🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
47Basu iso gidan Mai martaba ba sai bayan sallar magriba,
Sai bayan an idar da sallah Sanan Mai martaba ya umarci sarkin fada da yayi Masa Kiran iyalansa dake cikin gidan,haka kuwa akayi hajiya babba da mama karama da afnan da khausar tare da yarima sai Fatima dake wajen dik suna zazzaune,
Gyaran murya Mai martaba yayi ya dubi malam sani dake gurfane Yana faman hada zufa saboda tsananin furgici da yake ciki a wanan lokacin,
Gyaran murya Mai martaba yayi Sanan yace "malam sani sunanka bawan Allah?"
Gabansa ya fadi ya Kara rusunawa "ehh ranka ya Dade sunana kenan"ya fada a furgice,
Ganin yadda dik ya tsure yasa sarki sassauta murya "ka kwantar da hankalinka bawan Allah Nan masarautace Mai cike da adalci da kaunar talakawa Dan haka Babu abinda kayi Babu abinda zaayi maka cikakken bayani mukeso kawai kayi Mana game da wanan baiwar allahr dake cikin hoton Nan"ya mikawa malam sani hoto,....jiki na rawa ya karbi hoton ya Kara dubawa,
Sarkin fada dake gefe yace "ka natsu kayiwa sarki bayani kadaina rawar jiki a gaban Mai martaba kake"
Shiru yayi na Dan wani lokaci yayinda parlon yayi tsit bakajin karar komi sai fanka,
Wata Rana,
"Na fito gabanin sallah asuba ta lungun dake jikin gidana dan zuwa masallaci sallah kawai cikin duhu na hangi mace tsaye ta raba hanya da tsohon ciki a jikinta farko na tsorata Dan tunani nayi ko gamo nayi Ina rike da carbina sai na Soma Kiran sunan Allah Ina kokarin karasawa inda take,
Tsayawa nayi daf da ita dikda tsananin tsoron da nake ciki be hanani yin jarumtar bude baki inyi Mata magana ba,
"Assalamu alaikum"...shine abinda na ce Mata sai Naga yadda ta waigo gareni a furgice tamkar wadda ta samu tabin hankali Tana neman hanyar gudu yayinda lokaci daya take fadin,
"Dan Allah kada ka kasheni ka taimakeni sun biyoni abinda ke cikina sukeso su cire su kasheshi ni Kuma Ina son abuna bawan Allah ka taimakeni Kila Allah ne ya jehoka cikin rayuwata Dan ka Taimakeni"....Tana maganar ne Tana waige waige ta furgice tamkar me neman wani Abu,
"Ina fatan mutum ce ke ba aljanah ba"....da sauri ta amsa da ,
"Ni mutum ce kamarka ka taimakeni bawan Allah ""Ki kwantar da hankalinki zan taimakeki Amma da sharadi Akan bazan taimakekiba daga baya ni kizo ki saka mun da sharrri daga taimako Dan duniyar yanzun abin tsoroce"sai kawai ta fashe mun da kuka harda durkusawa kasa Tana fadin "wallahi bazan saka maka da sharrri ba sai alheri bawan Allah ka rufamin asiri"
Jinjina Mata Kai nayi dikda zuciyata dake waswasi akanta Amma hakan be hanani samun karfin gwiwar Taimaka Mata ba nan nayi Mata umarni da ta tashi muje gidana inkaita Dan anata kiraye kirayen sallahr asuba ta Mike Babu musu ta bini muna tafe Tana sharar hawaye har gidana na kaita wajen matata shaawa,
"Shaawa!"
Da sauri matata ta fito daga daki Tana fadin "malam ko kayi mantuwa ne gashi anata Kiran sallahr asuba"...Bata karasa zamcenta ba ganina da mace yasa Tai shiru Tana Bina da kallon tuhuma da tambayea,
"Ki ajiyeta har indawo masallaci"shine abinda nace Mata na juya abuna inda ta Kama hannun wanan baiwar allahr suka Shiga ciki,
Bayan na dawo sallahr asuba ne na taddata Kan dadduma itama tayi sallahr suna zaune da matata Tana Bata labari Akan ita din matar sarki ce tsangwama da azaba ya korota daga masarautar su take bamu labarin irin azabar da Tasha na baaso ta haifi cikin jikinta,mun matukar tausaya Mata nida matata inda mukai Mata alkawarin riketa har ta haihu tunda muma ba karfi garemuba,ni lebura ne matata Kuma Tana kitso Tana wanki da guga dashi muke ci da kanmu tunda ba yara Allah ya bamu ba,
![](https://img.wattpad.com/cover/191531360-288-k885650.jpg)
YOU ARE READING
Anyi Walk'iya.......
Historical FictionBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...