🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*_Wanan shafi kyautace zuwa gareki Yar uwata Rabin jiki bazan iya_ _musalta matsayinki da kimarki a idanuna da zuciyata_ _ba_ *SOPHIE GALADANCI* _Ina yi Miki son so Allah ya Kara Mana dankon zumunci....Allah ya barki da *N* dinki ya nuna mun bikinki in kwashi rawa harda shoki😹😹😹...._
27********
Bangaren sarki kuwa tunda hajiya rahina da deejahmah suka gurfana a gabansa hajiya rahina ke koro Masa bayanin abinda ya faru Daren jiya na karya da gaskiya Wanda akayi da Wanda baayiba har cewa Mai martaba tayi yarima yace da gangan ya kawota gidan dama Dan ya aureta....shidai Mai martaba shiru yayi Yana saurarenta har ta Dasa Aya a zancenta,Gwauron numfashi ya sauke hade da Dan murmushi sanan yace "ai rahina be kamaceki ki kawo karar danki ba bayan kinada yancin da Zaki hukuntashi da kanki batare da kin fadamun ba,ni yanzun banida abin cewa da ya wuce kiyi hakuri da su duka Dan yarane kanana wani abun yaro yakan fadesa ne batare da tunanin mezaije ya dawoba ,to ke babba ce matsayin uwa Kuma suruka saboda haka kiyi hakuri kibarni da shi kabirun"
Gyara Zama tayi "ranka ya dade yanzun maganar da kabiru yakeyi dik ya Gama zagaye gari Wai zai auri wannan tsintacciyar yarinyar Mara iyaye wadda baasan asalintaba,baasaniba ta hanyar aure aka haifeta?ko ba ta hanyar aure ba?"..
Murmushi Mai martaba yayi irin na manyan sanan ya danyi gyaran murya,jimm kadan yace "yanzun dai a jira hukuncin da zan Yanke zuwa gobe"
Dan shiru hajiya rahina tayi na Dan lokaci sanan ta Kara durkusawa"Allah ya taimakeka ya Kara maka lafiya ka duba yuwuwar wanan lamari ga Dan sarki jikan sarki"
Daga Mata Kai kawai Mai martaba yayi batare da yace komiba.....
Jiki a sanyaye tayiwa Mai martaba sallama suka baro fada jiki Babu kwari....
A hanyarsu ta komawa cikin gida suna tafe deejahmah na bambami tamkar zata Ari baki "wallahi tallahi sai yarinyar Nan tayi datasanin shigowa rayuwarmu,saina yi Mata abinda bazata taba mantawa daniba"
"Kidaina Bata bakinki Domin na tanadi sabon makami Wanda zamuyi yaki dashi azabtarwa Mai sauki ne Allah dai ya Bata ikon yin kishi dake"
Kwafa deejahma tayi ta gyada Kai lokacin sun shigo sashin hajiya babba,
Tsayuwa deejahmah tayi rike da kugu sai hura hanci takeyi Tana huci,a fusace ta juyo inda bilkisu da Rahane ke tsugunne ta watsawa Rahane mugun kallo sanan tace "ke jeki kiramun Fatima"
A kidime jiki na rawa Rahane ta Mike tayi hanyar ficewa harta Kai kofa ta tsinkayo muryar deejahma na fadin "ki tabbatar da kin kawota Nan kunzo tare"
"Toh ranki ya dade Allah ya huci zuciyar sarauniya"....ta juya ta fice....
Zare ido kawai bilkisu takeyi a zaune tamkar zata saki fitsari Dan ta tsorata da ganin yanayin wadanan azzaluman,addua kawai takeyi a zuciyarta na Allah ya kar yasa aga Fatima...
*********
"Mamana ki fahimceni wallahi auren Fatima a gareni tamkar jihadi ne a gareni daku baki daya,ke mahaifiyatace banaso kiyi wani mugun furuci Akan wanan lamarin Domin ke uwace a gareni yardarki itace bukatata kiyimun addua Allah ubangiji yasa sanaddiyar hakan Allah yayi Mana rahma Dani daku baki daya"
Tunda ya fara magana tai shiru Tana fuskantar sa,Harga allah dik maganganun daya fad'a a fadar sarki gaskiya ce Amma yuwuwar hakan fa?shin me hakan ke nufi?idan wasu sun fahimci wanan lamari wadansu bazasu fahimtaba....
ESTÁS LEYENDO
Anyi Walk'iya.......
Ficción históricaBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...