P...4

944 99 2
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

      *Wannan page sadaukarwace a gareku masu yiman posting, kuji dadin ku da wannan😘😘😘 godiya marar adadi, Allah Ya biyaku da mafificin abin Ameen*

           *P...4*

_"Babbar butaddumen". Itace kalmar da naji tayi gaggawar fitowa daga cikin kogon bakin sa, sannan ya kara da cewa "Jar'uba! wlhy ba zata sabu ba bindiga a ruwa, kayan da na aro wajen Ashiru Mai wanki za'a wulakanta haka, billahillazi sai an fanshe su, ko kuma yanzu mu ziyarce PoliceStation ni da  uban mutum, kuma kafin mu tafi  sai na tabbatar da na gama cin ubanki da kyau, ta yanda ko gobe ba zaki kara sha'awar aikata ma wani hakan ba._
                
           _Tsaye kawai nake na sandare waje guda ina kallon shi cikin fuskar ban tausayi dan kar ya yi yunkurin aikata man wani abu amma tun yanda naji yayi maganar "sai yaci ubana" sai nima rashin mutumcin nawa ya tashi sama, na ce "wlhy sai dai kai kaci ubanka domin ubana ya kada naka cikin harawa ya burka tusa dari da goma", nan take na maida abin waka, sai na kai intaha sannan na sake daukar wata  ayar,_

                _Ai ko nan da nan naga wannan gayen kauye, ya hiranyo sama ta kaina a harzuke   zai kaimin wani wawan naushi a saman bai, Nan take, na hira sama kamar wata tsuntsunwa na kauce daga wajen,_
               _A maimakon na shige cikin gidan  kuma sai na kara fitowa waje gabadai,  wanda hakan yasa  ya samu nasarar wazgeni da wani wawan mari, sai da naga wuta bauuu a cikin idanuwa, a dabirce na shiga tangal-tangal sai jina nayi a saman katifar kasa ina mulmula a kasa  kamar mulmulallen dawo, nan na shiga sakin ihu kamar wadda ake yankan naman jikinta tana gani._

                _A hanzarce naga wani bawan Allah ya sheko a guje Ya yo ta wajena ya cirani sama, na mike tsaye,  yana tanbayata abin da ya hadani da wancen gayen,_
               _Amma ban iya cewa da shi ko uffan ba, domin kukan da nake yi  ya ci karfina,_

     _Kai tsaye wajen wannan gayen ya nufa dake tsaye tun dazu a wajen da yake ya wani sha omo kamar wani katon soja sai famar huci yake yana furzar da iska kamar ya fashe a wajen,_

       _Ya ce "Subhanallahi, Malam miye hadin ka da waccen karamar yarinyar? da shekarunka sun ninka nata sau 3 ko hudu"._
           _Cikin  furzar da wani zazzafan iska a waje, ya soma korama wannan mutumen baya ni kamar yanda abin ya faru, sai dai ya toge zancen da cewa, "Da gangan na aikata mashi hakan._
                     _Kafin ya ida karkare mashi bayanin  tuni ya ji saukar wani wargajejen katon dutsi a saman goshin shi, sai da, ya ce "Kwa kwal" nan take wannan gayen ya bare katon bakinsa gabadai ya buga wata kafurar kara tare da dahe goshin shi da hannayen shi  biyu ya kai duke yana saukar da wata nannauyar a jiyar zuciya cikin karfin hali, da ga nan kuma sai ga bulbulowar jini malalala kamar abin da aka saka yuka aka yanka,_

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now