🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
35Hajiya zainab ita tafara Isa fada bayan yarima,a can ta iske fatima a gaban Mai martaba Tana faman zubar da hawaye tamkar an bude famfo kallo daya tayi mata ta kauda kanta saboda tsananin tausayin yarinyar da ya lullubeta take taji idanuwanta sun ciko da hawaye ta nemi gefen da Fatima ke zaune ta zauna da kyar ta bude baki tace "ya Isa haka Fatima kiyi Shiru insha allahu komi zaizo karshe Domin wannan cin zali yayi yawa na tabbatar da Mai martaba adalin sarki ne zai duba lamarinki kinji share hawayenki"ta kamo Fatima zuwa jikinta ta shiga goge Mata hawaye,a haka su hajiya babba suka shigo kowa ya hallara cikin fadar...
Wanan karon sarki ransa yayi mummunan baci a fusace yake sai kaiwa da komowa yakeyi Saida kowa ya Gama zuwa sanan yanjuyo da kakkausar murya ya Soma magana "Kun bani mamaki kun zubarwa kanku da mutunci sanan Kun dauki wuka Kun dabawa cikinku yadda kuka taru waje daya Kuna hayaniya kuka kokarin fallasa asirin cikinku na tabbatar cikin gidan Nan ba zallar Yan uwa bane ciki harda na waje,yau Koda Yan uwane bai kamata kutaru ku nemi zubarwa da wanan masarautar mutunci ba "
Gyara Zama ummu tayi ta ce cikeda ladabi "Allah ya huci zuciyar Mai martaba baa kyautaba sharrin shaidan ne"
"Babu ruwan shaidan a wanan lamari sai sharrin zuciyoyinku wadanda gabaki daya Babu abinda kukasa a Rai sai son Kai da son zuciyane"
Ya juyo inda hajiya babba ke zaune kanta a kasa Tana famar hura hanci "hajiya safiya kinbani mamaki ban taba tunanin ko kowa zaiyi rashin hankali ke zakiyi ba"
Da sauri ta dago "ranka ya dade..."
"Dakatamun hajiya Babu abinda kowa zaicemun a wajen Nan Domin ba yarda zanyi daku ba tunda kunci amanata kunci amanar marainiyar Allah Kuna neman aikata lahira to na yanke shawarar dauketa daga gidan Nan kafin ku kasheta" ..
Jin haka yasa hajiya zainab saurin fadin "Allah ya huci zuciyarka ranka ya dade ai idan aka Bari har aka fita da yarinyar Nan zuwa wani waje Domin rukonta munyi asarar ladan da muke samu ta sanadiyyarta bazan taba bada goyon baya a fita da yarinyar Nan daga gidan nanba"...Harara kawai hajiya babba ke jifan ummu da shi,Jin furucin da tayi,
"Yanzun ke zainabu nasan kinada hankali Kuma kin girmi rahina kinsan ya kamata inaso ki fadamun yau abinda ya faru a cikin gidan Nan a gaban kowa Dan banaso daga baya inji wani gutsiri tsoma Yana tashi...
Murmushin Jin Dadi hajiya zainab tayi sanan ta gyara Zama murya kasa kasa ta kwashe kaf abinda yafaru Wanda tagani a idanuwanta ta fadawa Mai martaba sanan ta Kare maganarda "dama da Naga haka shine na yanke hukuncin yanta yarinyar ta dawo hannuna da Zama tunda ni dama Allah be bani haihuwar ya mace ba sai in riketa har zuwa lokacinda zaayi aurenta da shi kabirun,...shine nakeso a yanta ta"
Ran Mai martaba ba karamin baci yayiba a fusace ya karbe zancen da "ai yarinya ya'ntacciya ce Domin yace kamar kowa tunda baa yaki aka siyota a kasuwar bayi ba balle a kirata da baiwa sanan maganar kikeso a yantata?aike kin Isa ki yanta kowa a gidan Nan Domin inda ke macece da idan na mutu banida da' namiji kece Zaki gaji mulki bayan ni Domin bayan yayana da Allah ya saukarwa kaddarer rashin lafiya ai saini saike sanan ita rahinar saboda haka ni da kaina na ya'nta Fatima na Kuma danka Miki amanarta halak malak harabada nabaki Fatima diyarkice"
Juyowa hajiya zainab tayi ta kalli Fatima ta bude hannuwanta ta fada jikinta ta rungumeta Fatima ta fashe da kuka Mai ban tausayi,
Mai martaba ya dubi Fatima wadda ke faman kuka yace "ke Fatima daga yau na mallaka Miki kanwata jinina ta Zama mahaifiyarki Niko dama a matsayin ubanki nake Kuma harabada a haka muke har karshen rayuwarmu idan Allah ya nufemu da ganin iyayenki shikenan idan bamu gansuba kina Nan a Yar amanarki kinji?ki share hawayenki inajin kaunarki cikin jinin jikina kamar khaussr da ummul khairi".
![](https://img.wattpad.com/cover/191531360-288-k885650.jpg)
YOU ARE READING
Anyi Walk'iya.......
Historical FictionBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...