🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*_Ina daukacin_ _jama'ar_ *KUNDIN* *HASKE?..* _wanan shafin kyautace ga dik wata member ta group din kundin_ _Haske,ku rarraba_ _Banda wawa😹_ 😹😹.....
28
Zaro ido Fatima tayi waje hade da sakin wani fitsari Mai zafi a tsugunne jikinta na faman karkarwa,a wanan yanayin da take ciki har gara Harbin kunama da balain dake Shirin samunsu,
Zagaye dakin kawai sukeyi suna Haske Haske Amma basuga kowaba,kusan minti arbain basuji motsiba tsaki isyaku yayi "Kai Amma yarinyar Nan Bata kyautamunba dik na Gama Shirina dazun Dana fita har jiko Nasha yadda zansamu karfin cin uban shegiya Yar taadda Mai kisan Kai sai gashi ta gudu,komi Daren dadewa tunda hajiya tabani go a head saina aiwatar da nufina"
Tsaki abokin yayi hade da kashe yar touch light dinsa yace "muje mu kwanta dare nayi dik Kai kasamun Rai wallahi"....Yana karasa fadin haka yayi gaba abinsa,
Jiki a mace isyaku yabi bayansa yanata jera uban tsaki haka suka fita suna waigen dakin....
Jin takun fitarsu da kamar minti goma Fatima ta saki sassanyar ajiyar zuciya hade da fashewa da kuka ,rike da kafarta take fadin "na shiga uku shikenan ajalina yazo".....
A guje bilkisu ta fito daga mabuyarta jikinta jike sharkaf tayo hanyar kofa Tana lalube,waigawa takeyi gefen hagu da dama "kina ina Fatima meyasameki?meya faru?"
Kuka Fatima ta Kara rushewa dashi hade da janyo jiki ta fito daga bayan kofar ta zube a kasa "ganinan bilkisu kunama ce ta harbeni"
Dafe kirji bilkisu tayi hade da zaro ido cikin duhu "kunama fa kikace,munshiga uku a Ina ta harbeki"
Cikin shasshekar kuka Fatima ta Bata amsa "a kafana"
Ai bilkisu batayi wata wataba ta daga kasan rigarta tasa hakori ta yago dogon kyalle tayo Kan Fatima Tana lalube da hannu kasantuwar akwai duhu sosai,....Kama hannunta Fatima tayi hade da fadin "gani nan"
Da sauri bilkisu ke zare Dara daran idanuwan Nan nata ta shiga nada Mata kyallen a kafar tanayi Tana daurewa tamau,yayinda azaba da radadi ke Dada ratsa sassan jikin Fatima ga karkarwa da jikinta keyi Nan da Nan zazzabi Mai tsanani ya rufeta....
Kallon bilkisu takeyi da rashin fahimtar wanan dauri da taiwa kafarta tamau "bilki kin dauremun kafa Tana karamun zugi da azaba Mai hakan ke nufi"
"Kiyi hakuri Fatima hakan shine mafita kafin safiya Domin k'arinta bazai rinka Miki yawo a jikiba kinji ki daure zuwa safiya musan abunyi"
Murmushi Fatima tayi hade da Jan majinar hancinta "abunyi kawai mu gudu na gaji da wanan azabar nagaji da wanan masifar"hawaye na Dada gangarowa a idanuwanta....
Cikin tausayawa bilkisu wadda itama zuwa yanzun ta karaya da wanan lamari Wanda tun kafin aje ko Ina masifa ta ishesu tace"ki kwantar da hankalinki Fatima wuya Bata kisa sai kwana ya Kare"
"Idan wuyar Bata kasheni ba ai ta wahalar Dani ko bilki,gaskiya nagaji bazan iya jure wannan masifar ba tun Ina kubuta watarana zaayimun abinda zai nakastamun rayuwa"
Hawayen da bilkisu ke boyewa su suka zubo Mata tasa hannu ta share "kece fa kike fadamana cewa bawa baya taba wuce kaddararsa,sanan bawa baya taba samun cigaba a rayuwa sai ya hadu da kalubale kala kala.....haba fati karki karaya Allah daya haliccemu Yana sane dake Wanda dik wuyar da kikasha kina jarinta zuwa yanzun ya rayaki kika girma da ranki da lafiyarki shi zai duba lamarinki"...
![](https://img.wattpad.com/cover/191531360-288-k885650.jpg)
VOUS LISEZ
Anyi Walk'iya.......
Fiction HistoriqueBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...