16

1.7K 116 2
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS* *ASSOCIATION💡*

   *NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

             16

  Juyi kawai yakeyi Akan makeken gadonsa da tunani cunkushe a cikin ransa babban farin cikinsa shine wanan shiga kotun da zaayi zaayine iya judges da lawyers abinda hajiya babba ke tunani ba hakan bane,Kuma Yana da tabbacin insha Allahu sukeda nasara Dan dik wata hujja da zai gabatar ya Gama tattarata sanan shi kansa yasan tarko ya Dana Mata ta manta da cewa Yana daya daga cikin judges na supreme Court,kwakwakwarta ta toshe Akan manta cewa supreme Court ita ce kotun karshe dik fadin kasarnan matukar aka daukaka dik hukuncin da suka yanke shine dai dai....wani malalacin murmushi ya saki a cikin duhu Wanda shi kansa besan yayisa ba.....haka yayita tunani kala kala game da rayuwa gabaki daya har bacci barawo ya sacesa.....

********
  Tunda garin Allah ya waye Fatima ke faman kuka a daki dik ta Gama tadawa barrister hauwa hankali,gefenta take zaune ta zuba Mata ido tana kallon yadda take kuka idanuwanta sun kumbura fuskarta ta kode saboda kuka,

  Cike da damuwa barrister hauwa ta dafa kafadar Fatima tace"wai Fatima kukan me kikeyi haka?so kikeyi ki janyowa kanki rashin lafiya ko?jiya Aysha tacemun haka kika kwana kina Kuka inaso insan kukan na meye ne"

  Cikin kuka Fatima ce "Abla(yadda taji Aysha na Kiran barrister hauwa) hankalina a tashe yake idan na tunada abinda Yaya yarima yace wai yau zaa mikani hannun hukuma gobe zaa Kara mikani kotu sai inji tamkar in hadiyi zuciya in mutu"

  Murmushi wanan karon barrister hauwa tayi sanan tace"to maida wukar ki kwantar da hankalinki babu me mikaki hannun hukuma shima kansa ne yayi zafi ya fada Miki hakan,wanan kotun ba irin wadda akaje bace wanan kotun badake zaa shiga shariah ba kina zaune a wani waje zai shiga su gabatar da komi ya fito saidai idan an nemi a gankine Amma babu inda zakije kinji kanwar ablah"

  Kuri da ido Fatima tayi Tana kallon barrister hauwa batare da ta gasgata maganarta ba gani takeyi kamar ta Fadi hakan ne Dan ta kwantar Mata da hankali,..

  Murmushi barrister hauwa tayi sanan tace"baki yarda da maganata ba ko?kin manta Nima barrister ce Kuma nasan komi Akan shariah ki yarda da maganata babu inda zakije yau kina cikin gidan Nan kinji"

   Gyada Kai tayi tasa bayan hannunta ta share hawayenta ta durkusar da kanta kasa....

  "Fatima ki dau breakfast dinki kici kafin ya huce Kinga babu kyau Zama da yunwa"

  Juyowa Fatima tayi ta dauki kofin da aka hado Mata tea Mai kaurin gaske ta janyo plate din soyayyen dankali da kwai tafaraci....

*********
Koda yarima ya shigo gida a shirye cikin manyan Kaya ya Sanya shadda Mai ruwan toka kansa babu hula ya nufi bangaren mahaifiyarsa a can ya tarada khausar zaune Tana ganin ya shigo ta Mike ta fita,dukkansu sai suka bita da kallon mamaki don Basu taba ganin hakan ba....

  Gefen mama ya zauna ya kawo gaisuwa ta karba masa babu yabo babu fallasa sanan shiru ya biyo baya....

  Mama ce ta katse shirun da cewa "sai Ina Kuma ranka ya dade"fuskarta a daure tayi maganar

  Murmushi yayi Jin abinda tace don yasan haushinsa takeji gyara Zama yayi sanan yace"zan fita zanje can Court of appeal ne inji yadda abun yake"

  Ajiyar zuciya mama tayi tace"kadaibi a hankali sanan Ina maka fatan alheri bazan taba hanaka abinda zakayi ya amfanar da Kai duniya da lahira ba Domin a hakikanin gaskiya nasan cewa abinda zakayin abune Mai kyau Amma hatsarinsa nake hango Masa dikda dai inayi maka adduar fatan alheri da nasarori a rayuwa"

Anyi Walk'iya.......Donde viven las historias. Descúbrelo ahora