49

1.5K 106 2
                                    

🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡

  *NA: SLIMZY✍🏼*

_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*

                    49

Da sauri ya karasa inda Fatima ke kwance a bargo ya ja bargon sai kawai ta runtse idanuwanta zuciyarta na cigaba da bugawa,

Tallabota yayi yakai idonsa fuskarta yaga yadda hawaye ke kwance a fuskarta sai ta bashi tausayi ga yadda jikinta yayi xafi Rau alamar zazxabi,

A raunane ya dubi Ahmad "Anya doctor zazzabin Nan zai barta kuwa?kaji yadda jikinta yake da tsananin zafi?"

"Wai meyasa kake haka ne friend bayan kasan fa dik inda akace ciki Yana karami musamman nata Dole ne sai anyi hakuri da kanana kananan ciwon da zatayi tayi saidai kawai a Bata drugs Wanda zata Dan samu saukin jikinta Amma bawai ya Bari ba sai cikinta yayi kwari"

  Beso jin wanan amsar daga bakin Ahmad ba Amma sanin shi din doctor ne yasashi Dole amincewa da hakan dikda yadda yakejin tausayin nata,

  Fatima kuwa a zahiri wani haushin yarima takeji tamkar ta shake shi yazo Yana wani kuri yanajin tausayinta bayan Yana can wajen matarsa ya biya bukatarsa ita tunda yayi Mata ciki ai shikenan...

Bude idanuwanta tayi ta saukesu akansa ,"yadai Fatima ya jikin"

Bata amsa masaba sai kokarin kwacewa da takeyi daga rukon da yayi mata,....mikewa Ahmad yayi ya dubi bilkisu Wadda ke zaune a gefe a takure yace "zo muje ki dakkowa Fatima sako a mota,..."

Ba musu ta Mike ta fice,...juyawa yayi ga yarima "to malamin soyayya malamin Mata biyu Allah ya sauwake ni nayi Nan"...ya fice abinsa,

  Yana fita Fatima ta kwace jikinta ta jingina daga jikin kujera watsa Mai harara,

  "Baby Wai lafiya kike wanan Harare hararen haka?meya faru?ko kina bukatar wani Abu ne?"

  "Ko Ina bukata ya zanyi tunda mijina bani kadai ke dashi ba ya tafi saukewa wata bukatarta...Koda yake Kila kaima kana bukatar ne"ta karashe maganar hade da Shan murrrr

  Shiko mamaki da tsoron Allah ne suka Kara lullubesa yana binta da kallon takaici,lallai ma wanan yarinyar wato Yana can Yana nema Mata farin ciki ita Tana Nan Tana zarginsa,ya rasa dalilin da yasa Fatima ke irin wanan mugun kishin hakax

  Haushi ne ya Kara kamasa ya Mike daga tsugunnon da yayi ya fice abinsa,sai kawai ta sa kuka a zaune wiwi tamkar karamar yarinya....

*********

"Wanan cikin bazata taba haihuwarsa a gidan nan ba inhar Ina numfashi deejahmah kidaina wanan kukan da kikeyi Domin wanan karon na shiryawa lamarin zakisha mamaki"

  Kukan deejahmah ne ya tsananta Babu abinda take da buri a duniya sama ta ganta da jikan Dan sarki a hannunta,ya zamana itace ta Soma bawa sarki jikan fari.....batada hope Akan abinda hajiya babba ke Fadi Domin zuwa yanzun ta Gama sarewa da lamarin gabaki daya musamman data fahimci dik abinda suka sa gaba basa nasara akai sai wani Abu ya gifta Wanda zaisa basuyi nasara ba,....hawaye be daina gudu a idanuwanta ba,....Anya wanan tafiyar da hajiya babba ke tunani zata yuwu na su Bata cikin Fatima?shin idan Sukai kokarin hakan akwai nasara kuwa?menene basuyiba Akan shi aurem gabaki daya,

  Zuwa yanzun zuciyarta ta karaya batada wani hope Wanda ya rage Wanda ya wuce ta nemi zuciyar mijinta ta yada makaman yaki ta zauna lafiya,dama ita batada burin cutar da kowa a rayuwarta iyayenta sune suke sata a hanya....jikinta yayi sanyi dakyar ta motsa ta goge idanuwanta ta maida dubanta ga mahaifiyarta tace a raunane "Babu ruwana da zancen cikin Fatima,babban burina be wuce Nima in ganni dauke da juna biyu ba,....idan har zanyi wani Abu be wuce inyi abinda zansamu ciki ba"ta karashe maganar da share hawaye,

Anyi Walk'iya.......Where stories live. Discover now