*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**P...23*
Haka dai rayuwa tayi ta juya masu da dad'i da babun dad'in dik haka ake daurewa a zurawa sarautar Allah ido.
Kusan shekarar Rafi'at 3 da yin aure amma ko b'atan wata babu balantana a saka ran yin b'ari, har lokacin auren k'anen Mijin ta ya gabato wato Mukhtar inda ya yi auren shi cikin farin ciki da godiyar Allah, shekarar su d'aya da Aure Allah ya azurta su da samun karuwa d'a namiji inda ya ci sunan shi da Abir farin ciki a wajen su kam ba ya kwatantuwa Sai da yaron yakai shekara guda da haihuwa Allah ya yi ma mahaifiyar su Jabiru rasuwa, halin kunci da halin damuwa ba irin wanda basu shiga ba, abin dai sai hamdala
Haka dai Allah ya yi ta azurta Mukhtar da samun k'aruwa dik bayan shekara biyu inda a wannan lokacin yake da yara 3 kuma duka Maza Abir shine na farko sai Bikhram sannan Fadil, a lokacin kuma Daddy yakai shekara kusan ukku da samun aiki a Federal Illar revenue services, as a Managen Director,
Arziki kam sai k'ara hab'b'aka yake a wajen shi wanda hakan ne ya zamo sillar fara canzawar halayyan Rafi'at na kirki sannu-sannu a hankali suna komawa na shairi a wajen iyalan shi, inda kai tsaye ta tsinci kan ta cikin tsananin hassada da kyashi ga iyalan k'anen Mijin ta harda shi d'in, dik da shi Jabiru ba abin da ya canza tsakanin shi da k'anen na shi sai tulin farin ciki da kyautatawar dake tsakanin su, dan shi ma Jabiru'n ya dad'e da kammala karatun Degree d'in shi tun-tuni kuma takardun shi sunyi matuk'ar kyau sosai sai dai bai damar da kan shi na samun aikin gwamnati ba wanda shi a ganinai b'ata lokacin kan shi ne zaiyi a banza shi ya sa ya nema d'an kasuwancin sa na saida Yadikan Hijabbai yana yi kuma yana samun riba dai-dai gwargwado sai dai koda hakan ta b'angaren Rafi'at ko kad'an bata ganin hakan ita dai burin ta suyi kud'i fiye da na Mukhtar
Nan dai da taga abin ba mai iyaka ba ne, ta yafa mayafin ta taje wajen wata k'awar ta mai suna Maryam domin ta bata shawarar da ya dace,
Daganan ita kuma ta d'ora ta a hanya wajen biyar Bokaye lungu-da-sak'o akan a dak'ile dik wata hanyar da Mukhtar ke samu ta arziki a d'orawa mijin ta, Sai dai dik inda taje ace mata abin ba mai yuwa ba ne, daganan dai ta samu nasarar samun wani tantirin azzalumin Boka inda ya shaida mata da cewa dole ne sai ta samu haihuwa da Mijin nata kuma haihuwar ta zamana D'a namiji ne ta haifo, shi kad'ai zai sa ta iya mallakar rabin dukiyar K'anen mijin nata idan har tabi sharud'd'an da zai gindaya ta akai nan gaba, sosai ta aminta da wannan karatun nashi
Bayan taje gida ta tayarwa da mijin nata hankali akan tana son sanin inda matsalar take a wajen su da har yanzu sun kasa samun haihuwa, nan dai dik inda ya b'ullo mata ta toge mashi har dai ya yanke hukuncin zuwa asibiti domin a gano inda matsalar take
Bayan anje anyi gwaje-gwajen da ake nan di Doctor ya tabbatar masu da matsalar daga wajen Mijin nata take sai dai suna sa ran magungunan da aka rubuta mashi idan dai har ya ci gaba da amfani da su kamar yanda ya kamata to zasu iya samun haihuwa nan bada jimawa ba
Hankalin ko wanne daga cikin su ba k'aramin tashi ya yi ba da jin wannan furucin bayan sun dawo gida cin mutumci da gori ba irin wanda Ammie bata ma Abba ba har dai ta gaji ta bari shi dai bai ce da ita ko k'ala ba ya saka mata ido domin shi mutum ne mai hak'uri da juriya baya son tashin hankali ko kad'an dik yanda yake kuwa
Bayan komai ya lafa ne taje gidan Maryam k'awar ta ta kwashe komai ta fad'a mata, anan dai suka yanke hukumcin komawa wajen wannan Bokan domin su sunar da shi abin da ke faruwa
Bayan sunje sun gaya mai komai dan basu b'oye mashi ba tare da neman mafita a wajen shi
Nan dai ya ce masu mafita d'aya ce idan har ta Aminta ta biyo shi d'aki! domin shi ya bata abin da mijin nata ya kasa bata
Ba tare da tunanin komai ba tabi shawarar k'awar ta da kuma hud'ubar shaidan ta biye ma son zuciya suka aikata alfasha ita da bokan
Bayan kwana biyu laulayin ciki ya kama ta wanda hakan ya fara bayyanar da tana d'auke da juna biyu
Mamaki sosai ya kama Jabiru matuk'a Sai dai da ya tuna wannan abin ba komai ba ne a wajen Ubangiji ya saka shi farin ciki sosai tare da k'ara tarairayar matar ta shi dari bisa dari har bai son abin da zai tab'a mashi ita
Wanda samun Cikin ta ya yi dai-dai da samun cikin Mummy wanda lokaci guda suka haife abin da ke cikin Cikin nasu duka Mata
A b'angaren guda kam farin ciki ne a wajen uwar d'iyar marar misiltuwa domin tayi ta rok'on Allah ba dare ba rana akan ya azurta ta da samun k'aruwar D'iya mace a wannan karon
Ta b'angaren guda kuwa uwar D'iya harda kuka hinhinhinn kamar ta turbud'e kanta akan bak'in cikin samun 'Ya mace wanda wasu mutanen suke kallon kukan kamar na farin ciki ne irin dad'ewar da tayi bata ga jinin ta ba
Bayan biki
D'iyar Mummy taci sunan ta da Intisar
Inda ita kuma d'iyar Ammie taci nata sunan da Khairat
Sati guda da biki Ammie ta yafa ta koma wajen bokan ta gaya mashi abin da ta samu
Nan dai ya kwantar mata da hankali akan ta jira har yarinyar ta girma sannan tayi dik yanda za tayi ta had'a auren ta da D'an K'anen mijin nata a sannan wani mummunan abu zai faru da iyalan k'anen mijin nata daganan ne zai zama dik wani abin da wannan k'anen mijin nata ya mallaka zai dawo a tafin hannun ta amma kuma sai ta sadaukar da wani abin da take mutuwar so, sai dai ya tabbatar mata da cewa koma menene ba zata ji shi a yanzu ba sai lokacin ya yi.
Haka dai ta dawo gida zuciyar ta fesss cike da wani zuzurutun farin ciki sannan babu nadama ko kad'an a cikin ta sai ma k'arin harzuk'ar da tayi na burin ganin bayan mak'iyanta ko ta halin k'ak'a ne
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...