11

1.4K 131 0
                                    

*🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*

*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA SLIMZY*

_Wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*

              11

Kuka sosai mukeyi nida Yar uwata bilkisu Babu me lallashin wan hakikanin gaskiya tausayin kanmu nakeji a wanan lokacin saboda rayuwar da mukeyi ta rashin gata,uwa uba rashin gata yasa ake dibarmu Ana lalata Mana rayuwa,inda a gaban iyayenmu muke hakan bazata faru ba....

  Kwana nayi Ina zubda hawaye wanda bansan dalilinsaba haka kawai na tsinci kaina a matsananciyar damuwar da bansan dalilinta ba.....

********
Washe gari da sassafe aka kawo mota yayinda dukanmu muka shirya tsaf damu muka karya da kunu da kosai ,misalin karfe bakwai da rabi mukaita shiga mota....sauran yara Yan uwanmu Sai fatan alheri da samun nasara sukeyi Mana,

  Har na shiga mota na fito na rungume bilkisu Yar uwata hade da bubbuga bayanta nace "ki kula da kanki Sai Allah ya Kara hadamu"

  Kwallar da nake boyewa CE to sulalo a idanuwana,ban Bari taganiba nasanya hannuna na goge na kauda fuskata na shige motar aka jamu,Sai daga musu hannu mukeyi.....

  Tsagaitawa Fatima tayi da labarin ta kalli barrister hauwa wadda ke kuka harda majinu Tana kallon Fatima cike da tsantsar tausayawa ,girgiza Kai Fatima tayi itama Tana hawayen ta cigaba da cewa....

   Makarantar da zaa kaimu yin jarabawa Nan aka nufa damu,Sai kallonmu sauran yara sukeyi da jamaar wajen mussaman da akace yaran gidan marayu ne wasu na tausaya Mana wasu najin kyamar mu,nidai ko a jikina tunda nasan cewa baninayi kainaba Allah ne yayini,a haka aka shigar damu ajin jarabawa inda mukabar hajiya da haruna zaune jikin mota suna jiranmu.

  Nice farkon fitowa da aka Gama babu inda na nufa Sai wajen motar mu,a Nan na tararda su hajiya halima,tun daga nesa sukemun faraa itada haruna Sai jikina be bani ba Amma Sai na kauda zargi a zuciyata Dan babu kyau....

  Dan durkusawa nayi nace "sannu da hutawa hajiya"na sunkuyar da kaina,

  Washe Baki hajiya tayi tace "Fatima kune zaayiwa sannu kuda kukasha Zama a ciki,Allah dai ya bada saa Fatima"

  "Ameeen hajiya"

Na koma jikin mota na jingina,
  Malam haruna ne ya juyo ya miko min lemon gora guda daya da fanke yacemun ga nawa sauran ma zaa Basu nasu,

  Hannuna na rawa na amsa nayi Masa godiya,na tako na karasa Kan wani benci wajen Mai Saida abinci na zauna Ina ci Ina kurban lemon Nan saboda yunwar da nakeji,minti minti Ina da'go Kai in kalli wajen dasu hajiya ke zaune tare da haruna saboda kada Yan uwana su fito a tafi a barni ,Sai Inga Basu fitoba hajiya CE ke shewarta itada haruna a wajen.

  Biyu na Raba lemon da fanken na ajiyewa bilkisu Yar uwata Wanda Zan Kai Mata a matsayin tsaraba idan na koma,Ina Nan zaune shiru shiru nafara gyangyadi wani irin bacci Mai nauyin gaske yake dibata Ina wartsake idona,tun Ina controlling kaina har na kasa,na kifa kaina a cinyata na Soma bacci......

  Zuwa wannan lokacin kukan Fatima ya tsananta,barrister hauwa ta dafa kafadarta tace"daure ki karasamun labarin Nan Fatima Kinga ankusa zuwa tafiya dake ga yamma tayi"

Share hawaye Fatima tayi ta cigaba da magana....

  Wanan baccin da nayi shine Wanda ban farkaba Sai cikin dare Wanda Ina bude idanuwana na ganni Akan babban gado Wanda tunda nazo duniya ban taba Hawa irinsa ba,

  Zumbur na Mike nafara waige waige,Ganin irin dukiyar dake cikin dakin tamkar dakin wani sarki ko shugaban kasa,kici kicin sakkowa nafarayi Sai naji motsin bude kofa da sauri na waiga,

Anyi Walk'iya.......Where stories live. Discover now