana dafamin abinci"....
YOU ARE READING
Anyi Walk'iya.......
Historical FictionBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...