🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
44Kallon hoton yarima yakeyi Babu ko kifta idanuwa....hannuwansa ne kawai yake rawa yayinda zuciyarsa ke bugawa tamkar zata fasa kirjinsa ta fito,
Ahmad ne ya Mike Yana duban yarima yadda dik tashin hankali ya bayyana a fuskarsa yace "ranka ya Dade lafiya kuwa?meke faruwa ne"....still yarima Yana tsaye idonsa Akan hoton bema San Ahmad Yana magana ba Saida ya gaji ya bugi kafadarsa "malam da Kai nake magana fa meye ya faru ne?ko kasan wani Abu dangane da wanan hoton ne?"
Murmushi kawai yarima ya sauke yayinda ya cije lebensa kwalla ce cike a Ramin idanuwansa sai kawai ya kada kansa dakyar ya iya juya kansa ya kalli Fatima wadda ke durkushe da daya hoton Tana kallo Tana kuka,
"Tashi muje gida"
Wanan tsohon ne ya sauke ajiyar zuciya "iko sai Allah wanan al'amarin akwai boyayyen lamari cikinsa Allah ya warware muku yara"
Ahmad ne yayi karfin halin cewa "ameen"... yayi gaba yarima na biye dashi hannunsa rike da hoton,
Fatima ce karshen fitowa daga gidan Tana kuka Mai ban tausayi tanayi Tana waigen kofar gidan,....dakyar ta shiga mota suka tafi,
Gidan tsohon maaikacin gidan marayu suka fara zuwa suka saukesa,
Yarima da kansa ya fito yayi Masa godiya sosai ya Ciro kudi masu yawa a aljihunsa ya Mika Masa sukai sallama sanan ya juya ya shiga gidan gaba ya zauna,
Ta gefen ido Ahmad ya kallesa "Ina muka nufa?"
"Gidana zamuje"
Jin amsar da yarima ya bawa ahmad yasa Fatima saurin dago kanta Tana duban bangaren da yarima yake,....sai ta sunkuyar da kanta zuciyarta nayi Mata tsananin Kuna da zugi...ga tsantsar takaicin yarima dake kwance a zuciyar Fatima...dik yadda taso da suje gidan sarki taga ummunta Amma yarima ya Hana sai kawai ta kauda kanta ta cigaba da zubar hawaye,
A kofar gida ya saukesu ya juya abinsa suko a tare suka shiga gidan,
Deejahmah na tsaye tana Shirin Hawa sama suka shigo dik tabisu da kallo ganin yanayin da suka shigo....
Sama Fatima ta Haye a guje Tana hada matakala
Yarima dake Shirin bin bayanta deejahmah ta dakatar dashi "barka da dawowa"
"Barka dai"....ya Haye sama abinsa...tabishi da kallo hade da tabe baki,
******
Kan gadonta ta fada ta fashe da kuka harda majinu Tana juyi a haka ya sameta a dakin,Bece Mata komiba ya jingina kansa da jikin bangon dakin shima ya runtse idanuwansa saiga wasu hawaye masu zafi na sauka a fuskarsa,..
Zuro kafafuwanta tayi kasa ta Tako gabansa ta tsaya "ka Tai makeni Kabir ka kaini inda iyayena suke Domin yanayinka gabaki daya ya nuna kanada masaniya game da inda iyayena suke...ka taimaki rayuwata ka kaini inda iyayena suke a daina kirana da shegiya"ta karashe maganar idonta kyar akansa,
Hannuwansa yasa ya tallabota lokaci daya ya saki lallausan murmushi dikda hawayen da suka wanke Masa fuska "tabbas Fatima nasan inda iyayenki suke ko Ince inada masaniya da su saboda kedin jinina ce"...
"Ta Yaya na Zama jininka?ko ka manta a inda ka sameni ne?ko ka mance a inda aka tsinceni ne sanan kaga a irin gidan da uwata ta haifeni"..
Hannu yasa ya share Mata hawayen idanuwanta "ke jinin masarautar barayar Zaki ce fatima"
YOU ARE READING
Anyi Walk'iya.......
Historical FictionBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...