*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**P...22*
Mummy ko kad'an bata ji alamun tsayuwar su a wajen ba domin ita kunci duniya da na lahira dik yabi ya addabe rayuwar ta
Yubra ce dake kwance a saman k'afafuwan Mummy taji alamun kamar wani abu ya fad'o a saman kan ta, cikin wani mugun firgici ta hira sama ba tare da ta shirya ba da niyyar kakkab'e koma menene wanda hakan ya maido hankalin Mummy a wajen ta da niyyar jin hujjar ta na son d'aga masu hankali da take son yi, nan take taga su Ammie tsaye a gefen su fuskokin su dik a kumbure kamar wad'anda suka sha kunun Mad'aci suna bin su da wani wawan kallon su mai cike da ruwan tsana had'i da bak'in bala'in tsiya.
Mummy ta d'an ji tsoro kad'an da ganin su domin ko kad'an bata ji alamun zuwan su anan ba nan dai tad'an kwakwalo murmushin k'arfin hali ta ce.
"Sannun ku da zuwa Hajiya Rafi'at ku ne anan dan Allah ku zauna mana kunyi tsaye sai kace bak'i.!"
Fuskarta d'auke da annurin farin ciki take masu maganar cikin tsakin fuska
Buɗar bakin Ammie kad'ai ke da wuya ta ce
"Ai wajen arziki ake zuwa a zauna ba wajen tsiya ba!"Mummy ta ce
"Subhanilillah! Hajiya! me ya kawo wannan maganar kuma?.!"Ammie ta ce
"Ko ma me ya kawo ta ai kinfi kowa sani, tunda kinfi kowa sanin mahaukacin d'anki da kika ajiye a gida!."
Cikin fuskar rashin fahimtar inda yaren nata ya dosa Mummy ta ce
"Banfa gane inda zacen naki ya dosa ba Hajiya Rafi'at!."Ammie ta ce
"Hmm ban yi mamaki ba ai tunda so da yawa kike aikata abu kuma ki nuna kamar ba ke ba ce, ai dik wani abin da yaran ki keyi kina sane kuma kina ji kina kallo amma bakya iya tsawatar ma su dan haka da akai ga kashe man d'iya wadda ita kad'ai ce Allah ya azurta ni da ita har ake man bak'in ciki to gwanda an cinma matsaya tun daganan dan wlhy bazan d'auki aikin ganganci ba, haka kawai dan anga muna kyalewa akan dik wasu abubuwan da ake yi mata a gidan dan bama magana shine harda wani wulak'antaccen duka! To wlhy bazan d'auka ba ko kad'an kuma ba zan lamunta ba.!"Murmushi mai cike da hayak'in k'unar zuciya Mummy tayi kafin ta soma tambayar abin da ke faruwa cikin muryar lalama tare da ban hak'uri.
Ammie ta ce "Ai ni a tunani na kinfi kowa sanin abin da ya faru har d'anki yakai ga yi ma d'iyata bugun mutuwa, shin wai sai me ma dan sun zuba mata ruwan zafin ta mutu wa ya damu da hakan wadda ma ba d'iyar Cikin ki ba ce da har zaki wani takurar da kanki akan ta, Sai dai kuma ina son ku sani tun wuri wlhy maganar Auren Khairat da Abir babu ta dan tabi iska ta wuce dan ba zamu tab'a gangacin had'ata da mahaukaci a gida guda ba ya kashe ta a banza ya kai mu ya baro ba dan ni dama ba son auren nake yi ba.!"
Mummy kam hankalin ta ya kai mak'ura wajen tashi da jin wannan maganar da Ammie tayi da ta ce "sai me dan sun zuba mata ruwan zafin ta mutu!. wanda hakan ya yi nasarar jefa ta a can k'ololuwa wajen yin tunanin abin da ta kasa gasgatawa, ta ce "ke nan daman Khairat ce sanadin wannan halin da Fatima take ciki dik wannan kame-kamen da take yi d'azu kenan daman ta san komai amm......
Tana cikin yin wannan tunanin ne wata Nurse ta katse mata hanzari wajen cewa "Doctor yana neman ta yanzu.!"
Haka ta tashi tabar wajen ba tare da ta ce ma su ko k'ala ba, Ita ma Yubra baya ta rufa mata suka bar wajen rai a jagule
Da harara su Ammie suka bi su da kallo har suka b'acewa ganin su, a sannan Aunty Khairat cikin k'unk'unin shagwab'a ta ce"Haba Ammie ya zaki ce a fasa Auren! Ni gaskiya Ya Abir nake so."
Sake da walgalallen baki Ammie ke bin ta da kallo kafin ta soma cewa "Kunga Shahaha! Iyyeeeee, ke ko kad'an ba zaki iya yi ma kanki yak'i ba wajen kwatar 'yancin kanki, kenan ko auren aka yi haka zaki yi sake da baki kina kallon shi yana zaluntar ki a banza! Hmmm Nima ai ko kad'an ba so nake a fasa wannan auren ba dan idan na ce maki na ma fiki son ayi auren ba zaki yi mamaki ba domin a sannan ne nake tunanin wasar zata fara aiki tsanin mu da su domin dik abin da suka dad'e suna yi mana tun bama da kud'i su kuma suna da har i zuwa yanzu da kowa yake da nashi wlhy dik sai sun fanshe.!"
Khairat ta ce "Wlhy ina goyon bayan ki d'ari bisa d'ari Ammie ta.!"
Ammie ta ce "to shikenan muje muga Doctor yanzu sai mu koma gida ayi dik wadda za ayi.!"___________Wace ce Ammie?
Ammie asalin ta 'yar k'auyen BUNZA local government ce dake cikin garin Birnin Kebbi state wanda a cikin garin su ne tayi Primary Skull sannan ta dawo Kalgo Local Government tayi Secondary Skull d'in ta anan har zuwa Senior Level
Ammie ba kowa ba ce face d'iyar wani k'asungumin talaka wanda halin talaucin ne ya yi sanadiyyar mutuwar shi da matar shi wad'anda 'yan fashi ne suka kawo masu farmaki akan su bada dik wata kadara da gare su dan su fanshe rayuwar su da ita, tun da Malam Abdul ya bud'e bakin shi ya ce baya da su kai tsaye ba su sake bin ta kan shi ba suka juya wajen matar shi Abuu sai dai sun mata gargad'i akan basa son jin kalmar babu dan tana saurin harzuk'ar da su Idan suka ji ta, Jin tayi shiru ta kasa ba su amsa nan take babban su ya saka bindiga ya halbe su gabadai suka wulla k'iyama.
Safiya na wayewa Ko da Rafi'at ta dawo gida, dan lokacin ba a gida ta kwana ba ta kwana ne a gidan da take aikatau kasancewar gidan suna hidimar bikin d'iyar su macce da zasu wanke ga goben, tana shigowa gidan ta cinma gawawwakin iyayen ta zube kamar kayan wanki a cikin filin gidan kwakkance a yashe.Bayan wasu kwanaki gidan da take zuwa wajen aikatau d'ai daga cikin d'iyan gidan ya neme ta da lalata akan tak'i amincewa ya sa iyayen shi suka kore ta daga gidan da sunan ta k'allafawa yaron su shairi
Bayan tabar gidan ta koma kamar abin tausayi babu mai taimakon ta sai Allah sai kuma ita idan ta d'anyi wanki an biya ta, nan dai ta yanke shawara zuwa Birnin Kebbi domin neman na kan ta, anan Rafin-Atiku ta samu wata mata mai tuwo-tuwo ta fara aiki a wajen ta daganan suka had'u da JABIRU wato Abba, cikin d'an k'ank'anen lokaci aka yi komai aka gama sosai Hajiya Rabi mai tuwo-tuwo ta zame mata tamkar uwar da ta haife ta, basu dad'e da yin auren ba Allah ya yi ma Hajiya Rabi mai tuwo-tuwo rasuwa wanda halin tashin hankali ba irin wanda Ammie bata shiga ba, a bangaren 'yan uwan JABIRU kuwa soyayya ba irin wadda basa nuna mata dik da shi ma Mahaifiya kad'ai gare shi sai k'anen shi guda da ya rage mashi wanda shi ma ya kusa kammala karatun shi na Degree wanda yana gamawa shima burin shi dik bai wuce auren ba.........
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*#Be smart*
*^Pls shere^**_More Comments_*
*_More Typing_*
YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...