19

1.5K 116 3
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *NA:SLIMZY✍🏼*

_wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

   
                  19

Lokacinda yarima ya Isa babban parlor inda dik Yan matan suke,ya tararda gwaggon sa rahi tsaye Tana magana da su deejahma Akan suyi haramar tafiya gida motocin daukarsu dunzo,

  Sallama yayi ganin kanwar mahaifiyarsa ya tsugunna har kasa ya gaisheta,a dakile ta amsa ta kauda Kai gefe sanan ya Mike tsaye ya kalli inda deejahmah ke ciccin magani yace"kije Mai martaba na kiranki"...

  Da sauri dukkansu suka juyo suna kallonsa cike da mamaki hada girar sama da kasa yayi ya juya zai wuce gwaggo rahi ta dakatar dashi da cewa"ai saika jirata kujera tare koh"

  Daga inda yake ya Bata amsa da "ya rigada ya sallameni,sauri nake inje indauki Fatima Dan yamma tayi"Yana fadin haka ya saki malalacin murmushi sanan ya fice Yana murmushin mugunta idan burunsu ya cika to shima burinsa ya cika Kuma komi Daren dadewa babban burinsa zai cika su cigaba da wasan donshi haka yakeso.....

   Kwafa gwaggo rahi tayi cike da takaici tace"maganinka abune Mai sauki a wajena kawai kayi kiskuren shigowa hannuna"

  Lokaci kankani wani Abu ya zo kirjin deejahma ya tokare Mata makoshi tunda taji furucin da yarima yayi na cewa zai dauko Fatima ta nemi farin cikin da takeciki ta rasa tamkar ta fasa ihu Dan bakin ciki,haka Nan ta Mike ta bukaci wata kuyanga da tayi Mata rakiya zuwa fadar sarki......

********
  Babu wani Bata lokaci yarima ya Isa gidan Ablah Koda ya shiga parlor wajen zamansu as usual kowa yayi jugum jugum kamar anyi mutuwa shiru kowa yayi sai TV dake aikinsa,sallamarsa ce ta dawo da kowa daga duniyar tunanin daya Lula,

  Cikin sanyin jiki Ablah tace"yanzun yarima daukar Fatima zakayi ka rabani da ita?ka dage Akan saita koma gidanku?gani kakeyi mu bazamu iya riketaba koh?kadai rabani da Fatima hankalinka ya kwanta"ta karashe maganar Tana hawaye hade da dafa Kan Fatima wadda ke famar shasshekar kuka,

  Murmushi yarima yayi sanan yace"haba Ablah Nima in Dana sunan,...babu Mai rabaki da Fatima sai Allah Dan a halin yanzun kece uwar Fatima ko Fatima tabar gidan Nan bazan rabakuba zan rinka kawota akai akai Tana duba ablarta kema Kuma nasan zakije ganinta Kinga ko baku rabuba ki kwantar da hankalinki har kwana zatazo yi"

  Gyada masa Kai kawai tayi Tana kallon Fatima Tana sharar  hawaye,

  Aysha dake gefe ta hada fuskarta ta zunguro baki gaba saboda takaici,yarima ya kalleta shi dariya ma ta bashi  saida yadanyi dariya sanan yace"haba Ashmah bakya kyau da kunci kisaki ranki kinji ban rabaki da kawarki Fatima ba Kuna Nan tare har kawota zanyi ta rinka Miki kwanaki,sanan makaranta ma nakeso in nema Mata Kila makarantarku zan kawota ko ai Kinga Kuna tare wannan bakin da aka turomin a maida"

  Harararsa aysha tayi ta Mike tabar parlorn dukansu suka bita da kallo,

  Kallon Ablah yarima yayi yace "magriba tayi banaso a Kira sallah Ina Nan Naga abokina bayanan Kuma naso mu hadu wallahi Amma bakomi zan dawo zamu tafi saboda tare da Mai martaba muke sallar magriba "

  "Badamuwa shima fitar ta gaggawace ta kamashi an kirashi daga gidansu shine ya tafi zan fada Masa,"....kallon Fatima tayi hade da mikewa tace"kindaiji maganganun Danayi Miki ko Fatima karki kuskura ki ketare shawarwarin Dana baki kinji Allah ya baku zaman lafiya"

  "Ameen"....

Mikewa Fatima tai ta rungume Ablah ta fashe da kuka a haka suke tafiya har waje,yayinda Aysha ta biyota da Dan akwatin kayanta Wanda Ablah ta sissiya Mata da Wanda itama ta Bata har wajen mota suka rakasu dakyar Fatima ta saki Ablah ta shiga mota Aysha tasa akwatinta a bayan mota yarima ya shiga yaja suka wuce,

Anyi Walk'iya.......Donde viven las historias. Descúbrelo ahora