30

1.4K 85 2
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

  *NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

    
     _nagode da kauna_ @ *ZAHRA MAI GARI*.... _son so_ _fisabilillahi_

                30

  ********
  A gurguje bayan kwanaki uku da faruwar haka kusan tunda Mai martaba ya yanke wanan hukunci Fatima ke cikin azaba dik ta rame tayi bakin Kirin, kwana uku kenan batasa yareemah a idanuwanta ba ta shiga matsananciyar damuwa wadda tunda take Bata taba shiga irintaba....

  A bangaren yarima shima hakan ce ta kasance Domin kusan kullum cikin fakon Ido yakeyi ko zai ganta,saboda zamanta a gidan yasa ya mance da gidansa da yake bayan gari Wanda a al'asarsa ma can ne wajen zamansa zuciyarsa yauma sake sake kawai takeyi mishi Yana zaune ya rafka uban tagumi ya kurawa TV dake manne a bangon dakinsa Ido a zahirin gaskiya ba kallo yakeba ya fada duniyar tunanine...

  Yau kwana uku Fatima be gantaba ita Kuma Bata nemeshi ba me hakan ke nufi?yarinyar Nan kenan ba sonsa takeyiba dik abubuwan da takeyi mishi Tana yi Masa shine kawai bawai Tana sonsa bane ya shiga rigingimu kala kala daban daban akanta Amma ta juya Masa baya,bazai taba nemanta ba inhar Bata nemeshi ba tunda abin nata haka ne....

  Mikewa yayi ya suri makullan motarsa da wayoyinsa ya zura a aljihunsa ya fice daga bangarensa har ya Miko hanyar parking space ya juya yabi side din da akeyi Masa gini...

  Sauri sauri ya keyi ya tsaya daga Dan nesa kadan abin ba karamin mamaki yabasa ba ganin yadda cikin kwana uku ansa foundation gini ya Mika,zuciyarsa cunkushe da takaici haka ya juya ya  nufi motor park

  Sauri sauri bilkisu ke bin bayansa bai San da itaba ya shige motarsa yaja a guje ya bade wajen da kura....itama kallo ta bishi dashi haka ta juya jiki a sanyaye ta nufi cikin gida....

  A daki ta tarar da Fatima kwance sai rawar sanyi takeyi dik jikinta Babu inda baya rawa a kwance take saman tiles Babu arzkin abinda  zata shimfida ta kwanta ,gefenta bilkisu ta zauna fuskarta dauke da damuwa ta sa hannu ta taba wuyan Fatima Wanda yayi zafi rau

"Fati nabi bayan Yaya besan Ina binsa ba ya shiga motarsa ya wuce dama tunda ya fito daga bangarensa Ina fakonsa inga inda zaije in sanar Masa da halin da kike ciki sai Naga yabi bangaren can da ake gini ya dade wajen tsaye sanan ya Mike wajen motoci Ina kiransa beji ba haka ya wuce"

  Runtse idanuwa Fatima tayi hawaye na gangarowa ta gefen hancinta masu zafi "ban taba tunanin yareemah zaimun haka ba,Saida ya samun soyayyarsa da kaunarsa sanan yake neman juyamin baya idan ko haka ne na shiga babban bala'i"

  Cikeda alhini bilkisu ta matso kusa da ita sosai ta kamo hannunta "kiyi hakuri ki kyautata zato akansa kila abubuwa ne suka Sha Masa Kai saboda aurensa Nanda sati biyu da Yan kwanaki ne Kinga kila akwai hidimomin da yakeyi kuma a kwanakin Nan Ina lura be shigowa sai dare kiyi hakuri"

   Kuka Fatima takeyi harda shassheka "tun kafin yayi aure kenan ya Soma canjamin inaga yayi aure ni danasani ma da ban jefa kaina cikin matsala ba Dan tabbas soyayya matsala ce bilki"

  Rufe Mata baki bilkisu tayi da hannunta "karki Kara cewa haka wallahi Yana sonki kidai kwantar da hankalinki kila yanada uzuri ne karki zargeshi kinji Yar uwata?....yanzun Bari inje Kar hajiya ta nemeni"

  Daga Mata Kai kawai Fatima tayi daga kwance yayinda bilkisu ta Mike ta fice a dakin Fatima ta bita da kallo har ta bace....

********
Hajiya babba ce zaune a parlor gefenta lemon Zaki ne da ayaba Wanda bilkisu ke bare Mata Tana Mika Mata daya bangaren Kuma Mami ce kuyangarta Tana durkushe....

Anyi Walk'iya.......Where stories live. Discover now