P...9

552 61 2
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

              *P...9*

_Jiki ba kwari nabar gidan gabaɗai na tunkare majalisarmu, sai dai ban cinma kowa a nan ba sai Aisha Mai yamin baki, da Balkisu Maicin Tansoni (Hantoni) shine laƙanin da nayi masu._

                 _Suna ganina suka dauke shewa, suna fadin "Yau wacce rana Fatima anyi wan.........  basu kai ga karasa zancen ba  suka kama bakinsu suka yi mui ba tare da sun karasa ba._

            _Cike da shan kamshi Na Iso daf da su sannan na turmike fuskar nan  tare da tambayar su abinda suke kokarin fadi, Amma fir suka turje idanu sukaƙi faɗi akan tsoro, karshe da suka ga alamun so nake naci kaniyarsu kamar yanda na saba, suka kwashe na kwasa ko waccen su ta arce._

....

_Bangaren su Mummy Balkisu kuwa, sun gama tsara komai ita da Kaka kamar yanda ya kamata, jiran wayewar safiya kadai suke yi,  Mu tayas._

             ~~~

_Washe gari, Da sassafe su Mummy Balkisu suka tashi suka shiga  Kakkance-Jakkacen kayan su, tare da bawa kowa tsarabar da suka kawo mashi,_

.....

             _Komawa ta cikin bedroom  kadai keda wuya, naci karo da Kaka ta tattalo bakko ta, ta tufafi tana kokarin fito da ita waje.   Cikin tashin hankalin fadawa cikin ramen kunya, na ce "Yanzu Kaka ina zakije man da tufafi?._

    _"Waje zanje da wandannan raggadudan, afidda na dauka, a yada matattu" ta karkare maganar ta ta kai tsaye tare da nufar hanyar fita daga cikin bedroom din._

            _Cikin wani shagwababben kuka na ce, "Yadawa fa kika ce?, Ni wallahi abar man kayana haka nan ina son abina, yanzu  sai kisa su Yumra su raina ni._

       _Ba tare da ta tsaya sauraren shirme na ba, ta rantame Gana mazgo din ta fito da ita waje._

                _Cike da mugun jin haushi wannan abin, na ida shigewa cikin bedroom din, tare da tunanin irin fuskar da zan fito waje da ita, domin nasan kayan nawa dasu da raggadudan basu da wani banbanci domin da gangan nake saka reza nayi ta yagarsu, sannan idan Kaka tayi man wanki da gangan nake shiga rere dasu inyi ta tunburbuda a ciki, kuma dik yanda take matsaman da nayi wanka sai naki yi karshema idan ta ce zata man da kanta  to a wannan ranar da kokowa nake baro bathroom din kamar ƴar'dambe, karshema na fita Garka Zigidir ina sharbar kukan rashin son yin wankan._

       _Ina cikin yin wannan tunanin ne, naji sautin Fitar dariyar su Yubra a waje har da ta Mummy Balkisu daga bisani naji ta Kaka na tashi, Itama Gwaggo Talatuwa daukar ta ta tayi._
                  _Da karfi suke dauka tare da ajewa tare, kamar cikakkansu su fashe ɗiyan Emoji su fito, sai a sannan na ankaro da ashe dik aka fiddo zane guda daga cikin bakkon tawa sai su  kwashe da dariya, ta sanadiyyar yagar da su kaga andarje anwa tufafin,  a cikin kuwa har da tufafin da nake rabawa biyu nama diyar roba ('Yar tsana) ta dinki._
               
             _Kai tsaye Kaka ta dago wata riga sama, wadda gabadai na yanke hannayen rigar, nawa 'Yar tsana ta Sket, ta ce "Yanzu ku duba ku gani wadannan tufafin fa dik sababbi ne amma a dubi yanda dik  nabi na lalata su da raiza, Cikin dariya irin tasu ta Manyan Mata (Masu abin atata😂) ta ce "Mama kawai abar kayan  ba sai anje da su ba, idan  muka isa gidan zata dinga amfani dana su Yubra kafin a dunka mata nata". ai ko ina jin wannan batun nayi buzut na fito waje Ina fadin "Wai maganar me ake yi, wlhy ni ba inda zanje."  nan da nan naji na fashe da wani dan ballajja'un kuka tare da maimaita wannan kalmar ta, " ba inda zanje"._

        _Nan Mummy Balkisu Ta shiga Lallabata har ta samu nayi shiru tare da taimakon su Yumra, ta hanyar kwantarman da hankali tare da ambaton sunayen Kaji da kuma Makaranta da za'a saka ni kullum ana cikaman kula da Indomie, Nima na zama 'Yar bariki, kamar yanda na taba cema Kaka"._

         _Ai ko bansan lokacin da na washe baki ba ina kwasar dariyar jin dadi tare da farin cikin faruwar wannan Al'amarin, dan ni har na manta da batun wata matsalar da nake kokarin hangowa a gidan, dangane da su Ya Abir._

              _Kaka kuwa ta rasa abinda ke mata dadi a cikin duniyar nan, domin daidai da minti guda bata son tayi ba tare da ni ba,  kuma tana matukar tausayina musamamman idan ta tuno da iyayena wanda yanzu abin har ya zame mata jiki, nan take ta mike tsaye ta nufe cikin daki, Mummy Balkisu da ta gama fahimtar hakan, ta rufa mata baya cikin rashin kwarin jiki, domin tasan dik yanda Kaka taso ta dake abin acikin zuciyar ta wani sa'in  sai ya bayyana dik yanda taso boye kuwa._

              _Ni kuma gabana gadi, sai famar shirye-shiryena nake yi  ni da su Yumra, har na matsu 12pm ba tayi ba Daddy da Ya Fadil su zo mu tayas, Sabida su a gidan su dake Unguwar GRA suka zauna,  dan tun lokacin da suka gaisa da Kaka suka wuce can._

            _Sun yi niyyar  subi Jirgi, amma ta sanadiyyar banada Passport bana da komai yasa zamu je a Mota_

~~~

  _Ko da 12pm tayi dik mun gama komai, ko 5mins ba'a kara ba sai ga Direbobin gidansu sun iso har sun parka motocin su gefe a bakin garkar mu (waje) Mutanen Unguwa kuwa sai zuwa ake ana bankwana da Mummy Balkisu sabida kwadayin abinda take raba masu idan tazo da kuma idan zata koma._
                _Abokanai na kuwa sai famar kukan rabuwa suke da ni dik da irin azabar da nake gallaza masu._

.....

                 _Har muka fito waje Kaka bata biyo mu ba, ta shigewarta cikin daki tana kukan rabuwa da ni, Dik da Mummy Balkisu ta yi mata Alkawarin zata dinga kawoni akai-akai tana gani na, dan ba yadda bata yi da ita ba tun kwanakin baya akan ta dawo wajen ta da zama harda Daddy ya saka bakin shi a cikin al'amarin da su Ya Abir amma ta nuna masu tafison nan inda take._

....

        _Gwaggo Tatatuwa kadai tayi mana rakkiya har wajen da a kayi parking din Motocin, sai da taga mun shige cikin  motocin har mun dauki hanya sannan ta dawo cikin gidan tare da yi mana baibai (babayi) ._

        .....

_Tun tafiya ba tayi nisa ba, na fara Angaje a saman jikin su Yumra, Ta sanadiyyar sanyin AC'n dake dukan sassan jiki na, da kyau, domin Mota guda muka shiga Ni da Su da kuma Ya Fadil, dik da shi yana gaban Motar, Ita kuma Mummy Ta shiga Motar da Daddy yake ciki,  sauran Motocin kuma dik Emty suke, direbobin dake tukasu kadai ne ke ciki._
*Follow me on wattpad and vote— Smart_Feenert*
                *Be smart*
                     *^pls shere*

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now