P...31

320 50 2
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•BE-SMART•»•—*

*_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*P...31*

Haske ne mai had'e da wani daddad'an sanyi kamar kana cikin gadina ya fara tashi a wajen, daga bisani kuma sai ga b'ullowar wata keken doki daga cikin giragizai tana k'ok'arin saukowa k'asa d'auke da wasu had'ad'd'in kyawawan mata ajin farko a cikinta wad'anda ke cikin shigarsu ta masarauta, kai tsaye wajenda nake kwance suka dira ba tare da wani b'ata lokaci ba suka d'aukeni suka saka a cikin wannan keken doki daganan wannan keken ta sake tashi sama kamar tsuntsun, b'at muka b'ace kamar k'iftawar gira. Cike da wata mugunyar harzuk'a Hajiya Maryam ke fad'in, "Ai laifin ba na Khairat ba ne, laifin naki ne! tun farko me ya sa ke ba kiyi aikin da kanki ba?, ko da dai ni meye damuwa ta a ciki da har zan tsaya b'ata raina akan banza, ko ma me ya faru kanku kuka cuta ba ni ba danni ba abinda ya shafe ni da matsalarku kawai dai ni nasan na taimake ku ne.!" cike da mamaki Ammie ke kallonta tare da tsayar da kukan da take ta famar zabgawa, ta ce "Maryam kin san abinda ki ke fad'a kuwa.?" a shak'iyance Hajiya Maryam ta ce "Ni ko nasan abinda nake fad'a sai dai idan ke ce bakya a cikin hayyacinki, sannan maganar da zan gaya maku ta k'arshe ita ce! wlhy! wlhy!! ba d'an shegiyar da zai sake shigarman mota a cikinku dan ba zai tab'a yuwa matsalarku ta shafeni ba, k'iri-k'iri ku jazaman masifa a banza a wofi? Inaa wlhy ba zai yuwu ba.!" a marairai ce Ammie ta ce "Haba Maryam! wai ke me ya sa wani lokacin baki da tausayi ne?, kinga ni dik ma ba wannan ba! yanzu mu koma cikin mak'abartar mu fara tono yarinyar tunda ma bamu saka ta dai-dai ba, sai mu saka mata wannan layar kinga daganan komai ya dawo dai-dai sai mu zauna mu sasanta kanmu.!" wani banzan kallo ne Hajiya Maryama ta fara jefo mata, cikin nuna halin ko in kula ta ce "Ina ga k'ila kin manta yanda Boka ya gaya maki ko? to kinga ni ba gantalalliya ba ce, na san aikin da nake yi wlhy ba za a yi wannan da ni ba! kinga tafiya ta kuma kar wadda ta sake ta biyo ni a cikinku.!" wata mugunyar fizga ce Ammie ta mata mai cike da takaici dan taga alamun dagaske take, ta ce "Wallahi baki isa ba Maryam idan kinga kin bar wannan wajen to tare da mu ne kuma mun ida kammala aikin da ya kawo mu, sannan da ki ke cewa kar mu jaza maki masifa, tun farko ubanwa ya jefa ni cikin wannan bak'ar masifar?.!" sai da Hajiya Maryam ta fara kecewa da wata shegiyar dariya sannan ta ce "Ubanki ne ya jefa ki cikin wannan bak'ar masifar Rafi'at! na ce ubanki ne tunda tun farko halin talauci ne ya kashe su har ya yi sanadiyyar barowarki k'auyenku ki ka dawo birni wajen yawon karuwanc....!" wata mugunyar cakuma ce Ammie tayi mata tare da shak'e mata wuya takin kamar da gaske kasheta d'in zata yi, ta ce "Yau sai na gwada maki cewa ke k'aramar 'yar iska ce Maryam, wlhy sai kin san yau kinyi da 'yar halak.!" sannan ta dubi wajenda Khairat take tsaye cikin tashin hankali tana kallonsu, ta ce "Ke kuma da kazat-kazat kije ki tada muna mota mubar wajennan da hanzari kar assirinmu ya tonu.!" ba ta jira cewar Khairat ba ta koma kan Hajiya Maryam ta ce "Matsiyaciya wlhy sai dai ki mutu anan dan anan zamu barki kuma....!" maganar Khairat ce ta katse mata hanzari inda taji tana cewa "Ammie nifa banga motar ba.!" Ashshar Ammie ta fara d'unguma mata kafin ta ce "Shegiya ki bini a hankali ke ma bada jimawa ba zan dawo kanki wlhy kuma sai na maida ki wajen shegen uban..!" shiru tayi tare da sakin Hajiya Maryam daga takurarren rik'on da ta mata, tana kallon wani wajen na daban wanda su ma ganin wajen da ta k'urawa ido ya sa suka maido hankalinsu gabad'ai a wajen, cikin wani mugun tashin hankali Ammie ta ce "Maryam ya naga motarki na tashi sama? daman tana da fikafikai ne?." a tsorace Maryam ta ce "Idan ma tana da ai da kinfi kowa sani, wlhy ni ina ganin assirinku ne ya fara tonuwa tun yanzu, dan haka k'afa me naci ban baki ba.!" ganin ta kama hanyar guduwa ya sa su Ammie biyo bayanta a guje rigija-rigija kamar zautacci, ganin gudun kawai suke kwasa ba tare da sun san ta'inda zasu nufa ba, ya sa Hajiya Maryam tsayawa cikin shasshek'ar wahala ta soma cewa "Nifa na rasa gane hanyar da zamu bi ta fidda mu cikin wannan silisinin dajin.!" cikin wani matsanancin mugun tashin hankali Ammie ta nufe wajenda Khairat take, kai tsaye ta shiga jibgarta tana fad'in "Munahuka! dik laifin d'aibabbiyar Albarkarnan ne, dik ita taja muna wannan bak'ar wahalar, wallahi ni yau ko kashe ki nayi banida asara.!" ganin irin dukan da Ammie ke mata ba na wasa ba ne ya sa ta mik'ewa tsaye daga durk'ushen da take ta shiga famar gewayar fili tana fad'in "Allah dai ya isa tsakanina da ke Ammie.!" ita kuka Ammie kuka, Hajiya Maryam kam da haushinsu dik yabi ya isheta ta shiga yin tafiyarta ita kad'ai cikin rashin kwarin jiki tana k'ara tsinewa Ammie, tana cikin yin tafiyar ne taji k'afarta tayi tuntub'e da wani abu kamar dutse a saman hanyarta, nan take ta fad'i k'asa kwance kamar shara, cikin k'arfin hali ta yunk'ura zata mik'e zaune domin duba k'afarta idan ba tayi jini ba, maida kanta k'asa kad'ai ke da wuya ta ci karo da wata zundumemiyar k'afa wadda tsawonta da fad'inta kad'ai sun kai tsawon kilometer10, aiko bata san lokacinda ta sake wani irin firgitaccen ihu ba tare da ja da baya daga zaunen da take a wajen, cikin k'arfi hali ta tadda kanta sama da niyyar kallon fuskar wanda ke da wannan zundumemiyar k'afa sai dai ko kad'an bata iya hango fuskar ba, ganin tsawon wannan basamudiyar halittar ya wuce lissafinta ta sake buga wani rikitaccen ihu wanda sai da ya yi sanadiyyar dawo da hankalin su Ammie a wajen. A b'angarensu Abba kuwa, Alhaji Sulaiman ne wato mijin Hajiya Maryam, ya zo gidan misalin k'arfe 1am domin yaji ko lafiya rashin dawowar matarshi gida, cike da damuwa Abba ke gaya mashi cewa shi ma tun lokacin da aka gama wannan shari'ar a koto da ita har Ammie bai sake saka su a idonshi ba, sannan ya k'ara da cewa "Ita ma Khairat yanzu an nemeta an rasa kuma na kira mijin nata na tambaye shi ko tana wajenshi ya ce bata zo ba kuma ana ta kiran wayayuwansu sun kasa d'agawa.!" Alhaji Sulaiman ya ce "To Allah dai ya sa lafiya.!" Abba ya amsa mashi da "Ameen Alhaji Sulaiman.!" sannan suka yi sallama, Alhaji Sulaiman ya koma gida kamar yanda suka yi sallama da Abba...........
*Follow me on wattpad and vote Smart_Feenert*
*_#Be smart_*
*_Pls share_*

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now