20

1.6K 106 2
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *NA:SLIMZY✍🏼*

_wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

     
     *SAKON GAISUWA DA FATAN ALHERI* *GAREKU SUMAYYA* *ADAM* ( _fauza house of_ _novels_ ) *TARE DA* *MOM SAYEED* *DA* *NOOR* ( _Haske_ _fans club_ ), *UMMU* *RAMLAT* ( _slimzy_ _novels_ )...... *SON* *SO FISABILILLAH* 😍👏🏼

                    20

  Ilahirin jikin Fatima Babu inda baya rawar sanyi saboda hunturun da akeyi a wanan lokacin sanan a tantagaryar kasa take kwance ga sanyin tiles da ya dauka....baccin kansa ya gagareta saboda tsabar sanyin da takeji juyi kawai takeyi kafadunta sunayi Mata zafi gashi ganin Daren takeyi yayi Mata tsayi....cije lebenta tayi saboda tsabar sanyi har saida ya fashe jini ya fara fitowa,runtse idanuwanta tayi wata kwalla Mai zafi Tana gangaro mata a fuska a haka har wahalallen bacci ya dauketa,sai Kiran sallahr asuba ta farka da sauri ta kwashe Dan kwalin data shimfida da hijabinta da take lullube dashi ta say jikinta,

   Wata Yar kofa ta nufa batare da sanin inda zatajeba Tana shiga taga ta Kara karo da wata kofar a rufe ba tare da wani tunaniba ta tura kofar aikuwa tayi kicibis da wani katafaren bedroom Wanda yasha kayan more rayuwa da rantsatsen gado ta kunna Kai cikin dakin aikuwa furgigit wadda ke kwance a katafaren gadon ta Mike da sauri Tana kallon Fatima sanye da hijabi da sauri ta laluba hannunta zuwa gefen gadonta ta kunna globe ido hudu sukayi Fatima taja da baya da sauri ,

  Wani durowa hajiya babba tayi daga gadon Tana fadin "dawo Nan dama bacci rabi da rabi nakeyi saboda tsoron Kar a kashemu ubanme ya kawoki dakina kinzo ne ki karasani?kamar yadda kika kashemun da'be ishekiba koh"

   Ko Ina a jikin Fatima rawa yakeyi ji takeyi tamkar ta saki fitsari har ga Allah Koda ta bude kofar batayi tunanin dakin wanan azzalumar matar bane tayi tunanin dakinsu khausar ne don dakunan gidan da kofofin gidan kamanceceniya suke da juna......

   Wani mugun kallo hajiya babba ke jifar ta dashi ta Kara fadin "uban me ya kawoki Ina tambayarki?"

   Dago idanuwanta tayi sukayi ido hudu ta Kara saukesu kasa bakinta na rawa tace"kiyi hakuri wallahi bansan dakinki bane Nan wani dakin nake nema inaso in shiga bayi inyi alwala inyi sallah"

   "Dakin ubanki kike nema?ko dakin tsohon kwarton naki daya kawo ki kike nema kabiru?kinbiyo duhu kuyi karuwancin ne?to fitarmun a daki tun ban illatakiba cikin Daren nan"

  Da sauri Fatima ta juya har Tana hardewa kamar zata kife ta fice a dakin,hajiya babba ta bita da wani mugun kallo Mai cike da tsantsar tsana da kyama.....

   Tana fitowa taci Karo da wata kuyanga hannunta dauke da tsintsiyaye manya da kanana da alama itace Mai sharar gidan kallonta kuyangar tayi ta kauda Kai har zata wuce Fatima ta tsaidata da cewa"Dan Allah Ina zansamu bayi inyi alwala?"

   Hannu tasa ta nuna Mata wata hanya ba tare da tace komiba ta wuceta da sauri don kar ma wani ya ganta tanayiwa Fatima magana,kofar data nuna Mata ta shiga aikuwa saiga bayika a jere daga gani kasan na bayin dake bangaren ne ,ciki ta shiga ta Kama ruwa tayo alwala ta fito tazo parlor ta tada sallah....bayan ta idar da sallahr ne Tana zaune gari ya danyi Haske yarima ya shigo sanye da jallabiya daga gani masallaci ya dawo Yana shigowa yayi tozali da ita zaune Tana adduoi hannunta a sama juyowa yayi ya taho wajenta ya nemi gefe ya zauna har saida ta shafa,

  Sunkuyar da Kai tayi gefe tace"barka da tashi ranka ya dade ,fatan ka tashi cikin koshin lafiya"

  Murmushi yayi yace"na tashi lafiya ranki ya dade Dan kema yanzun kin Zama Yar gidan sarki Dole a ce Miki ranki ya dade"

Anyi Walk'iya.......Where stories live. Discover now