13

1.4K 124 2
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA:SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

   _Allah ubangiji ya jikanki yayi Miki rahma_ *HAFSAT RADDA* 😭😭😭

          13

Tiryan tiryen duk abinda ya faru tsakanin yareema   habib da Fatima Zahra ke fita tar a projector da aka kunna a court,

    Mamakine dankare a fuskokin alumma , Nan da Nan kotu ta kaure da hayaniya,

    Barrister hauwa farincikinta a lokacin be misaltuwa, ita da Barrister Abdul ganin Allah ya bayyana gaskiya,..gogan Koh hamdala kawai yakeyi Yana kara godema Allah abisa wannan gaskiya da ta bayyana ,sosai yakejin farinciki mara misaltuwa a cikin zuciyarshi,

   Hajiya babba duk ta rikice take sai zare ido take yi,Amma can kasan zuciyarta ita kadai tasan abubuwan da take ayyanawa,

    Bayan bubbuga tebir, sannan aka bukaci kowa yayi shuru domin alkali ya gabatar da hukunci,

   Dattijo Mai cike da kamala da natsuwa wato alkali abubukar  assadiq ne ya  Gyara zaman gilas dinshi sannan ya dago Kai ya kalli alummar cikin kotun cike da natsuwa hade da kwarjininshi,yayinda kowa yayi tsit tamkar babu jamaa a ciki don sauraren mai alkali zai yanke,

      "Abisa shedu da suka gabata a gaban kotu , bayan dogon nazari kotu ta yanke hukunci kamar haka"

" Kotu tayi laakari da cewa Fatima Zahra Bata kashe yarima habib da ganganba inlla domin Kare kanta,
Abisa dalili da Haka kotu tayi granting release na Fatima Zahra akarkashin tsari na  section 59 of d penal code,don Haka kotu ta sallami fatyma Zahara (discharge and acquitted)

   "Sanan kotu tabawa jamian tsaro damar kamo maaikatan gidan marayu wato hajiya halima da haruna,
  Don kotu ta yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na shekara biyar,
   Duk wani Mai complain zai iya daukaka Kara zuwa kotu ta gaba..."

   *Courtttttttttttttttt*

    A hankalinki  Fatima Zahra ta runtse idanuwanta tanamai hamdala ga ubangijinta  a lokacin da Alkali ya wanketa,ta rasa a wani yanayi ta tsinci kanta a wanan lokacin,farin ciki ne koko bakin ciki?....idanuwanta ta bude karaf sukai ido hudu da yarima,murmushi ya sakar mata a fakaice hade da kanne mata ido daya take ya waske tamkar bashiba,

Barrister hauwa kasa boye farincikinta tayi saida ta mikama Barrister Abdul hannu sukayi wani musabaha cikin kauna irin ta Mata da miji,

   A hankali Barrister Abdul ya Rada Mata a kunne , "yade madam kuka ya karekoh" ......murmushi tayi sosai har saida hokoranta suka bayya cikin tsantsan farinciki,

Suna a hakane yarima Kabir yayi gyaran murya sannan ya mikama Barrister Abdul hannu sukayi musabaha,sanan ya juya ya shiga ayarin tawagar gidansu don tafiya gida,

  Takowa Fatima tayi a hankali har ta iso inda su barrister Abdul ke tsaye shida madam dinsa,Tana kokarin tsugunnawa barrister hauwa ta dagota ta Kai mata runguma ,wani kukan Dadi Fatima ta fashe dashi barrister hauwa na bubbuga bayanta alamar lallashi,

  Dago kan Fatima tayi tasa hannu ta share Mata hawaye tace"kuka ya Kare Fatima,ai kinyi kuka iyayinki yanzun lokacine da Zaki godewa Allah Akan bayyanar da gaskiya da yayi,lokaci da'ya kika tsinci kanki a balai na duhun masifa Wanda muka kasa bayyana Haske,sai Allah da kansa ya bayyana , *ANYI WALK'IYA* halin kowa ya fito saiki godewa Allah da niimar da yayi Miki"

   Jinjina Kai Fatima tayi hade da yin murmushi Mai kayatarwa sanan barrister hauwa ta sauke ajiyar zuciya tace"ya kamata muje dake gidana yanzun kiyi wanka ki huta zuwa wani lokaci kafin musan abunyi ko"

Anyi Walk'iya.......Where stories live. Discover now