*🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*
*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*
*NA SLIMZY*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*
03
Tafe yake cikin mota Yana driving Amma Sam hankalinsa baya wajen gangar jikinsa ce kawai take tukin motar tunaninsa ya Gama gushewa da lissafinsa ga wanan babban ala'amari da ya faru....mafita kawai yake nema minti minti Yana tsaki zuciyarsa na tsananin Kuna da zafi a haka har ya Isa tangamemen gate din gidan marayun,horn yayi da karfi Mai gadi ya leko ta Dan kofar gate din sanan ya juya da sauri Dan bude Masa gate,wangale gate din yayi gaba daya ya koma gefe Yana daga Masa hannu tare da Mika gaisuwa,hannu kawai yarima ya daga Masa alamar amsawa inda sabo ya Saba da yadda yarima khabir ke amsa Masa gaisuwa cike da kasaita da izza irin na jinin sarauta.....
Can gefen wata bishiya yayi parking motarsa inda ya Saba ajiyewa idan ya shigo Kuma wajen ne ya kasance wajen zamansu idan yazo,ya Dade a cikin motar Yana waige waige wajen shiru Sai kukan tsuntsaye ko alamar giftawar Yan Mata da ya Saba gani be gani ba ya Dade a wajen a cikin motar Yana kalle kalle ko Allah zai hadashi da daya daga cikin aminanta na gidan Amma bega kowa ba ya kwashi kimanin minti arbain shiru babu wani labari haka yayiwa motarsa key ya juya jiki a sanyaye ya nufi hanyar gida....
******
Hajiya babba CE zaune da hadimanta a babban parlornta inda take ganawa da mutane ake karbar gaisuwa Tana zaune ta Mike kafarta daya daga cikin bayinta Tana Dan matsa Mata kafa idanuwanta a runtse zuciyarta na tsananin tafasa ta jiyo sallamarsa ,a hankali ta bude idanuwanta ta sauke akansa take taji tausayinsa ya kamata, yadda ya rame lokaci daya ya fita hayya cinsa saboda mutuwar Dan uwansa,a hankali ta bude baki ta amsa da "walaikumussalam"Tsugunnawa yayi har kasa ya dukar da kansa cikin sanyin murya yace "barka da war haka mama?"
"Barkadai kabir" Kara dukar da kansa yayi cikin girmamawa yace "ya Karin hakurin mu?"
"Hakuri alahamdulillahi"
"Allah ya jikansa Allah ya gafarta Masa"
"Ameen"
Jim kadan ya Mike har ya juya ta tsaidashi "khabir"ta Kira sunansa,tsayawa yayi Jim kadan sanan ya juyo a hankali ya tsugunna batare da yace uffan ba,Bata damu da rashin amsawarsa ba ta cigaba da magana cike da kasaita da gadara wanan Karan magana takeyi sama sama "khabir inaso Kai zakaja ragamar shariar Dan uwanka Habib,inaso kasa kakin ka na lawyer ka hau kan aikinka banaso a ragawa dik Wanda yayi wannan aika aikar,ko wacece ta kashe maka Dan uwa ka tabbatar da kabiwa Dan uwanka hakkinsa nasan Kai gwanine wajen shariah Kuma babu Wanda ya Dace da wanan shariar Sai Kai,anjima nakeso kaje can station din ka bincika Mana yadda ake gudanar da bincike Akan yarinyar akara Bata tsaro saboda kada ta tsere,na lashi takobin dik Wanda ya kashemun da' Shima Sai an kasheshi ko Dan gidan uban waye"
Wani irin firgici da tsorone ya ziyarci zuciyarsa a Karo na farko a rayuwa tunda yake babu abinda ya taba tada Masa da hankali ya furgita kamar wannan al'amarin daya kunno Kai Nan Nan zufa ta shiga karyo Masa ta ko Ina be Isa ya tsallake umarnin mama babba ba Amma ta Yaya zai tsaya a shariah a kashe Masa Fatima Zahra?kirjinsa ne ya cigaba da bugu da sauri Amma Sai ya dake yace"zaayi bincike sosai zaayi yadda ya kamata insha allahu"
"Allah yayi maka albarka tashi kaje dama maganar kenan"
Mikewa yayi jikinsa a sanyaye dakyar yake taka kasa ya haka yake tafiya kansa Yana tsananin Sara Masa tamkar zai rabe biyu haka ya lallaba ya shige bangarensa.....
*******
Tunda aka rufeta a cikin wanan dakin da kullum Sai anyi Mata tambayoyi Wanda babu Wanda ta taba amsawa ko abinci baa Bata,Yan hajinta babu abinda sukeyi Sai kukan yunwa dikda babu abinda zata iyasawa a bakinta Koda ruwane, makoshinta ya bushe, idanuwanta sun kasa zubda hawaye, kukan zuci kawai takeyi,babu wani Abu da take tsammani Wanda ya wuce kisan Kai kamar yadda tayi Dan batada sauran Amfani a wanan duniyar me cike da tashin hankali kala kala batada wani sauran Amfani a matsayinta na marainiya babu uwa babu uba babu Dan uwa babu gata Sai Allah.....shin menene makomarta Wanda ya wuce a kasheta ta huta?.....ta rigada ta cire Rai da rayuwa tasanyawa zuciyarta dik Wanda yazo ya Kara tambayarta zata sanar dashi Akan itace tayi kisan gara a kasheta kawai....

YOU ARE READING
Anyi Walk'iya.......
Historical FictionBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...