P...40

286 49 4
                                    

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

    *'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
       *—•«•BE-SMART•»•—*

*_{🌸EMAIL- smartfeenert@yahoo.com🌸}_*

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*_🌴BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🌴_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

              P...40
Murmushi mai cike da k'unar zuciya Khairat ta yi kafin ta ce "Abba Fatima bata san komai akan mutuwarsu Mummy Balkisu ba hasali ma shairi aka mata.!" shiru wajen ya yi ita kad'ai ake saurare inda Ammie da Hajiya Maryam suka yi muzu-muzu da ido suna sauraren abin kamar bak'on abu a wajensu, sannan Khairat ta kwashe dik yanda aka yi ta sanar da kowa da ke wajen, salati kowa ya saka inda su Ya Abir da sauran mutanen da ke wajen banda hawaye ba abinda suke yi, sannan Khairat ta k'ara da cewa "Bayan mun koma wajen Boka mun sanar da shi abinda ke wakana ya bamu wani kullin magani da laya....!" Dik ta gaya masu yanda aka yi da su tare da yanda aka gudanar da shari'ar cikin zalumci da kuma yanda aka turbud'e Fatima a cikin rame da dawowar da suka yi basu ganta a ciki ba har wajen Bokan da suka koma inda anan ne ta san asalin wacece ita da kuma irin had'arukan da suka dinga shiga, dikkan mutanen dake wajen kuka suka saka harda Abba da ya yi zaune ya d'ank'are kuka kamar ranshi zai fita idan ya tuna da irin tulin cin amanar da Ammie ta mashi da kuma abinda tayi ma d'an wanshi da kuma ni, haka ma Ya Abir da su Ya Fadil tare da su Yumra harda ni ma a ciki tare da Aunty Intisar da ke cewa "wlhy ni ma na cuceki Fatima, na cuce rayuwarki kuma dik ta sanadiyyar son zuciya da kuma biyewa rud'in shaidan, tabbas ba makawa ni na taimaka aka jefaki cikin kitchen har kika fad'a cikin ruwan zafi tafasasshi wad'anda ni da kaina na aza su a wuta tare da taimakon Aunty Khairat, sannan ba wannan ne kad'ai abinda muka maki ba, bayan wannan ma harda fyad'e na bada tawa gundummawar da ayi maki........!" Ta kwashe dik yanda suka tsara tun farko ta fad'a, kowa dake wajen ya girgiza da jin wannan al amarin tare da Allah-wadai da hali irin na su Ammie. Hajiya Maryam ce ta zube a gaban Alhaji Sulaiman tana rok'onshi gafara ga dik abin da ta mashi inda take cewa "Wlhy dik matsalar dake tsakaninka da iyayenka da 'yan-uwanka dik ni ce sila, ni ce silar korar iyayenka da kayi daga gidanka a cikin wannan daren misalin k'arfe 2:00am wanda har suka yi had'arin mota cikin wannan daren suka mutu wlhy dik ni ce silar faruwar dik wasu abubuwan dake wakana dangane da matsalar harkar karuwancin da k'annenka biyu mata suka fad'a har cutar k'anjamau tayi sanadiyyar mutuwarsu, kuma dik ni ce sanadiyyar haddasa wannan gagarumar k'iyayyar dake tsakaninka da su ta sanadiyyar maganar da Doctor Hashim ya gaya man ta rashin haihuwar da bana yi wanda hakan ya sa na shiga malamai dan ganin na raba ka da kowa naka sabida ganin nake idan suka ji wannan matsalar da nake fama da ita ta rashin haihuwa zasu shiga tsakaninmu ne su raba mu! dan Allah mijina ka gafarta m........!" a tsawace ya dakatar da ita cikin d'aga murya ya ce "Kul! kar bakinki ya soma furta ban hak'uri a gareni, macuciya bak'ar azzaluma, makira, wlhy ko na k'yaleki anan ina da tabbacin hakkin wad'anda kika zalunta ba zai barki ki zauna lafiya ba amma ki je ke da Allah shi kad'ai ne zai iya yi maki hukunci dai-dai da abinda kika aikata a garesu sannan tsakanina da ke sai dai na ce, Allah ya isa, kuma ki saka a ranki dik wata alak'ar dake tsakanina da ke da ga yau ta k'are domin ko a mafalki ba na tunanin zan sake zama da azzalumar mata macuciya kuma marar imani, marar tausayin irinki ba, dan haka kafin kiyi tunanin k'ara yunk'urin sake shiga wata duniyar ki ida halakani ki sake cutar wasu! to gwanda na sauk'ak'e maki kije can ki k'arata da wad'anda suka kama maki har ki ka samu damar cutar da wad'anda basu rageki da komai ba a rayuwa, dan haka ina son kowa dake wannan wajen ya shaida cewa Ni Sulaiman Muhammad Abubakar, na....!" Malam ne tare da jamar dake wajen suka shiga k'ok'arin dakatar da shi daga abinda yake k'ok'arin fad'i amma inaaa baki ya riga ya furta inda ya ce "Na sake Maryam Malam Ibrahim, saki ukku sakin da bana fatan ya sake gyaruwa ko ba anan ba.!" wani razanannen ihu ne Hajiya Maryam ta saki tare da fad'uwa k'asa kwance tana birgima, Ammie ma kuka ta fashe da shi dan ta san ita ma nata na nan zuwa, kamar ko ta san abinda Abba ke tunani kenan,  kai tsaye ita ma ya jefo mata na ta inda ya ce shi ma ya sake Ammie saki ukku ta je ta bi k'awarta wadda ta d'auka a matsayin abu a gareta, shi ya yafe mata ita duniya da lahira, ita ma bori ta tashi tana yi inda DPO ya kira yaranshi gabad'ai suka saka masu handcuffs harda Khairat dake gefe tana rusa kuka sannan aka fita da su waje gabad'ai. Aunty Intisar ce ta taso daga wajen da take ta rumgume Fatima suka shiga zuba kuka hinhinhin tana fad'in "Fatima ki yafe man dan Allah wlhy nayi nadamar abinda na aikata maki, wlhy ina cike da jin kunyarki ga dik wani abinda nayi maki dan Allah ki yafe man Fatima ki gafarta man ko zan samu sauk'i a cikin zuciyata.!" su ma su Yumra tasowa suka yi dukansu suka rumgumeni suka shiga zuba kuka kamar yanda mu ma muke yi babu mai lallashin wani a cikinmu sai da muka yi mai isarmu sannan muka yi shiru ko wannenmu yana fitar da shashshek'ar kukanshi a fili, haka ma dik wanda ke wajen shi ma hawaye ne ke fita a idonshi, Ya Fadil ne ya soma magana cikin muryar wanda ya dank'are wani likkimin kuka ya ce "Wlhy harga Allah ni ko kad'an ban tab'a yarda da Fatima ce ta kashe muna iyaye ba.........!" daganan kuma wani sabon kukan ya k'ara kubce mashi inda Ya Abir ya shiga lallashinshi inda shima yake  fad'in "Ni ma wani lokacin idan ina zaune sai na dinga tunanin ta ya ma Fatima zata iya kashe iyayenmu harda kuma Hajiya, wlhy wani lokacin idan ina zaune haka nake tunani amma na kasa gazgata hakan a zuciyata.!" maganar yake amma ni ko kad'an ba shi ne gabana ba dik da idan muka had'a ido biyu da shi ina jin wani kwarjininshi na tasoman a zuciya wanda hakan ke sa na yi hanzarin d'auke idanuwana daga na shi, cikin raina na ce "Kenan shi ya fi k'arfin ya bani hak'uri!." nan dai na kawar da wannan zancen a cikin raina na ce "Mai ma zanyi da wani hak'uri nashi, ya rik'e abinshi dama ni ba so nake ba.!" Ido hud'un da muka yi da Mummy Zulfa ya sa ni jin wata 'yar kunya kad'an dan ina ganin kamar ta ji abinda nake tattaunawa da zuciyata, murmushin da tayi man ne ya saka ni jin wata 'yar kunyarta na d'an gincira kaina saman kafad'arta, Papa ne ya d'anyi gyaran murya kad'an cikin burgewa inda hankalin kowa dake wajen ya dawo kanshi, a hankali ya shiga kora masu bayanin ko shi wane ne a wajena, idan na cire maku ni da Malam cikinsu Abba ba wanda bai girgiza da wannan al-amarin ba sai dai ko ba a baka labari ba idan ka kalleni ka kalle Papa kasan abu guda ne, sai da komai ya d'an lafa sannan Papa ya yi sallama da su Malam akan mu zamu wuce, cikin damuwa su Aunty Intisar suka shiga rok'ona akan na zauna tare da su, Mummy Zulfa ce tayi hanzarin dakatar da su da cewa "Su yi hak'uri, In sha Allah bada jimawa ba zasu sake ganina.!" haka dai muka rabu cikin kewar juna, su Abba suka rakomu har waje tare da su Ya Abir wanda tunda muka fito yake son mu had'a ido cike da damuwa amma ni ko kad'an nak'i bashi had'in kai, anan waje muka samu DPO tsaye yana waya inda yana ganin su Papa sun fito ya yanke kiran ya k'araso wajen da yake tsaye da su Malam!. ina cikin tafiyata ina sharar kwalla ta kewar 'yan uwana da nake yi, dan su Yumra suna rakomu waje suka koma cikin gida a hanzarce suna kuka, jin kawai nayi an danko man hannu da k'arfi, a tsorace na juya ta bayana dan ganin wanda ya rik'e man hannun, Ya Abir ne tsaye ya wani turmuk'e man fuska ba yabo ba fallasa kamar ba abinda ke mashi dad'i, k'ok'arin kwace kaina na shiga yi tare da yunk'urin sakar mashi kuka dan naga hankali kowa ya tafi izuwa wani gun, k'asa-k'asa ya yi da murya yana ce man "Mu je ina son magana da ke kuma karki man kuka wlhy.!" Mummy Zulfa ce ta juyo muka had'a ido biyu tare da ita ba tare da shi Ya Abir ya lura ba, murmurshi ta sakar man tare da game d'an yatsanta na hannu babba da manuni ta murzasu waje guda, tuni muka tsintsi kanmu a wani keb'ab'b'en waje ni da shi...........!
FOLLOW ME ON WATTPAD AND VOTE—Smart_Feenert
#Be smart
Pls share

'YAR BALLAJJA'UWhere stories live. Discover now