🌩 *ANYI* *WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS* *ASSOCIATION* 💡
*NA:SLIMZY✍🏻*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga* *k'awata faty D'an* *maliki*
06
Yarima Wanda ke zaune a dakinsa bayan ya dawo kotu Yana tunanin yadda shariah zata kasance,ya Mike a fusace Jin bayanin da barrister Abdul yayi mishi na Fatima Taki Basu wani bayani Yana fitowa gidansu yayi cikin tsananin tashin hankali ya Isa gidan,
A parlor ya tarar dasu da alama Basu Dade da shigowa gidan ba,suna zazzaune barrister hauwa Tana Yan rubuce rubuce a takaddarta,bayan sun gaisane barrister ta gabatar mishi da recording din muryar Fatima na tattaunawa da sukayi ,Dafe kansa kawai yayi bayan ya Gama dauraren komi Nan da Nan hankalinsa yayi kololuwar tashi ga wani haushin Fatima da ya ziyarci zuciyarsa a Karo na farko,
Da'go rinanun idanuwansa yayi ya saukesu Akan barrister Abdul dakyar yake motsa labbansa yace "barrister me yarinyar Nan take nufi?ta zabi a kasheta Ni in shiga uku Koh?me take nufi?"
Dan murmushi barrister Abdul yayi yace "kadaiji abinda take fada sanan barrister ta tabbatar mun da yadda take maganar cike da confidence Akan itace tayi kisan shi zai baka mamaki"
A fusace yarima yace "to idan ma itace tayi kisan meyasa bazata fada Mana dalilinta nayin kisanba ko kuwa Ana kisa Babu daliline?idan wani ne yasata tayi kisan ta fada Mana ta tsaya Tana wahalar damu,fatyma na neman in rasa farin cikina a Karo na biyu,Fatima na nema tasa zuciyata ta buga in mutu inbarta cikin kunci da masifar da take ciki,Fatima Taki tausayawa kanta ta tausayamun Nima"zuwa yanzun yarima yakai karshe cikin tsananin damuwa da tashin hankali....hannu yasa ya Dafe kansa zuciyarsa na harbawa tamkar zata faso kirjinsa ta fito,da yanada dama da ya cireta cikin zuciyarsa,Amma ta Yaya hakan zai kasance bayan Fatima itace jinin dake yawo a jikinsa har zuwa cikin zuciyar tasa?runtse idanuwansa yayi Yana tuna abubuwan da dama dayasa bazai iya barintaba...
Tunda ya Dafe kansa,barrister Abdul da madam dinsa suke kallonsa cike da tausayawa barrister hauwa CE ta Nisa tace
"Ka kwantar da hankalinka yarima insha allahu Fatima zata kubuta da yardar allah"Da'go kansa yayi cikin kosawa yace "ta Yaya"
"Addua zamu dukufa yi sanan mu hadu a kotun gobe"
"Shikenan baristers nagode allah ya kaimu goben,Ni zanje gida"
"Ka tsaya muci abinci Mana,don daga ganinka bakada lokacin abinci ma"cewar barrister Abdul,
Girgiza Kai kawai yarima yayi tare da sauke ajiyar zuciya yace "naci dazun a gida Bari inje kawai"
"To shikenan Sai Allah ya kaimu goben"
Gyada musu Kai kawai yayi ya juya ya fice jiki a sanyaye dukkansu kallo suka bishi dashi Mai cike da tausayawa...
******
Washe gari da sassafe yarima yayi shirinsa tsaf cikin kananan Kaya Riga jeans da polo shirt masu kyau Wanda sukai matukar amsar jikinsa,Amma hakan be hana Rama fitowa a jikinsa ba fuskarsa tayi fayau kamar yayi zawo da amai,A can fadar sarki ya tarar da a halin gidan dukansu,bayan ya gaida iyayen nasane sukayi Masa adduar samun nasara sanan kannensa biyu suka fada Masa bukatarsu nason zuwa kallon shariar,jinjina musu Kai yayi a shirye suke Nan da Nan aka bada Motoci da matakan tsaro wadanda zasuyi musu rakiya zuwa kotun....
*******
*COURT*
Mutanene cike da kotun har waje wadanda keso suga yadda wanan shariar zata kasance,
Kallo daya zakayima kotun, ka tabbatar ba karamar Sharia za'ayiba ,duba da yadda take cike makil da da'n adam.....
![](https://img.wattpad.com/cover/191531360-288-k885650.jpg)
YOU ARE READING
Anyi Walk'iya.......
Historical FictionBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...