P...24

469 48 2
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

             *P...24*

            Dik wani gyaran da ya kamata ayi ma Khairat anyi mata an saka bandeji a inda yake kwakkwald'e an manne da kaɗa
           Bayan an gama ne Ammie ta ja ta suka dawo wajen da su kayi parking d'in motar su, har sun bud'e zasu shiga suka hango motar su Ya Abir dake k'ok'arin shigowa cikin Asibitin
                   Nan da nan suka canza shawarar shiga cikin motar suka yi tsaye cak a wajen da suke suna jiran ganin su Ya Abir sun ida shigowa ciki tukunna kafin su kai ga kai masu farmakin cin mutumci

             Ko da suka gyara parkin d'in motar su suka fito waje tare da k'ok'arin shiga cikin Asibitin
             Nan hankalin su ya juya izuwa wajen Ammie dake k'ok'arin tunkaro wajen da suke hunga-hunga kamar wadda aka koro daga gidan giya
           Ba tare da ta tsaya gaida ko Daddy ba ta shiga zazzaga masu ruwan bala'i, ta inda take shiga ba tanan take fita ba
                  Ba wanda ya tadda kai ko ya kalle ta a cikin su inbanda Daddy  dake ta k'ok'arin bata hak'uri dan yaga alamun kamar bata cikin hayyacin ta sai dai tak'i kwantar da hankalin ta balle tayi hank'urin wanda hakan ya sa Daddy kai tsaye ba tare da ya sake cewa da ita ko uffan ba ya yi shigewar shi cikin Asibitin sabida gudun karta tara masu jama'a a wannan wajen, ta sa da girman shi a dinga kallon shi kamar k'aramin yaro
               Su ma su Ya Abir baya suka rufa mashi suka barta tsaye rik'e da k'ugu tana balbalin bala'i
                 Khairat dake tsaye a wajen da suka yi parking d'in motar su tana kallon mahaifiyar ta cikin burgewa sabida bala'i da take yiwa su Daddy, nan dai ta tako wajen da take cikin rashin kwarin jiki taja ta suka yi wajen motar su dan taga alamun mutunen da ke wajen sai wani kallo suke biyar su da shi na k'asa da sama suna zubdawa a cikin kwandon shara

       Bayan su Daddy sun iso cikin d'akin da nake  Yumra ta fara tarbar su da cewa "Ya Ashe Aunty Khairat ce ta zuba ma Fatima ruwan zafi a jiki! Yanzu suka zo suka gama zagin Mummy wai Ya Abir ya dak...............!" Tsawar da taji Mummy ta daka mata ne ya tsaida ta wajen ci gaba da yin zancen da take, Inda taji tana ce mata
           "Wa ya tambaye ki Aku sarkin magana?.!"
           Ya Bikhram ne dake zaune a saman d'ayar kujerar dake cikin d'akin kusa da su ya ce "Ai ba ita kad'ai ba ce! Harda wannan babbar banzar.!"
            Yana mai nuna masu Aunty Intisar dake tsaye a bakin kofar d'akin a makure kamar wata saliha
                 Cikin mamaki Mummy ta ce "Intisar! Intisar!!"
                A d'an tsora ce ta d'ago fuskar ta dake sussudule ta kalle Mummy cikin fuskar mai ban hak'uri ba tare da ta ce ko k'ala ba
            Shi kam Daddy cewa kawai ya yi "Allah ya sauk'ak'a.!"
             Yana gama fad'in hakan ya mik'e tsaye su ma su Ya Bikhram suka rufa mashi baya gabad'ayan su suka bar d'akin, aka bar daga Mummy sai su Yumra tare da Malama Aunty Intisar dake tsaye tun d'azu a wajen da take ta kasa k'arasowa ciki
            Mummy ta ce  mata "Shigo ciki, kuma ki rufe mana d'aki tunda ba rabon Awaki ne muke yi ba.!"
             Cikin rashin kwarin jiki ta kulle k'ofar sannan ta dawo wani wajen na daban daga cikin d'akin ta zauna tana kallon Mummy dake jifan ta da wani wawan kallo
                Cikin muryar damuwa ta ce "Dan Allah Mummy kiyi hak'uri wlhy shairin shed'an ne.!"
           Mummy ta ce "Ba hak'urin ki nake buk'ata ba dan haka ki rik'e abin ki.!"
             Aunty Intisar dai bata ce ko uffan ba
         Mummy ta ce  "Ke yanzu dan baki da hankali kuma ba ki da tunani harda ke za'a iya had'a baki a kuntatawa K'anwar ki dan rashin Imani da rashin tausayi?.!"
               Aunty Intisar zata bud'e baki tayi magana Mummy ta dakatar da ita da cewa "Ke dai kinji haushi wlhy kuma kin ji kunya babbar banza kawai.....!"
      Fad'a dai sosai ta mata tare da yi mata wani zazzafan warning akan Fatima wanda har sai da yasa Aunty Intisar fashewa da kuka sannan Mummy ta k'ara da ce mata "ta tashi ta basu waje kuma karta sake ganin k'afafuwan ta a cikin Asibitinnan da sunan ta zo wajen su.

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now