10

1.8K 108 2
                                    

*🌩ANYI WALK'IYA.....🌩*

*💡 HASKE WRITERS ASSOCIATION💡*

*NA SLIMZY*

_Wattpad@slimzy33_

*Sadaukarwa ga k'awata Faty D'an maliki*

              10

Kallonmu yakeyi Yana murmushi,ganin yadda muka runtuma a guje yasa ya tsaya daga inda yake takowa zuwa garemu,

  Mukuwa rarrabuwa mukayi duka mu ukun kowa ya nemi wajen buya,Sai haki nakeyi a jikin wani karfe Ina maida numfarfashi Ina Dan leko da kaina ko Zan hangoshi Amma ban ganshiba,ajiyar zuwa na sauke na dafe kirjina da yake bugawa fatt fatt saboda gudun da mukayi.....

Taro sosai ake gudanarwa  a wanan ranan domin harda kayan sawa aka kawo Mana tallafi gidan marayu da buhun Hunan abinci,yayinda Yan jarida keta daukar hoto.....shiru Banga Yan uwana ba na fito Ina takawa a hankali tamkar mejin tsoron wani Abu inayi Ina waige waige Sai ji nayi ance cikin wata murya Mai dadin sauraro"har yanzun tsoron be sakeki ba kenan?"cakkk na tsaya wani irin tsoro da furgici suka shigeni lokaci daya nakasa ko kwakkwaran motsi,

  Takowa ya karasayi ya tsaya a gabana shine dai na dazun Wanda muka gani Yana waya yanzun hakan ma wayarce a kunnensa yakeyi, karkarwa kawai jikina yakeyi, domin har ga Allah na firgita sosai da wanan bawan Allah Sai ji nayi yace "yanzun haka Yan uwanku ake rabawa kayan sawa ke kuwa kina Nan kina buya,to boyon me kikeyi?"

Bakina na rawa nace "Dan Allah kada ka saceni kaji?kayi hakuri wallahi bazan sake ba"

Cikin mamaki yake kallona yace "Babu abinda kikamun Yan mata,sanan Ni Kuma bame satar mutane bane Koda Kika ganni a Nan ba a cikin mutaneba akwai dalili, dalilin kuwa shine bana son hayaniya shiyasa nadawo gefe inata waya abuna"

  Jin jina Kai kawai nayi na juya nafara tafiya Ina hardewa har na danyi nesa dashi naji yace "Amma ya sunanki?"

Sarai nasan Dani yake na cigaba da tafiya,Sai ya Dan daga murya yace "idan har Baki fadamunba to Zan saceki in gudu dake"

  Ai da sauri na juyo nace cikin daga murya "Fatima"Ina fada Masa na Ruga a guje ko Ganin gabana banayi saboda tsoron kada ya saceni,

  Daidai tawagar Mai girma sanata sun taho domin zagayen gidan marayu lokacin na rugu a guje Zan gifta ta gabansu aikuwa hajiya ta kwalamun Kira "ke Fatima meye haka saikace wata akuya kin taho a guje kamar ba mace ba"

  Da sauri na zube a wajen Ina Bata hakuri "hajiya Dan Allah kiyi hakuri wallahi tsoro naji shiyasa"....da'go idanuwana nayi don kallon yanayin hajiya kawai Sai muka hada Ido da wani kyakkyawan mutum fari Tass tamkar na dazun saidai wanan Shi yanada Dan jiki Kuma be Kai na dazun tsawo ba,

  Da sauri na sunkuyar da kaina na Mike na wuce tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki,su kuwa wucewa sukayi domin zagaye.....


    Cikin Yan uwana yara na shiga dik Wanda na kalli fuskarsa a wanan ranan cike yake da farin ciki saboda murnar an kawo Mana tallafin kayan sawa da kayan abinci, ...neman su bilkisu na shigayi cikin mutane Amma ban gansuba,Nima kawai Sai na juya na nufi dakin kwanciyar mu ko can sukaje,

  Haka kuwa akayi,Ina shiga suka tuntsiremun da dariya dukansu dariya suke Babu kakkautawa,cikin dariyar bilkisu ke nunani da yatsa "faty Wai me yace Miki Dana hangoku ya kamaki?"ta Kara tuntsirewa da dariya,haushi ne ya kamani batare da nace komiba na karaso na nemi waje na zauna hade da daure fuskata,domin idan akwai abinda na tsana be wuce a kalleni a rinka yimun dariya ba ,su kuwa Yan uwana dabiarsu kenan musamman bilkisu,

**********
Bayan kwana biyu,

   Muna zazzane a ta bayan kitchen nida su Maryam da Kuma tsurarun yara a wajen Sai mukaji hajiya halima ta rangad'a guda a cikin kitchen,dik Sai muka juya da sauri muna kallon windown kitchen din Wanda hayaki ne kawai ke fitowa,

Anyi Walk'iya.......Where stories live. Discover now