P...32

317 49 2
                                        

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•BE-SMART•»•—*

*_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE GA MASOYAN WANNAN LITTAFIN A DIK INDA KUKE INA MATUK'AR ALFAHARI DA KU, MUSAMMAN..👇🏻_*

*_BALKISU AHMAD_*
*_ANTYN GAYU_*
*_SAFIYA SHEHU DALIJAN_*
*_MOMYN SIYAMA_*
*_BILKISU_*
*_Da dai sauransu_*

*_Ina jin daɗin cmmnts ɗinku sosai ku ji daɗinku da wannan page_*

*P...32*

A fusace Ammie ta tunkaro wajen da Hajiya maryam take da sunan idan ta kamata zata mata shegen duka ne dan ita a halin yanzu jin kanta take kamar wani Boss, wani wawan shuri ne ta fara d'auke Hajiya Maryam da shi kafin ta dawo gabanta tayi tsaye tana huci tare da furzar da wani busasshen iska a baki, daga bisani ta ce "Maryam! wlhy dambe nake son muyi dan a kece raini tsakanina da ke, ko kina ganin kamar tsoronki nake ji?.!" Jin Hajiya Maryam tayi shiru ta kasa bata amsa illa kafe ta da ido da tayi ko k'iftawa babu wanda a zahiri ganin take kamar dik ita ce take ma wannan walgalallen kallon amma a bad'ilance Fatalwar dake gabanta ce take ma wannan kallon, wanda hakan ya sa haushin abin dik ya k'ara turmuk'e ta ta aza hannayenta biyu saman fuskarta tana huci kamar maciji cikin d'aga murya ta ce "Wlhy yau gabad'ai haushi kuke bani kamar na kashe ku nake ji in huc........!" wani d'an k'aramin Jaki ne da taga yana k'ok'arin tunkaro wajen da suke ya sa ta kasa k'arasa zancen ta nufe wajen da yake tana cewa Maryam "Saninki da nayi a rayuwata har kika cuceni kika kaini ga halaka Allah ya shiga tsakanina da ke! muguwa bak'ar annamimiya.!" Ta k'ark'are maganar ne a dai-dai lokacin da take kaiwa k'ad da k'ad da wannan Jakin, murmushin jin dad'i tayi ba tare da damuwar komai ba ta d'aga gudan hannunta sama ta dake wannan Jaki'n tana cewa "Shege ka zo a lokacinda kake da amfani.!" sannan ta dubi gefe da Khairat take tsaye dik ta wani sandare ta ce "Idan kin gama abinda ki ke ki zo ga Jaki Allah ya kad'o muna daga sama dan mu samu mu fita a cikin wannan dajin da nake ganin babu tantama akwai mugayen aljannai a cikinsh.......!" maganar da taji wannan Jakin ya yi ne tayi bala'in rikitar da k'ok'on kunnenta inda taji yana cewa "Allah ba zai tab'a taimakon marar imani irinku ba.!" a tsorace ta murje idanuwanta cikin k'arfin hali zata sake kallon wannan Jaki'n mai magana da tunda uwarta ta haifeta bata tab'a ganin dabba makamancin wannan ya yi magana ba, sai dai kallon da zata sake mashi kenan ta ga ya koma wata irin mugunyar halitta marar kyan gani mai cike da ban tsoro da ban firgici, bud'ar bakin da taga ya yi ne da niyyar zai had'iyeta ya sa nan take ta zame jiki daga wajen da take ta fad'i k'asa kwance sumammiya, Hajiya Maryam kam bata juyo bayanta ba balle taga abinda ke faruwa sai dai ganin hannun wannan basamudiyar halitta na famar zulowa k'asa da niyyar d'aukarta nan take bata sake sanin inda kanta yake ba, Khairat dake tsaye a waje guda kamar wata jaruma tana kallon abinda ke faruwa sai dai ita ko kad'an bata ga abubuwan da suka gani ba ita dai kawai taga suna zamewa k'asa suna kwantawa, wata b'ullumar Mage ce bak'ik'irin taga ta hiranyo ta bayanta aguje kamar wadda aka koro wanda hakan ya sa a zabure Khairat taja da baya tana kallon abinda ke gabanta cikin k'arfin hali saida ya kawo k'ab da ita sannan ya dugungune sai dai ganin Mage ce ya sa taji hankalinta ya soma kwanci a sannu, bata ankara ba taga wannan Magen ta zuro mata ido wanda sai da taji tsikar jikinta ta tashi a d'an tsorace ta fara ja da baya tana kaucewa wannan magen sai jin tayi wannan Magen ta ce mata "Ke ba zaki suma ba ne?.!" Ihu Khairat ta sake a dai-dai lokacin da taji wannan Magen ta mata magana kafin tayi wani yunk'urin kiran sunan Ammie tuni wannan Magen ta shek'o cikinta a guje ta hira sama da niyyar hiranyowa saman jikinta ai kuwa tuni Khairat ta ce "Ni ma na bi su Ammie.!" Nan take ta sulale a wajen. Tab'a gashin kaina ne da naji alamun ana yi ne ya saka ni bud'e idanuwa na a hankali ina k'ok'arin sauke su kan wanda keman shafar, a tsorace na mik'e zaune tare da d'agawa daga wajenda nake ina kallon mutanen dake kewaye da ni tare da wanda yake tab'a gashin kaina, dube-dube na shiga yi ta ko ina ina mai k'ara yima wajen wani kallo na k'urulla dan ji nake kamar na san wannan wajen indai ba gizaune idanuwa ke man ba, wanda ke shafaman kai ko kad'an banga ya kalle wajen da nake ba naga ya duk'e kanshi k'asa yana kallon faratan hannunshi dake make da zobba na gold, wani d'an k'aramin k'arfe ne na hango a wani wajen wanda zamanshi ya dace da wajen da yake sai famar basbanniya yake da wata kyakkyar walk'iya, wanda kana ganinshi ko ba a fad'a maka ba kasan darajar wannan k'arfen tafi k'arfin a saye shi da kud'i, wajenshi na nufa zan d'auka domin na samu nasarar kare kaina a wajensu sai dai ban ida kai hannuna gare shi ba naji wani abu zurrrrrr ya ziyarce cikin hannuna kamar shocking, nan take naji jiwa ta fara d'iba ta a wajen ba tare da b'ata lokaci ba naji alamun gangar jikina na son kasa d'aukata tuni naji na sulale k'asa zan fad'i ba tare da zato ko kuma tsammani ba na ga wannan mutumen dake kusa dani a d'azun ya taroni, sai a sannan na samu ganin kyakkyawar fuskarshi mai shimfid'e da wani hamshak'in murmushi k'arara a samanta, a lokacinda da muka yi ido hud'u da shi naji hankalina ya soma tashi fiye da ko wanne lokaci domin ko a cikin duhu naga me wannan fuskar da na dad'e ina kallon photonta ga Kaka tun ina 'yar k'ank'anuwata zan iya gane ta, cike da wani mugun firgici nake kallonshi ban san lokacinda na bud'e bakina na ce. Ya Abir ne zaune a saman darduma yana gabatar da azkar bayan ya gama sallolinshi na nafila anan Asibiti wajen Ya Fadil dan shi ke jinyarshi, Ni ce na fara fad'o mashi a rai kafin su Mummy da har yanzu ya kasa gasgata cewa mutuwa suka yi, yana cikin yin tunane-tunanenshi ne har ya ji an fara kiraye-kirayen sallar Subahim ya tashi da hanzari ya sake yin wata al'wala sannan ya tafi masallaci. B'angaren su Abba kuwa tun lokacinda Alhaji Sulaiman ya b'ar gidan, ya shiga cikin rud'u da tashin hankali, haka ma su Intisar in banda aikin kuka ba abinda suke yi, a daren ranar dai ba wanda ya runtsa a cikinsu haka ma Alhaji Sulaiman. Safiya na wayewa Abba da Alhaji Sulaiman suka bazama wajen 'yan-sanda da kuma kafafen yad'a labarai suka bada cigiyar su Ammie...........
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*_#Be-smart_*
*^Pls shere^*

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now