P...42

288 47 19
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•BE-SMART•»•—*

*_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

P...42

Washe gari misalin k'arfe 10:00am aka shiga Koto, inda wasu har sun hallara a cikin koton suna jiran lokacin fara shari'ar ya gabato kasancewar an saka lokacin ne da k'arfe 10:10am, a gefe guda Abba ne zaune tare da Alhaji Sulaiman had'i da Malam tare da Ya Abir gami da Ya Fadil, sai kuma gefe guda Aunty Intisar ce tare da Yumra da Yubra, ta wani b'angaren kuma masu laifi ne tsatstsaye a gefensu da aka ware musu Police tsare da su, Ammie ce tare da Khairat da kuma Hajiya Maryam da fuskokinsu dik sun wani sussundule sun yakuce kamar ba su ba dik kamanninsu ya canza, tare suke da wad'annan k'attan 'Yan Jan-bulo wad'anda kallo guda idan ka masu ba zaka so ka sake masu wani kallon ba  domin wasu irin manya-manyan samudawa ne naji da fad'i kana ganinsu kaga alamun rashin imani k'arara zazzage a fuskokinsu, su wajen goma sha ukku ne gabad'ayansu, ta wani b'angaren kuma Alk'ali ne zaune shi da CP a cikin jerin kujerun da aka ware ma 'yan kallo, fuskokinsu ba yabo ba fallasa, ba a wani b'ata lokaci ba muka iso wajen Ni da Papa da kuma Mummy Zulfa tare da Fatima wanda a wannan lokacin mu hud'u kad'ai muka bayyana kuma ba a cikin kayan sarauta ba, mun dai yi shigarmu ta alfarma, sai kuma masu tsaronmu wad'anda dik a wannan wajen ba mai ganinsu domin dik a b'ace suke, gabad'ai ilahirin hankalin mutanen dake cikin wannan koton kanmu ya dawo, kowa yana kallonmu cike da burgewa, kafin idanuwana su kai ga kowa ga Ya Abir suka fara sauka wanda shi ma gaba d'ai ilahirin hankalinshi da tunaninshi dik sun karkata ne izuwa wajena, wata irin kunyarshi ce naji ta ratsa jinin jikina wanda kai tsaye naji wani hamshak'in murmurshi ya kub'ce man, shi ma shi ya sakar man, ganin idanun mutane ya fara dawowa kanmu ya saka ni janye fuskata daga kallonshi cikin shigewa gashi. kai tsaye wajensu Abba Papa ya nufa wad'anda tun zuwanmu wajen suka mik'e tsaye suna kallonmu fuskokinsu d'auke da murmushi, bayan sun gama gaisawa ne ya zauna tare da su, Ni da su Mummy zulfa dukanmu wajensu Yumra muka nufa muka zauna tare da su, wanda tun kafin mu k'araso wajen suke zumud'in isowarmu, nan muka shiga gaisawa cike da annashuwa, inda kan ka ce me k'oto ta cika tank'il ko wajen zama babu ya gagara ta ko ina mutane ne, ba awani b'ata lokaci ba Alk'ali ya iso wanda nan take aka fara gudanar da shari'ar inda gabad'ayansu masu laifin sun amsa laifinsu, musamman ma su C.P wad'anda tun lokacinda aka fara gudanar da shari'ar suke jin gabansu na ta famar fad'uwa ridididi, wanda hakan ba k'aramin rikici da dagule masu lissafi ya yi ba, lokacinda aka kirasu gaban koto, cikin fita a cikin hayyaci suka d'inga tona ma kansu assiri a gaban kowa dake wannan wajen, wanda hakan ya janyo cece-kuce a tsakanin mutanen dake cikin Koton, sosai suka yi tir da Allah wadai da hali irin na su wanda hakan ba k'aramin kwarin gwiwa ya bawa Alk'ali ba wajen yanke masu hukunci dai dai da abinda suka aika, inda Ammie da Hajiya Maryam aka yanke masu hukuncin d'aurin rai da rai a gidan gyaran hali, Khairat kuma aka yanke mata hukuncin shekara30 a gidan gyaran hali, su kuma 'Yan Jan-bulo aka yanke masu hukuncin d'aurin rai da rai ta hanyar halbi, CP da Alk'ali kuma aka yanke masu hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekara goma-goma tare da haranta musu ci gaba da aikinsu ko bayan sun fito, bi ma'ana an amshe dik wani muk'amin dake hannunsu, sannan aka wanke Fatima twas daga laifin da ake zarginta, sosai kowa dake cikin wannan k'oton ya ji dad'in adalcin da aka yi wajen yanke wannan hukuncin inda su kuma wad'anda aka yankewa hukuncin suke cike da kunci da takaicin mai had'e da dana sanin abinda suka aikata, su Ammie kuwa dukansu kuka suka fashe da shi a wajen suna tubarwa Ubangiji,  Alk'ali na buga gudumarshi ya koma office d'inshi, a sannan kowa ya samu damar fita daga cikin Koton, su Ammie kuma aka wuce da su Prison inda ana fitowa da su 'yan jarida suka yo kansu sai dai ba wanda aka bawa damar yin magana, inda ni kuma koda 'yan Jaridar suka yi yunk'urin maida akalar aikinsu ta kaina tuni har mun shige mota mun tayas. Kai tsaye gidan Abba muka nufa inda acan muka zauna dukanmu harda Malam tare da su Papa da su Ya Abir, a babban Palour'n gidan dukanmu muka sauke farali, bayan an bud'e taron da addu'a anan wannan Malamin ya shiga yi muna nasihohi, inda yake janyo muna Aya yana fassara muna, bayan ya gama muna nasihohi ne ya shiga yi muna hud'uba ni da Ya Abir,  bayan Malam ya gama muna hud'ubar ne ya yi sallama da su Papa akan shi zaya koma makarantarshi, hakan ya saka suka mashi rakkiya har a bakin get wanda Ya Abir ne ya je ya maida shi gida, tun a wannan lokacin ba mu sake sakashi a idonmu ba, musamman ma ni da nake jin kaina dik wani iri sabida rashin ganinshi, Mummy Zulfa kuwa d'akin da aka saukesu ne ta koma ta barmu a Palour ni da su Aunty Intisar dake ta famar kod'a Kunshin da aka man da kuma Kitsona tare da fad'in irin kyawon da na k'ara sosai ta sanadiyyar wani mahaukwacin gyaran jikin da aka man, ni kam in banda murmushi ba abin da nake masu domin kwata-kwata hankalina ba akansu yake ba!. wasa-wasa har k'arfe hud'u tayi banganshi ya zo gidan ba gashi ina bala'in jin kunyar amsar wayar d'ai daga cikin k'annenshi na kirashi. ina kwance nayi ruf da ciki a saman gado naji Mummy Zulfa na famar tab'ani a hankali tana kiran sunana, mik'ewa nayi zaune tare da amsa mata cikin damuwa domin na san abinda aka saba ne za a yi, wani had'ad'd'en turare ne wanda kana jin k'amshinshi ka san wannan had'in sai dai aljannai wanda ke gefenshi daban daddad'an k'amshinshi dik ya gama k'amshe d'akin, ina cike da jin dad'in wannan shauk'in da na fad'a ciki ba tare da na shiga yunk'urin saukowa daga saman gadon ba kai tsaye naji ya azaman wata yar guntuwar riga a saman tafin hannuna nan take naga wannan rigar sanye a jikina, ban wani damu ba sabida indai magic ne ba yau na saba ganinshi a wajensu ba, kai tsaye ta ce da ni naje na tsugunna a saman wannan kaskon, cike da damuwa na kalleta zan mata magana ta turmuk'e man fuska, tun da na ga alamun hakan ban tsaya mata musun komai ba na je na tsugunna kamar yanda ta ce, dan ita mace ce ba mai son musu ba, wani bargo ne naji ta aza man a jiki, nan da nan zufa ta fara rufeni sai maik'o nake ina hawaye. sai da na kusan shahe wajen minti20 sannan ta d'auke man wannan bargon, ta ce na tashi, ina tashi ta mik'oman wani had'in cike da cup ta ce sai na shanyeshi, ina matsar kwalla na amshi wannan abin na sha, haka dai Mummy Zulfa ta yi ta wahalar da ni da kayan hakukuwa har magrib, bayan nayi wanka tare da yin sallarmagarib, nan kuma ta ci gaba daga inda ta tsaya, kala ina boye kukan dake son kub'ce man har na kai ga sakin abina, sai da aka fara kiraye-kirayen sallar isha'i, bayan na sake yin wani wanka cikin humra da wasu had'ad'd'in kayan k'amshi irin nasu na aljannai sannan nayi sallar Isha'i, ina gamawa kuwa Mummy Zulfa da kanta ta shiga shiryani dikda da kayan jikina ita ce ta sakaman, wani mugun kyawo ne na ga nayi har na Innadillahi wa'inna ilaihim raju'un, ko doguwar rigar da ta sakaman ma abin kallo ce gashi kalar rigar ba k'aramin kyawo ta k'ara ma fatar jikina ba, sai da ta shiryani tsaf sannan tafito da ni babban palour'n, anan muka same su Abba da Papa tare da Ya Abir zaune suna jiran fitowata, wani had'ad'd'en k'amshi ne da ya dinga ziyartar kussayen hantunansu ne ya saka su taddo kansu sama dan ganin abinda ke tafe da wannan sanyayyen k'amshin, tsakanin Abba da Ya Abir dukansu idanuwansu a kaina suka dira sai dai shi Abba yana ganin ni ce ya yi hanzarin saukar da kanshi k'asa yana magana da Papa, shi kam gogan har muka kawo daf da su bai d'auke idanuwanshi gareni ba, duk'awa nayi har k'asa kaina na duk'e na gaidasu, suka amsa man cikin kulawa, a hankali na d'an d'ago kaina na kalleshi, nan take muka had'a idanuwanmu waje guda, a hanzarce na janye fuskata tare da sake noce kaina k'asa ina tuno irin mugunyar had'uwar da ya yi man sosai a cikin wannan shigar da ya yi, sanye yake cikin wata tsadaddiyar shadda pitch wadda kalarta ta zo dai-dai da fatarsa, hullar kanshi ma pitch color ce sai agogon gold dake d'aure a tsintsiyar hannunshi haka ma tsadaddin takalman da ke sanye a k'afarshi, ba tare da wani b'ata lokaci ba Abba ya shiga yi muna nasiha mai ratsa zuciya, bayan ya gama ma Papa ya d'aura da tashi tare da yi muna fatan alkhairi da fatan kasancewa tare har abada, bayan sun gama yi muna nasihohin ne suka bashi damar da ya d'auke matarshi su koma gida tare, inda tun lokacin da ake muna hud'ubar kuka nake har lokacin da aka ce Ya Abir ya d'aukeni mu wuce gida tare, cike da wani matsanancin tashin hankali tare da kewar iyayena da nake jin yana ziyartar dik ilahirin sassan jikina na fad'a jikin Mummy Zulfa ina rusa kuka mai cike da ban tausayi, ita ma kukan ta saka tana lallashina tare da kwantar man da hankali, da k'yar de da wala-haula tare da hamdala ga Ubangiji kukan da nake ya d'an tsaya inda shi kuma gogan har ya dad'e da fita waje wajen da ya yi parking d'in motarsa, Abba ne da kanshi ya je ya kiranyo su Aunty Intisar akan su zo muyi bankwana, kasancewar tun lokacinda aka kira sallar azzahar naje nayi sallah basu sake ganina ba sai yanzu da Abba ya kirasu, su ma kasa ganeni suka yi tare da son gasgata irin wannan had'uwar da nayi sai dai ganin ina kuka dik ya saka jikinsu yin sanyi tare da katse masu zuciya suka shiga lallashina ganin kukan da nake ba na wasa ba ne ya sakasu su ma kukan, sai da muka kusan kwashe wajen 10mins a haka, sannan Mummy Zulfa ta jani a hankali tare da su Aunty Intisar muka fito daga gidan, fadawan Mummy Zulfa na biye da mu a baya, ko da muka iso wajenshi har ya gyara parking mai gadi ya wangale mashi get ni kad'ai kawai yake jira, yana ganinmu ya bud'e man marfin kujerar gaba, Mummy Zulfa ta sakani ciki tare da gyaraman zamana sannan ta rufe marfin motar tare da yi muna fatan alkhairi, godiya mai tarin yawa Ya Abir ya yi mata cike da ladabi kafin mubar gidan, sai da su Mummy Zulfa suka ga mun fita daga cikin gidan gabad'ai sannan suka dawo cikin gidan zuciyoyinsu cike da kewa ta................
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
#Be smart
Pls shared

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now