*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•BE-SMART•»•—**_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**ASSALAMU ALAIKUM FAN'S*
*_Kamar yanda kuka sani wannan Buk na fara season2 d'inshi a 1/9/2020 mai taken suna da👇🏻_*
*_RUD'ANI!!💀_*
*_Yanzu a bisa wani kwakkwaran dalili na maida sunanshi yanda yake tun farko, inda idan baku manta ba a season1 mun tsaya dai-dai pages30 inda a season2 wato RUD'ANI muka tashi a page1 har muka yi page2 inda zamu tashi a Page 3 a RUD'ANI sai na canza na ci gaba da rubuta season1 d'in inda muka tashi a pages33 yanzu kuma page34, ina fatan yanzu kun fahimta Fan's🤗_**P...34*
Yarinyar da ke k'ok'arin nufato wajen da wannan mutumen yake cakk ta tsaya a dai-dai lokacinda fadawanta ke k'ok'arin tsayawa su ma, yarinya ce 'yar k'arama wadda shekarunta ba zasu wuce 8 ba, kamanni na da na wannan yarinyar sun b'ace sosai ba abinda muka baro ni da ita kamar abinda aka zana, kallon-kallon da muke yi wa junanmu ne ya sa gabad'ai hankullan dogaren dake wajen dawowa kanmu su ma mamaki ne shimfid'e a fuskokinsu wanda hakan ya sa wannan mutumen wanda na kira da suna Papa ya yi hanzarin katse shirun da muka yi ta hanyar cewa "Fatima ki zo ki gaida Aunty'nki kuma takwararki Fatima.!" had'ad'd'in idanuwanta ta waro waje tare da sakin wani k'ayataccen murmushinta mai cike da annuri wanda ya fito da ainahin dimples d'inta waje, aguje taje wajen wannan mutunen ta shige cikin jikinshi fuskarta d'auke da murmushi, ta ce "Papa wace ce wannan?." ta k'ark'are maganar ne tare da nuna mashi ni da d'an yatsanta guda tana mai k'ara shigewa jikinshi gami da b'oye fuskarta a k'irjinshi alamun kunya, a yanda tayi maganar tayi bala'in burgeni domin a yanda na fuskanta bacin k'uruciya tana da matuk'ar shagwab'a sosai, madubin dake gabana wanda sai a yanzu na iya halkanta da shi, na kalla naga fuskata d'auke da murmushi kamar ba abinda yake damuna nan take naji raina ya k'ara b'aci sosai na sake tamke fuskarnan kamar ba abinda ke man dad'i a yanda na nuna a bad'ilance, amma a zahirance cikin zuciyata cike take da k'aunar wannan yarinyar mai matuk'ar kama da ni dan ta yi matuk'ar burgeni, ina cikin wannan tunanen ne na halkanta da wasu matan wajen su hud'u tsaye a gefe na duka kyawawa masu kama da larabawa, had'e rai nayi ina kallon kowaccensu da ta duk'e kanta k'asa cikin girmamawa take gaidani ba tare da na amsa masu gaisuwar ba na d'auke kaina daga kallonsu inda naji Papa yana ce masu, "Ku yi mata iso izuwa d'akinta ta yi wanka idan kuka shiryata ku kaita wajen Zulfa.!" cike da girmamawa suka amsa mashi da "An gama ranka shi dad'e." cikin girmamawa suka ida k'arasowa wajen da nake guda ta rik'e hannuna na dama guda kuma ta rik'e hannun hagguna biyun kuma suka tsaya bayana suna biyar tafiyarmu a hankali, tafiya nake raina dik a jagule, maganar da Kaka ta tab'a gayaman ce a lokacinda take bani labarin mahaifina ta fad'o man sak a rai inda take fad'aman cewa "Ba'a da tabbacin mahaifina yana raye ko yana mace, amma ita a yanda take ganin tsawon lokacin da aka d'auka ana nemanshi ba'a ganshi ba ya sa take ji a jikinta kamar baya raye.!" kai tsaye wasu zafafan hawaye naji sun fara yi man ambaliya tare da tunanin a inda nake kuma wane ne wannan mutumin mai matuk'ar kama da Papa'na?" zuciyata ce naji ta bani amsa da "koma wane ne a wajenshi ya kamata naji" a fili na ce "Allah ya sa alkhairi ne, idan kuma shairi ne Allah kayi man maganinshi," murmushin da naji wad'annan 'yan matan sunyi ne ya ankaro da ni a dai-dai lokacinda muka iso a cikin wani makeken Palour'n wanda tsayawa ma fad'in had'uwarshi b'ata lokacin masu karatu ne, abin da zan iya cewa shine, babu abinda babu a cikin wannan makeken Palour'n sannan komai dake cikinshi golden and silver color's ne, dik yanda na so na ci magani akan kallon wannan santalelen Palour'n nayi amma na kasa, nan dai na turje idanuwana na bi komai daki-daki a palour'n ina kallo har muka isa Bedroom ko anan ma na sha kallo kamar wata k'asungumar bak'auya sai dai color's d'in dake d'akin irin color's d'in da ke palour'n ne da bisa gado har bisa kujerun dake make a wajen da ya da ce da su da komai dake cikin bedroom d'in dik wad'annan color's ne, a bakin k'ereriyar gado suka ajiye ni tare da barina sake da baki ina bin ko wanne lungu da sak'o da wani kallo na k'urulla, har suka fito daga cikin bathroom d'in a yanda suka barni haka suka same ni, ba tare da sunce dani ko uffan ba illa murmushin da suke tun d'azu yak'i gushewa a fuskarsu, suka ja ni sake da baki galalaa muka shiga cikin bathroom d'in, tsaye nayi ina kallon ikon Allah ganin tun da uwata ta haifeni ban tab'a ganin bathroom mai matuk'ar d'aukar hankali irin wannan ba, komai dake cikinshi a tsare yake kamar abinda aka sassaka da bangon ginar, ruwan da nake tunanin sun shigo sun had'a man ne na wanka na shiga dube-duben ta inda zan gansu domin naga wad'anda ke cikin bahon wankan kamar madara ce zallarta aka zuba a cikin wannan bahon tare da wasu jajjayen flowers masu cike da d'aukar hankali, sai wani daddad'an k'amshin da ke tashi a wajen wanda dik ya gama game bathroom d'in, ganin k'ok'arin rage tufafin dake jikina suke son yi ya sa a hanzarce na dakatar da su ta hanyar ce masu "Ya'isa! ku barshi ba sai kunyi ba!, ina ne wajen wankan?." dan naga alamun su dik abinda aka umarcesu shi suke idan nayi wasa ina ji ina gani zasu mayar da ni tumb'ur ranar haihuwata, d'ai daga cikinsu ce tayi k'arfin halin ce man "Ranki ya dad'e ga ruwan nan a cikin bahon.!" ta k'ark'are maganar ne cikin ladabi, kai kawai na iya gyad'a masu tare da yarfi da hannuna inai masu nuna da su tafi, a hanzarce suka bar bathroom d'in tare da janyo k'ofar gam suka rufe. Da kyar da walahaula tare da taimakon wani dattijo su Ammie suka samu nasarar baro cikin wannan jejin inda bayan sun fito babban titi ne suka samu nasarar cafke wani mai keke napep ya d'auke su gabad'ai ya jibgesu a gidan Ammie, a wajen Baba mai gadi suka amshe kud'in da suka biya mai napep d'in, bayan sun shiga gidanne sunji shi tsit suka dawo wajen Baba mai gadi suna tambayarshi inda mutanen gidan suke, anan ya shiga shaida masu cewa duka sun fita tun d'azu basu dawo ba, ba tare da damuwar komai a rai ba suka koma ciki suka yi wanka sannan suka shirya, Hajiya Maryam kuma ta saka kayan Ammie dan ta ce ko gida ba zata koma ba sai sun dawo daga wajen Boka dan ita ba komai ya sa take rawar jikin zuwa wajen Boka'n ba sai dan a raba tsakaninta da Ammie kowa yaji da tashi matsalar da take damunshi dan abinda ta gani jiya da dare ya yi matuk'ar wahalar da ita kuma ya tsorata ta, wata motar Ammie ta d'auka dukansu suka shiga sannan suka bar gidan a hanzarce suka nufi wajen Bokansu. B'angarensu Ya Abir kuwa bayan komai ya d'an lafa Aunty Intisar ta yi k'arfin halin ciro wayarta a jaka ta lalabo number Abba domin ta shaida mashi abinda yake faruwa, kira guda d'ai daga cikin Police d'in da ke kula da su Abba ya d'auki wayar anan ya shiga shaida mata halin da ake ciki, tashin hankali ba irin wanda ba su tsintsi kansu a ciki ba har dai suka godewa Allah, bayan Police d'in ya tambayi dalilin kiran da ta yi, nan ta shaida mashi abinda ke faruwa, cike da ban al'ajabi wannan Police yaje ya sanar da DPO abinda ke wakana, bayan sun tambaye Asibitin da aka kwantar da Ya Abir suka je duba shi, shi ma da suka je sun cinma the same case da matsalar su Abba wanda har yanzu an kasa gano takamammen abinda ke faruwa da su, wanda hakan ya kawo kwakkwanto a cikin zuciyoyin wasu Doctor's inda suka bada tabbacin cewa in dai ba abinda ya canza nan da kwana biyu zasu bada sallamarsu cikin gaggawa domin a samu damar zuwa wajen malaman addini da su su bincike halin da suke ciki dan yana yuwa lalurarar dake damunsu aikin jinnu ne".......
*FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert*
*#Be smart*
*^Pls share^*
ESTÁS LEYENDO
'YAR BALLAJJA'U
FantasíaSai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...