P... 1

3.1K 216 5
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

           P... 1

      Kwance nake a saman wani tamurarren gado, irin na dori d'in nan, Na buga wani uban botso ina ta famar sharara baccina cikin isa da takama tare da kwanciyar hankali da walwala.

Wata mugunyar d'ibga ce da na ji an yi karfin halin kai man a saman duwawu ta yi gaggawar ankarar da ni, firgigit na falka tare da gyara kwanciya ta cike da kunar da zuciyata ke yi kamar ta fashe domin nasan wannan ba shairin kowa bane illa na Kaka sarkin takura mai rai.

             A fadace na ji tana cewa, "Billahillazi kika sake kika yi man fitsarin kwance yau wlhy ko na lahira sai ya fiki jin dadi".

             Cikin mugun jin haushin wannan kalmar ta fitsari da na ga kullum da'ita Kaka  ke bugun gaba idan masifarta ta tashi gareni, na turmike fuska nasha omo tare da kara gyara kwanciyata domin ci gaba da yin bacci na.

            Nan take na ji alamun sautin fitowar maganar gwaggo talatuwa, mai bakin kara, shine lakanin da nayi mata a cikin zuciya ta, tana cewa "Ai wlhy Inna na ma ga kokarin ki da har yanzu kin kasa canza mata wajen kwanci, yarinya da shegen fitsarin tsiya haka ajima-ajima sai ka ce Shanuwa ko kuma Tunkiya  uwar tambele."

            Ta karkare maganar   ta tana mai mirginawa a saman wata lafatattar katifarta mai kama da lomar tuwo, cikin raina  na ce, "Oho dai dik bakin cikin ki dai bai wuce saman gadon da kika ga ina kwanciya ba, kuma bazan daina ba." Na karasa maganar ina mai murguda baki na gefe kamar suna gani dan sosai maganar  ta bata man rai domin ni yarinya ce mai shegen saurin fushi kamar kaska.

             Sai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun  bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai.

              Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin "Ina za ki tantiriya a cikin wannan daren?".  a daidai wannan lokacin gwaggo talatuwa, mai bakin kara, kamar daman jiraye ta ke da taji Kaka ta yi maganar, ta mike zaune tare da  gyara daurin dankwalin ta, ta ce, "Ba wai tambayar ki a ke yi ba?"

               A takaice na ce "Fitsari zan yi". Banma tsaya jin ta bakin su ba Na kamo hanya ta ta fita daga cikin dakin a hasale, sai da na kawo daf da fuskar Gwaggo Talatuwa sarkin kicihi, da ta gama sakin baki da ido tana kallona cike da fuskar jin haushi, nan take na dade da dubin fuskarta na wanke ta da tukwicin wata kafurar tusa mai bala'in warin tsiya, a daidai lokacin da na fahimce komai ya tafi daidai nabar dakin a hanzarce tare da daukar wata waka ta Ado Gwanja a baki ina tafe ina raira abita kamar daman ni nayita   na barsu dwade da hanci dan babu bakin yin magana.......
*Follow me on wattpad and vote.

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now