50

2.8K 142 18
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

  *NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

                    50

A Daren ranan yarima ya sanarwa da Mai martaba samun mahaifiyar Fatima Wanda yayi tsananin farin ciki da Jin hakan....Nan da Nan yasa aka sanar da akwai kwarya kwaryar liyafa washe gari ta taryar mahaifiyar Fatima zuwa masarautar barayar Zaki Kuma matar tsohon sarki Marigayi....

********
  Washe gari yarima ya sanarwa da deejahmah samun mahaifiyar Fatima....saboda tsananin farin ciki har kuka tayi na Taya Fatima samun mahaifiyarta dikda Fatima a gidan kakaninta ya barota Dan zasu taho dasu zuwa masarauta...

  Duban deejahmah yayi ya shafa kanta saboda tsananin tausayinta da yakeji yadda lokaci daya ta canja daga yadda  take dik jikinta ya mutu tayi wani sanyi...

"Ki shirya dakyau kiyi Shiga ta alfarma saboda Mai martaba yace zaayi biki ne sosai na taryar mahaifiyar Fatima"

  Kashe Masa Ido tayi hade da lallausan murmushi "yadda kace haka zaayi ranka ya dade"...rungumeta yayi Yana jujjuyata a sama Tana kyalkyala dariya...

********
  Wasu tsadaddun Kaya ummu tabawa bilkisu ta Sanya masu shegen kyau tayi kwalliyarta ta alfarma tamkar ba ita ba dik inda ta gifta ummu sai ta kalleta tausayin yarinyar takeji yadda take rayuwa Babu iyaye Kuma Bata damu ba tasawa zuciyarta hakuri da dangana...

"Bilkisu Niko idan bazaki damuba zanyi Miki wata Yar tambaya"ummu taiwa bilkisu maganar cike da kulawa,

  Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta kasa Tana Wasa da Yan yatsunta,

"Shekaran jiya na ganku keda Dana Ahmad a jikin mota yadda kuke magana sai Naga tamkar akwai wata alaka a tsakaninku kedashi"

  Murmushi kawai bilkisu takeyi batare da tace komiba,....ummu ma Yar dariya tayi "to kodai tuwona Mai na zaayi ne keda Dan nawa?Dan gaskiya Kun matukar dacewa da juna"

  Mikewa bilkisu tayi tsulum batare da tacewa ummu komiba ta shige tsohon dakin Fatima na da,....

********
  Da yareema da deejahmah suka tafi gidan kakannin Fatima,

  Deejahmah Tasha mamakin ganin yadda suka tarbeta hannu biyu biyu tamkar Yar da suka Haifa haka mahaifiyar Fatima ta rungume deejahmah a jikinta,

  Fuskar Fatima dauke da murmushi take duban deejahmah dik yadda ta sauya tamkar ba itaba da abin mamaki yake Bata da Bata yarda da deejahmah ba dik tunaninta kissa ce kawai takeso tayi Mata Amma yadda taga deejahmah na shisshigowa lamarin nata yasa ta Dan saki jiki da ita,

  Wani irin kallo Mai cike da shauki da tsananin soyayya yarima ke jifan Fatima dashi ya kasa dauke idanuwansa daga gareta ya rasa dalilin da yasa Fatima ta Shiga ransa fiye da kowa a rayuwarsa....ga wani sabon sonta da yake ji a dik jijiyoyim jikinsa musamman yanzun da take dauke da gudan jininsa a jikinsa....

  Wucesa tazo yi ya ruko hannunta Yana murzawa hade da sauke ajiyar zuciya Yana Shirin janyota jikinsa deejahmah tayi Dan gyaran murya "malam ka Bari dai kuje gida tukunna ni banaso kasa Yar uwata Jin kunya....Dan yanzun da zarar aka shigo aka ganta a jikinka Kai ba kunyar da zakaji itace zataji kunya"...Tai maganar cike da zolaya....

  Turo baki Fatima tayi cike da shagwaba ta dubi Deejama "kina ganin ko tausayina bayaji so yakeyi yamun mugunta ma"

  "Yi hakuri rabu dashi zamu Rama Bari muje gida yau ai a gidanmu zamu kwana koh?injidai Zaki bimu"

  Gyada Mata Kai Fatima tayi tana murmushi,

  Kallonsu yakeyi cike da shaawarsu lokaci daya ya tsunci kansa cikin tsananin farin ciki....

Você leu todos os capítulos publicados.

⏰ Última atualização: Sep 10, 2019 ⏰

Adicione esta história à sua Biblioteca e seja notificado quando novos capítulos chegarem!

Anyi Walk'iya.......Onde histórias criam vida. Descubra agora