17

1.6K 111 1
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....* 🌩

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *NA:SLIMZY✍🏼*

_wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

 

*HAPPY BIRTHDAY IN ADVANCE MOMMAH....*( *_Billy_* _*galadanci* )_ ~Shaku shaku don~ ~start from today~ 💃🏻😍😍

             17

  Kuka Mai sauti wanan karon Fatima ta fashe dashi a cikin motar ta riko hannunsa Tana kallonsa cikin ido,kauda kansa gefe yayi ya zura kafarsa daya waje yace "ummhmm Ina sauraronki akoke gwamnan kuka me kike nufi kika rikeni kina rusamun kuka kamar nayi Miki wani Abu"

   Kuka ta cigaba dayi batare da tace Masa uffan ba haushi ya Kara kulesa a zuciye yace"Kinga idan bakida abinda zakice ki sakarmun hannuna in shiga gida idan Kinga Zaki biyoni ki biyoni idan Kuma cikin mota Zaki kwana to Bismillah"

  Baki na rawa idanuwanta a rufe hawaye kawai ke gudu tace"Yaya yarima kayimun Rai ka rufamun asiri wallahi zamana a gidanku zai zamemun tamkar kabari,bazan tabajin dadin zaman gidan Nan ba bayan kowa ya Gama tsanata,ka rufamun asiri ka maidani gidansu Ablah ko ka maidani ainihin gidan mu"

  Wani haushine ya turnikesa ya kalleta fuska a daure yace"wato ni kike kallon tsabar idona kina cewa wai zaman gidanmu zai zame Miki tamkar kabari?wato baki shirya fuskantar dik wani kalubale akainaba ko?nine na shirya hakan ko?hmmmm to Fatima kisawa ranki bakida wajen Zama sai Nan gidan Dan wadanda kikeson Zama dasu babu abinda na hada Dasu sai soyayya da mutunci da sukemun Kuma koba hakaba wallahi bazan iya barinki kiyi Nisa Dani ba,idan Kuma kinga ke Zaki iya rayuwa babuni saki fadamun"....Yana fadin haka ya Juyo  ya kafeta da idanuwansa da suka canja kala lokaci daya....

  Girgiza Kai kawai takeyi Tana kuka zuciyarta na wani irin harbawa sauri da sauri lallai yarima so yakeyi a kasheta a cinye namanta Danye,ta kashe musu da' Kuma ya dakkota yace tazo cikinsu tayi rayuwa?sanan a matsayinta na tsintacciyar mage?yadai kawota kawai tayi bauta.....batada yadda zatayi ta bijire Masa don ita kanta bazata iya rayuwa a wani wajeba Babu shi....

  Kukan kawai takeyi Babu kakkautawa hannu yasa ya cire makullim mota yace "share hawayenki ki biyoni"....fitowarsa yayi ya rufe bangarensa,

  Hakanan ta sako kafarta ta fito waje tasa hannu ta share hawayenta,shiko kulle motar yayi ya Kara hada ransa tamkar wani Zaki tamkar tunda yake be taba dariya ba yayi gaba,dakyar take cira kafa Tana binsa a baya.

  Babban gidane gidan sarauta dik inda suka wuce kallonsu akeyi daga maaikata har bayi da kuyangi kowa kallonsu yakeyi yadda take binsa tamkar tsomammiyar kaza ga uban hijabi har kasa.....

  Kuskus kawai ke tashi wajen bayi dik inda suka gifta har lekensu ake yayinda zuciyarta ta cigaba dayi Mata lugude ji takeyi tamkar ta hadiyi zuciya.....

   A haka har suka iso kofar da zata sadasu da babban sashi na gidan inda bayi ke tsattsaye masu tsaron kofar sashin take suka zube kasa suna kawo gaisuwa hannu kawai ya daga musu ya wuce Fatima na biye dashi.....

  Shi kansa uban gayyar cikin faduwar gaba yake saidai a fuskarsa ya tsare gida da jarumtaka irin tasa tun kafin su saka kafa a parlorn ya jiyo muryar gwaggo rahi....dammm gabansa ya yanke ya fadi haka kawai yaji zuciyarsa na bugawa sauri da sauri haka ya jajurce ya daga labulen dake zagaye a kofar yayi sallama"Assalamu alaikum"...fuskarsa a dake,

  Labewa Fatima tayi a bayansa taki shigowa dukkansu suka zuba Masa ido ganin yanayin yadda ya daura fuska Yana waige waige kamar Mai neman wani Abu a dake yace"Fatima shigo Mana ya kika tsaya a baya"

Anyi Walk'iya.......Donde viven las historias. Descúbrelo ahora