42

1.9K 142 19
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

  *NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

                 42

Tsayawar motocinsu yayi daidai da fitowar bilkisu da niyyar zuwa bayan gida hannunta dauke da mopper ganin motoci sababbi yasata tsayawa kallon motocin cike da kosawa da bukatar ganin kosu waye....

  Murmushi Fatima ta sauke ganin Yar uwar Tata tsaye tana kallon motocin tamkar Yar kauye ta juyo ta kalli yarima shima murmushin yakeyi ya daga Mata gira sama "Ali yaga Ali ko?"

Jinjina Masa Kai tayi tana mai maida dubanta ga bilkisu wadda har yanzun tana tsaye motocin take kallo sanan ta juyoga yarima ta ruko hannuwansa

  "Lokaci nake jira a yanta Yar uwata daga kangin bauta,"

  "Kefa kin fiye rigima tayaya hakan zai kasance?bayan kinsan baiwar hajiya babba ce"

  "Bedameniba inhar baa yantata ba zansa a daukemun ita Nan gaba kadan"

  Lakuce Mata hanci yayi "rigimarki yawace da ita yanzun mubar wanan maganar"

  Ta Bata fuska Tana kallonsa "to zan roki Mai martaba da ya nemamin alfarmar a bani ita a matsayin baiwata idan yaso a dawowa da hajiya bayi guda biyu Nan"

Bata Rai yayi "nibanason rigima bintu Kinga kibar wannan maganar ba yanzun ba"

  "Shikenan tunda haka ka zaba ganin Yar uwata a kangin bauta ni Kuma Ina ya'ntacciya tunda ka rigada ka mallakeni Dole kace hakan"..ta bude mota ta fito Bata jira cewarsa ba bayin dake zagaye da motocinsu suka rufa Mata baya,

  Zubewa bilkisu tayi fuskarta dauke da faraa "Allah ya taimaki sarauniya Fatima....barka da zuwa'

  Dagota Fatima tayi  cikin kasa da murya tace "harabada Yar uwata bazata taba durkusaminba,kiris nake jira in daukeki daga kangin bauta"Tana fadin haka tai wucewarta sauran kuyangin suka Mara Mata baya,

  Shiko yarima dage kafadunsa yayi yai hanyar fadar sarki tunda yaga cikin gida tayi.....

  
********
Sashen mama karama ta nufa Tana tafe Tana takama dik inda ta gifta maaikatan gidan na zubewa suna kawo gaisuwa

  Bakinta dauke da sallama ta shiga parlorn hajiya karama a nan ta tararda ummu zaune da afnan suna zaune sun idar da sallahr laasar

"Lale marhabun da zuwan diyata daya tamkar da dubu yanzun nake cewa kewarki ta isheni mijinku yaki kawoku ki gaida Mai martaba yanata fada"

  Kunyace ta lullube Fatima ta zube a kasa a gaban ummu hade da kamo hannayenta "Ina kewarki uwa ta gari na durkusa a gabanki Ina me neman afuwarki na rashin ganina da bakiyiba"

  Jinjina Kai ummu takeyi cike da farin ciki "ai idan kaji danka shiru a gidan miji to lafiyar kenan karki damu a dik inda kike inayi Miki addua"

  Gyada Kai Fatima tayi sanan ta juya gaban hajiya karama wadda tunda Fatima ta shigo take binta da kallon shaawa fuskarta dauke da murmushi Tana gyada Kai.....kwana bakwai kacal yarinya ta canja ta Zama tamkar balarabiya ga wani kyau da tayi sanan babban abinda ya karawa fuskarta kyau shine ladanin sallah dake manne a saman goshinta Dan karami yayi bakin Kirin dashi,

"Allah yaja da ranki ya kareki ya Kara daukaka barka da warhaka ranki ya dade"

  Daga Mata hannu hajiya karama tayi "barka dai Fatima ya gida?ya abokiyar zaman naki?"

"Lafiya Lau tace a gaisheku itama zatazo ko zamuzo tare "

  "Masha Allahu,kinje kin gaida hajiya babba ko?"...gaban Fatima ne ya fadi Dan shaff ta mance da wata hajiya babba Domin Bata ita takeyi ba

Anyi Walk'iya.......Where stories live. Discover now