08

1.6K 107 1
                                    

*🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*

*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA SLIMZY*

_Wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*

           08

"Yakubu banason a samu matsala Akan wanan aikin Dana saka ka tabbatar da kayi yadda nace baasamu matsala ba,banaso video din Nan ya fito complete idan akaje kotu"

  Dan rankwafawa yakubu yayi yace "insha Allah zaayi yadda kikace ranki Shi dade,ai Dole abi umarninki ranki Shi Dade"

  Wayarta ta Ciro ta Mika Masa "samun number ka a Nan sauran bayani zanyi maka aike"

  "Nagode ranki ya Dade Allah ya Kara girma da arziki"

Ba tare da ta amsaba ta juya suka fice a office din,securities da dogarawa suka take musu baya har wajen motocinsu....

******
"Wanan manakisa ce babba ake Shirin shiryawa Dan anga yarinyar batada gata to wallahi karyane,wanan maganar ruwan kwando CE Babu yadda zaayi ace Ana rikon yaro a gidan marayu ace baasan da zamansa ba bayan dik wani yaro da rikonsa zai koma hannun gwamnati Sai an rubuta sunansa da komi da shekarar da aka kawosa da Wanda ya kawoshi wannan maganar banza ce barrister"

  Girgiza Kai yarima yayi Sai yanzun hankalinsa ya Dan kwanta Jin wanan maganar daga bakin barrister Abdul"Ni kaina abin ya daure mun Kai domin Ni shaidane Akan zaman Fatima a gidan marayu saidai babu yadda zanyi in furta hakan tunda ga yadda shariar tazo bani nake kareta ba"

  "Ai ka kwantar da hankalinka Dole ne a koma Ayi bincike tsattsaura Akan gidan marayun Nan domin idan haka ne akwai wata makarkashiya ai wanan abin da sukayi tamkar sun nunawa duniya cewa Suma maha'inta ne ,sanan Babu gaskiya a lamarin Babu Amana"

  Sai yanzun yarima ya samu karfin gwiwa da kalaman Abdul,hankalinsa ya Dan kwanta yace "to yanzun barrister menene abun yi?me kake Ganin zaayi?"

"Ni da kaina zanje police station din,inyi magana da babban DPO din Akan Ni ban yarda da wanan binciken da akaje akayi ba a gidan marayu batare da dauko list din sunayen yaran dake gidan ba,ai a master list ne idan har baaga sunan Fatima da hotonta ba to shine zaa tabbatar da baa gidan marayu take ba wanan karon Dani zaaje saboda akwai binciken da nakeson yi a cikin gidan marayun"

  Jinjina Kai yarima yayi cike da gamsuwa yace"yauwa barrister Abdul Dan Allah kayi kokari Akan wannan lamarin a duba al'amarin marainiyar Allah dik duniya Fatima batada kowa Sai Allah Sai Ni"

  Kallonsa barrister Abdul yayi "ban gane inda maganarka ta dosa ba me kake nufi?"

  "Marainiya ce kamar yadda kasani,sanan Kuma nine a matsayin gatanta na uwa da uba,sauran bayani zanyi maka Shi idan komi ya kwaranye,fatana be wuce a shiga wanan kotun da zaayi musamu cin nasara a wanan shariar"

  Kalaman yarima ya daurewa barrister Kai Amma Sai ya share yace"Allah ya bamu nasara ranka ya Dade insha allahu Fatima zata kubuta"

  Murmushi yayi yarima Wanda ya tsaya iya fuskarsa yace'abu na gaba shine yadda zaa Kara zantawa da Fatima Akan abinda ya faru Dan idan ban mantaba jibi ne zaa koma shiga kotu"

  "Wanan ba matsala bace insha allahu,gobe da safe nakeson zuwa station din yin bincike bazan taba nunar musu da nasan cewa sunyi bincike Akan Fatima ba Yar gidan marayu bace zanyi musu tambayoyine inji me zasuce sanan in gabatar musu da bayanin da nayi maka yanzun,sanan madam zansa ta Kara neman izinin Ganin Fatima domin ta zanta da ita a Karo na biyu"

   Mikawa barrister hannu yarima yayi suka gaisa hade da rike hannun nasa "nagode sosai barrister bansan da kalmar da zanyi amfani da itaba wajen nuna godiyata da jin dadina Akan wanan halarcin da kayimun nagode Allah ya saka da alheri"suka rungume juna....

Anyi Walk'iya.......Where stories live. Discover now