🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
29A gaggauce ya shigo fadar da sallamarsa a bakinsa ya karaso deejahmah dake gefe gabaki daya ta maida hankalinta akansa Dan ba karamin kyau yayi Mata ba da kwarjini,ta manta shaf a inda take har ya zauna Tana binsa da wanan mayen kallon Wanda har uwarta dake gefenta Saida ta Dan zungureta cikin rada tace Mata "ki natsu Mana karki bada kanki".....a hankali ta sunkuyar da kanta hade da wayancewa ta fara Wasa da yatsun hannunta,yayinda zuciyarta ke Kara azalzalarsa da ta dago kanta ta kalleshi ko Allah zaisa su hada ido Amma tabbas idan tayi hakan to kowa zai ga maitarta a Fili......ta rasa dalilin dayasa matukar kabir Yana waje to Tana neman natsuwarta ta rasa ta kasa gasgata abinda zuciyarta ke fada Mata na ta fada tarkon sonsa,....idan kuwa haka ne zuciyarta batayi Mata halarciba Domin Koda Tana sonsa bazata janye kudurinta na daukarwa habeeb fansa akansa ba.....ajiyar zuciya ta sauke sassanya wadda tayita ne a dalilin maganar Mai martaba data dawo da ita daga duniyar tunanin data afka na wucin gadi....
Gyaran murya Mai martaba yayi yau fuskarsa Babu yabo babu fallasa a bisa alamu yau din Nan sarki Yana Jin sarautar,kasaitar Yan maza ta motsa shi kansa dakyar ya motsa labbansa yayinda ya maida dubansa ga waziri dake gefe yace "waziri ka bude Mana taro da addua"....Nan take babu Bata lokaci waziri ya cika umarnin Mai martaba ta hanyar yin addua kamar yadda ya umarcesa hade da shafawa da salatin annabi (s.a.w).....
Shiru fada tayi kowa da sake saken da yakeyi a zuciyarsa gyaran murya Mai martaba yayi sanan yace "nataraku a Nan ne a bisa dalilai biyu zuwa uku Amma kafin in zartar da hukuncin sai na tabbatar da kowa Wanda keda hakki a taron Nan Yana wajen Nan"
Shiru ne ya biyo baya Babu Wanda yace komi sanan Mai martaba ya cigaba da magana "kabiru Ashe abinda ya faru kenan?"
Rasss gaban yarima ya yanke ya fadi Domin be fahimci inda maganar Mai martaba ta dosaba,Amma sai ya Dan gyara Zama cike da biyayya da ladabi yace "Allah ya baka yawan Rai ban fahimci maanar maganarka ba"
Jinjina Kai Mai martaba yayi sanan yace"wani mugun labari ne yasameni dazun jakadiyyata ke sanar mun da cewa an nemi yar Amana an rasa ta gudu,maana Yar daka daukota ka kawota gidan Nan a matsayin Yar riko Wanda taron Nan musababbinsa saboda Kai da ita ne da Kuma Khadija"
Wata xuface ta ke karyowa yarima Wanda ya Gama shiga rudani a maganar Mai martaba ta farko ,kansa a kasa ya Kara gurfanawa "Allah ya baka yawan Rai Babu inda Fatima taje Tana cikin gidan Nan yanzun haka"....
Da sauri hajiya babba ta kallesa tayi maxa tace"maganar banza kakeyi bayan Babu inda baa dubana baaga yarinyar Nan ba har cikin tsohuwar rijiya an leka babu ita,karya kakeyi saidai idan nemanta zaka fitayi ka fakeda Tana Nan to idan gaskiya ne ai taron harda ita akace zaayi Tana Ina?"
Shiru yarima yayi batare da yace komiba,kansa na sunkuye a kasa ya tsinkayo muryar Mai martaba na fadin ,
"Dakata hajiya dik maganar Bata fada ko hayaniya bace,Nasha fada Miki da banaso idan kinamun magana kinamun hayaniya"
Jiki a sanyaye hajiya babba ta sunkuyar da Kai itama sanan tace "Allah ya huci xuciyar Mai martaba"....
Juyawa yayi ga yarima ya cigaba da magana "kabiru kace Tana gidan Nan,gashi ance an duba Babu ita meye gaskiyar lamari"
"Ranka ya dade kunama ce ta harbeta jiya daddare yau da asuba na fito zanje masallaci na gamu da ita zatayi alwala kafarta a daure shine na dauketa na kaita gidan waziri wajen malam ya'u ya yi Mata addua dagacan na kaita asibiti yanzun haka Tana waje nace tabari a Bata umarnin shigowa"
KAMU SEDANG MEMBACA
Anyi Walk'iya.......
Fiksi SejarahBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...