🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
48Tallafe yake da Fatima a jikinsa Yana faman riritata sai zuba Masa shagwaba takeyi Tana kakkaucewa saboda ummu dake kaiwa da komowa daga daki zuwa kitchen dinta,..wayarsa dake gefensa ce ta hau ringing be dubi wayarba ya Kara rungumota jikinsa Yana famar shafa kanta,wayar ta tsinke a karo na biyu ta Kara shigowa Dan tsaki yayi "mtsww Wai waye ne kuma?"ya janyo wayar Yana kallon me Kiran,
Receive ya Danna ya Kara a kunnensa "umhmm ya akayi sarkin fada?"
Daga can bangaren aka bashi amsa da "ranka ya dade iyalan gidan malam liman ne yanzun Mai gadin gidan da yake nabashi number ta ya kirani yake sanarmun sun shigo gari tun jiya gobe Wai zasu tafi umara"....
"Ganinan zuwa sarkin fada ka kirani a kofar fada"ya datse wayar ya dubi Fatima da tunda ya fara wayar ta kafesa da ido dikda batasan me akeyi ba,
Gyarata yayi ya janyo pillow ya Dora kanta akai Sanan ya durkuso daidai fuskarta "zanje indawo kinji babyna ki kulamin da kanki kina bukatar wani Abu ne?"
Girgiza Masa Kai tayi tana binsa da kallo har ya Kai kofa ta tsaidashi "habeeby"....cakkk ya tsaya ya juyo a gaggauce "ya akayi Fatima?mekikeso ?"
"Ka fadamun inda zaka dik ka kidime sai kace wani Abu ya faru"....jimm kadan yayi Yana Dan tunani bayason sanar da ita koma menene Dan saboda yasan rigima zatasa mishi sai taje gashi ba lafiya gareta ba,
"Mai martaba ne yakeson ganina shine zanje bada dadewa zandawo kinji?"
Yatsina fuska tayi hade da tabe baki ta juyar da kanta gefe cike da kishi tace"kodai me martabiya ba,Kila ma wajen matarka zakaje"...
Agogo ya kalla 'koma menene sai na dawo "be jira cewarta ba ya fice,
Idonta yayi kwalkwal,Kila wajen matarsa zaije suci soyayyarsu ita Tana Nan shine zaiyi Mata wayau yace Wai me martaba ke kiransa,....janyo bargo tayi ta rufe har kanta ta shige Tana sharar hawaye saboda tsabar kishi da ya taso Mata....
**********
Bacci sosai Fatima takeyi lokacinda hajiya karama ta shigo sashen ummu Domin ta duba jikin surukar Tata ,dikda kunya hakan be hanata zuwa ba,
Bayan sun gaisa da ummu mama karama ta dubi sashin da Fatima ke kwance fuskarta tayi fayau ta Dan rame hancin Nan ya fito zirr,
"Wai hajiya zainab meke damun surukar Taki ne?umm?"
Yar dariya ummu tayi "diyar tawa karuwa muka samu"
Da sauri mama karama ta dubi hajiya zainab fuskarta dauke da murmushi "Masha Allah alhamdulillah Allah ya inganta "
"Ameeen ameeen"...ummu ta amsa fuskarta dauke da faraa....
********
Cikin parlorn baki akayiwa yarima ma sauki shida sarkin fada da Ahmad Wanda ya samesu a can,Sosai dattijom yasha mamakin Jin daga inda suke ya dade Yana nanata masarautar barayar Zaki a ransa...lokaci daya abinda ya faru a baya ya dawo Masa Wanda hakan ya haifar Masa da tsananin tashin hankali...m
"Kaidin waye a masarautar barayar Zaki?"....Saida gaban yarima ya fadi Jin tambayar da dattijon ya jefo Masa,
Da kyar ya hadiye mugun miyau ya Dan rusuna "nine kabiru da na biyu ga sarki Muhammad Wanda ke mulki yanzun a masarautar barayar Zaki"...
![](https://img.wattpad.com/cover/191531360-288-k885650.jpg)
YOU ARE READING
Anyi Walk'iya.......
Historical FictionBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...