🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡
*NA:SLIMZY✍🏼*
_wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
*Wanan shafi kyautace zuwa gareki mommah* ( *_BILLY_* *_GALADANCI_* )... *kiyi yadda kikeso* *dashi, Ina yi Miki* *son so...* ❤😍22
Kallon mahaifiyarsa yayi a fakaice,bama ta kallon inda yake don yadda ta nuna tamkar batasan da zamansa a wajenba,
Yakai minti goma a zaune sanan ya Mike har ya juya hajiya babba ta tsaidashi ta hanyar yi mishi magana "A Ina zaka samo bayin kamar yadda kace"....batare da wata faduwar gaba ba yace "akwai wani kauye da Ahmad yacemun anyi rigima a wajen an zube mutane Kara zube wasu Ana dibarsu aikatau wasu Ana shigowa dasu cikin gari suna bara shine nace zanje in duba ko Yan Mata biyu ne asamo tunda Naga kuyangi sunfi yawa a gidan"
"Hakan yanada kyau"....juyawa yayi batare da yace komi ba ya fice abinsa....
********
Office yasamu Ahmad abokinsa Nan suka zauna yake bashi labarin shawarar da ya yanke...."Yanzun kana ganin dakko yaran Nan ka kawo gidanku baka kinkimowa kanka wata rigima ba?"
Dan Bata fuska yarima yayi yace "wace irin rigima"
"Dik ranan da asiri ya tonu har sarki sai yayi fushi dakai Kuma zaka Kara jefa kanka cikin zargin da akeyi maka"
Murmushi yayi yace "dik halin da zan shiga zan shiga matukar zansa Fatima farin ciki,sanan kafin insamu hajiya na gindaya Mata sharudda Akan hakan".....Nan yarima ya kwashe yadda sukai da Fatima ya fadawa Ahmad,
"Allah ya baka ikon rikon maraya cikin gaskiya da Amana ya baka lada"
"Ameen yanzun inaso in zauna a Nan ne zuwa ka tashi office dinka sai ka rakani muje can gidan marayu idan mun daukosu mukaisu gida tare da Kai Dan na fadawa su hajiya kauye zanje daukosu"
Dariya Ahmad ya sheke da ita sanan yace "dadina dakai fasaha,ni wanan tunanin be shigomin a raiba,shiyasa ka zabi dik inda zakaje kaje batare da excort ba ko?"
Murmushin gefen fuska yarima yayi ya shafa Dan sajen fuskarsa ya ce'ka cika sa ido"
***********
A gidan Ablah kuwa tunda ta tashi take tunanin yadda zaayi taje taga Fatima,...aikace aikace takeyi itada Yar uwarta Aysha Saida suka Gama suna zaune a parlor suna hutawa ablah ta kalli Aysha tace"Niko Aysha inaso inje Inga yarinyar Nan Fatima Inga halin da take ciki"
"Ablah kina ganin zaabarmu muganta?gidan sarauta fa?"
Dan jinjina Kai Ablah tayi sanan ta jingina da jikin kujera tace "zaabarmu insha Allahu ai yarima Yana Nan ki shirya anjima zankira oga a waya in sanar Masa da inason zuwa ganin Fatima sai muje da yamma ko"
"To Allah ya kaimu"
"Ameen"
*********
Tsaf deejahmah ta shirya ta dibi bayi da kuyangin gidansu Yan rakiya ta shiga mota Suma suka shiga tasu aka jata zuwa gidan sarki........
Tafiyar mintuna kadan ta kawosu gidan kasantuwar Babu wani tazara tsakanin gidan sarki da gidan galadima Wanda ya kasance shine mahaifin deejahmah.....
A parking space sukayi parking deejahmah ta fito Tasha kwalliya ta kece raini Tana sanye da super English atamfa anyi Mata dinkin Riga da skirt ya zauna Mata dasss a jikinta ta kawo mayafi ta yane kanta dashi Wanda ya rufe har Rabin jikinta,fuskar Nan Babu annuri sai yatsina takeyi bayi da kuyangin ta suna biye da ita wasu a gabanta wasu a bayanta tamkar itace Yar sarkin yadda take taka kasa ma abin kallo ne dik inda ta gifta maaikatan gidan sarki zubewa kasa kawai sukeyi suna kawo gaisuwa,saidai kawai ta daga musu hannu,a haka har ta Isa babban sashin gidan....

YOU ARE READING
Anyi Walk'iya.......
Historical FictionBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...