🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
_Sakon gaisuwa da fatan alheri gareku mutanen_ *KUNDIN HASKE* , _uoum sadeek,hussy luv, hauwa isah ibrahim,bawa subee,fulani ummu Ahmad,asmaul husnan mom,Maryam sabiu....._ *da dik Wanda ban Kira sunansuba Kuna raina*_Mutanen gidan uwata Kuma ban manta daku ba_ *TASKAR BILLY GALADANCI*.. _Hindu,teemah imran,maman_ _ameena,Fatima Hassan,mama faruk,...babbar_ _antyna_ *meenath kt*, _Nana Khadija,da'iman,shamsiyya_ _bilyaminu_ ......🤦🏽♀🤦🏽♀🤦🏽♀ *bazaku fadu dukaba dik Wanda beji sunansa ba register batazo kansaba Amma Ina mishi sonso😍*
41
Mikewa zaune yayi Yana mutsittsika Ido sanan ya dire daga hannunsa sama ya kashe murya "ni a daukeni nima ayimun wankan"yadda yayi maganar tamkar karamin yaro ba karamin dariya ya Bata ba....dariya ta shiga shekawa Tana nunasa da yatsa yadda ya makale hannu da kafada,
"Hebeeb ka ganka kuwa saikace jariri?tabdijan walleh ban iya daukarka" takara kwashewa dariya Tana tsalle,
Mikewa yayi yayo kanta suka shiga zagaye dakin Yana biye da ita Tana gudu har tagaji ta fada Kan gado rigingine ya Haye kanta Yana maida numfashi....kallon fuskarta yakeyi yadda Tasha kwalliya tamkar ba itaba ya sumbaci lips dinta "babyna kinyi kyau kin ganki kuwa?"
Dage Masa gira tayi "kamar?"
"Kamar sarauniyar barayar Zaki".....wani kayataccen murmushi tayi itama tayi kissing dinsa a lips dinsa sanan tace "itace"...
Kwantar da kansa yayi a kirjinta Yana sauke numfashi yanajin sautin bugun zuciyarta kussn mintuna hudu,...gajiya tayi tasa bakinta daidai kunnensa"ranka ya dade zamuyi latti fa"tasa hannunta Tana shafa sumar kansa Wanda yasashi lumshe idanuwa Yana budewa,a hankali ya shiga dagata har ya Mike tsaye Yana binta da mayen kallo Wanda yasata saurin mikewa Domin Sarai ta fahimci abinda yakeso Dan tagani a kwayar idonsa,
Jallabiyar jikinsa ya cire ya nufi bathroom dinta,har ya kai kofa ya tsaya sanan ya juyo yace "jeki daukomin kayana a dakina"
"Owk ranka ya dade"....
Murmushi ta sauke ganin shigarsa bayi ta Mike da sauri ta bude kofa ta fice,ta rufo koferta....
Cike da nishadi take takunta harta karashe sauka kasa,...tasha mamakin ganin deejahmah zaune da kayan bacci a wanan lokacin da yake safiya Dan batai tunanin Tana tashi da wuri ba,
Har ta wuce ta dawo "barka da tashi"...."barkanki dai uwar gida sarautar mata yaudai zakiyi ritire daga dakin Mai gida mannewar haka ta Isa da jaraba sai aba masu waje wuri"....
"Gaskiya na tayaki murna kasancewar Zaki dandana niimar dana da'ndaneta na rage....ba haka Rai yaso ba kanin miji yafi miji kyau"ta saki wani malalacin murmushi tai wucewarta side dinsa zuciyarta fesss cike da nishadi haka ta fito hannunta rike da kayansa har Zata wuce deejahmah ta dakatar da ita da fadin "idan kin shiga kicewa mijina inada bukatar ganinsa"
Murmushi Fatima ta sauke "karki damu zan fada Masa Amma saidai bazaki samu ganinsa yanzun ba Domin wanka yakeyi sai ya shirya matarsa Zata sanar Masada amaryarta nason ganin Mai gida"....
"Karya kikeyi baki isaba wallahi a dik lokacinda naso ganin mijina zan ganshi ba sai kinbasa umarni ba"
Dage kafadarta Fatima tayi hade dayi Mata gwalo tayi sama a guje Tana dariya.....
ŞİMDİ OKUDUĞUN
Anyi Walk'iya.......
Tarihi KurguBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...