🌩 *ANYI WALK'IYA.....🌩*
*HASKE WRITERS ASSOCIATION* 💡
*NA: SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_
*Sadaukarwa ga k'awata faty D'an maliki*
34Yan matan amarya uku ne tare da amarya a wani kebabben daki inda nan ne ake tsarawa amarya kwalliya wadda ta fito da ainihin kyawunta Domin ita kanta deejahmah ba baya ba wajen kyau da diri wadda fatarta ta kasance ita ba faraba ita ba baka ba fatarta tamkar mutanen Etopia ga manyan idanu da take dasu farare tas da yalwar Zara zaran gashin idanuwa sanan ita ba doguwa bace ba gajereba Tana cikin matsakaitan Mata Mai Dan jiki da shape dai dai ita....doguwar Riga ce jikinta kalar golden da kyalli kyalli na net da stones Wanda akai kwalliyar rigar dashi head dinta ma golden colour tayi matukar kyau na kece raini fuskar Nan Tata wadda ta kasance Koda yaushe a daure take yauma hkn ya kasance Amma hakan be tsantsar kyawunta bayyana ba...
Mayafi aka kawo Mai tsadan gaske aka lulluba Mata akanta wayarta ce ta fara Haske da sauri ta cire pin din wayar Tex ne ya shigo kamar haka ... _HELLO IN D NEXT 5 MINUTE IDAN BAKI FITOBA WALLAHI BAZANJE WAJEN TARON BA WAYE YARONKI DA ZAKI SHANYA...MTSWW_.
wani mugun takaicine ya rufeta wato yafi karfin ya kirata a waya ma saidai yayi Mata Tex,kwafa tayi hade da girgiza Kai cike da takaici a cikin ranta tace "zaka shigo hannu Dan rainin hankali"...a zahiri kuwa dago idanuwa tayi cikin mayafinta tana kallon su teemah dollar suna kashe selfi,haushi ne ya lullubeta dakyar ta bude baki cike da takaici tace "Sunita kubar daukar hoton Nan haka mu ake jira a wajen Nan yanzun haka prince ya turomin Tex suna waje"
Dariya Sunita ta kamayi "soyayya wanan wani irin ango ne da baya Kira sai Tex"
Teemah dollar ta karbe zancen "kedai Bari zee baby wanan amgon da abokanansa Yan Jin Kai ne domin Basu nemanmu sai amaryarsu zamu Rama wajen siyan baki"suka sheke da dariya suka tafa
A k'ule deejahma tace"Kun fiye son magana muje da Allah"
Saida suka kakkashe hoto da deejahmah sanan suka fito Tana tafe tamkar bazata taka kasaba ga wani uban takalmi me shegen tsini da kyau Wanda tasa Tana takawa a hankali mutum biyu suka tsaya gefe da gefenta daya na biye dasu a baya...
A kofar harabar gidan sukaga motoci reras na abokanan ango cike da xumudi Sunita ta bude bakar mota zata shige Ahmad ya juyo da sauri ya dakatar da ita "motar amarya da ango ce wanan".turus tayi ta juya Tana kallon yarima Wanda ya hada girar sama da ta kasa tamkar be taba dariya ba haka ta juya ta wuce,
Deejahmah na sako kafa cikin motar kamshi ya baibaye motar tamkar anyi barin turare,..ta gyara zamanta a baya kusa da yarima ta zauna Ahmad ya rufo kofar ya zagayo gefen driver ya zauna ta glass din mota yake kallonsu Yana dariya kasa kasa cike da zolaya yace "ranki ya dade,sarauniya deejamah amaryar sarki Mai jiran gado Allah ya Sanya alheri"
Murmushi cike da kasaita Sanan ta amsa cikin sassanyar murya "nagode"...
Fuska a daure yarima yace "Ahmad ka manta uwar gida ce?nan gaba kadan amaryarta zata shigo Wanda zataci girma ta barwa amarya Zama sarauniya tunda ita babba ce"...ya waigo ya kashe Mata ido...
Takaicine ya lullubeta suna tafe a hankali a mota kusan second talatin tamkar bazatace komiba tsulum yaji tace"sai na so na bada kofa wata zata shigo gidan mijina,Domin mijina nawa ne ni kadai Kuma baayin sarauniyoyi saidai ace sarauniya,mulki da sarauta na ya'yan asaline ba tsintattu ba"
Ta wurga Masa harara daidai lokacinda suka karaso wajen mota ta tsaya tayi parking ....
*********
Da sauri sauri Fatima tayi wanka ta fito bayan sunkammala ayyukansu dikda ranta da yake abace Amma bazai hanata zuwa wajenba kodan farin cikin yarimanta,

YOU ARE READING
Anyi Walk'iya.......
Historical FictionBanida wata alak'a da Zina da zan aikata Shi Maryama,sabida na taso na Kuma girma acikin gidan marayu bashi ze bani damar wulak'anta ni'imar da Allah yamun ba ya tasheni acikin musulunci, menene aibuna Dan kawai nataso banida gata se'a hannun gwamn...