P...6

744 81 0
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

   *Dedicate dis page to my luvly fan's💋💋Luv u more*

         *P...6*

_Ina sauri zan wuce cike da wani hamshakin farin ciki, Na ji Gwaggo Talatuwa ta soma tofa albarkacin bakinta,  ta ce "Inna maganar zuwan ta Makarantar fa?."_

                _Nan da nan Naji raina ya yi mummunar baci da jin wannan maganar kamar naje na wanke, Mai bakin kara) da wani wawan Mari, domin duniya na tsane maida zance baya, harna shirya tsaf domin maida mata martani mai zafi, dan nasan shikan Mari idan  nayi yunkurin aikatawa, Ina da tabbacin kafin inkai ga sauke hannuna kasa Kaka ta yanka Ni da wuka, sai da nayi gyara murya dakyau ta yanda maganar zata fi fita dai-dai,  kafin in kai ga cewa wani abun, tuni naji Kaka ta soma magana da muryar ganin laifin wanda ake magana akai, ta ce._

                  _"Hmm Talatu kenan, ai maganar zuwa Makarantar kuma yanzu ai ta yi kwana, Tayi ta zaman tunda haka take so, gata ga waje."_

          _Gwaggo Talatuwa, ta kara da cewa " haka'ne kam, to Allah ya kyauta" tana gama fadin hakan taja komotstsenta ta koma cikin daki rainta dik a jagule, ta rasa abinda ke mata dadi game da Ni, saboda na zame mata kamar haki a makogoro, Ita ma Kaka ci gaba ta yi da yin harkar gabanta, Nima kuma tafiya ta nayi wajen da aka aike ni zuciyata cike da haushin Gwaggo Talatuwa._

~~~

           _Ina fita garka ko 5mins banyi da tsayuwa ba Na samu wani bawan Allah, na tsaida shi, sannan na shiga gidan na dauko kajin guda biyu ya yanka,_

           _Yana gama yankan, na shiga gidan na ajiye kajin, sannan na wuce Majalisar mu ta wasar kasa dake bayan gidan mu,_

~~~~~

          _Misalin Karfe biyar5 na dawo daga wajen wasar wanda hakan yana dai daga cikin tsarina, dan kar na yi aikin komai a gidan ko kuma na tafi Islamiyya._

           _Ko da na dawo gidan na cinma Kaka na hashin hutar murhu da niyyar aza ruwan zafin da za'ayi figar kajin da su, dan sai yanzu suka samu kansu waje guda, soboda tun lokacin da nabar gidan suketa famar bulekin aiki kamar wajen da shugaban kasar America zaya sauka._

        _Itama Gwaggo Talatuwa (Mai bakin kara),  duke take tana ida yin sharar waje._

           _Ba tare da ko waccen su  ta ce da ni ko uffan ba, sukaci  gaba da yin sabgar dake gaban su, Nima waje na samu gefe na zauna._

         _Har na kai zaune  na tuna da ban yi sallar Azzahar da La'asar ba, a hanzarce na mike tsaye na tafi na dibo ruwa cikin buta naje na dauro alwalata, a dai-dai wannan lokacin Kaka ta gama hashin hutar ta aza tukunyar ruwan zafin, Ita ma Gwaggo Talatuwa  ta gama yin sharar amma kicihi ya hata kwashewa sai famar tambaya ta take "Wacce sallah ce zanyi yanzu?" Tare da kashe kunnayenta ta na jiran amsar da zan bata kamar daman ita zan yima sallar._
              _Wanda hakan ya ankarar da Ni na gano  jiran de take taji na ce "Azzahar ce zanyi" su hauni da masifa Ita da Kaka,  sai da na tamke fuskarnan takin babu alamun wasa a tattare da ita sannan na ce mata "La'asar ce zanyi" ina gama bata amsa ban ma tsaya jiran abinda zata sake cewa ba na kama hanya ta, ta shiga cikin dakin, na barta tsaye rike da tsintsiya a hannu._

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now