P...28

497 61 13
                                        

*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*'YAR BALLAJJA'U👩🏻‍🎤*

*—•«Start, on 23/2/2020»•—*

*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—*

*_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—*

         *Allah ya yi ma d'ai daga cikin Kakanni na rasuwa Ina rok'on Ubangiji Allah ya haskaka k'abarinshi yasa mutuwa ta zamo hutu ce a gare shi Allah ya karb'e bakuncinshi Ya jik'anshi da rahamarshi Ameen ya rabbi 😭😭😭😭👏🏻*
      *Allah ya jik'an musulmi Ya kyautata ta mu idan ta zo Ameen Ya hayyu Ya k'ayyumu😭😭😭😭😭.*

      *P...28*
         Kaka ce da ke k'ok'arin maka masukkanta a saman d'ayar kujerar dake cikin jerin kujerun alfalmar dake cikin d'akin, ta ce "Niko nace  Hajiya Rafi'at  ba kwa gajiya ne da zuwa gidannan ne halan? Naga kusan kullum kuna kan hanya, amman kam bada sanin Jabiru kuke zuwa nan ba ko?."  a kunya ce Ammie ta dubi Mummy dake k'ok'arin bud'e k'asa ta shige akan kunya sannan ta maida dubanta ga Kaka dake kallonta tun d'azu tana jiran Jin amsar da za'a bata, cikin mugun jin haushin wannan tambayar ta soke kanta k'asa sannan ta taddo shi sama ta kalle ta cikin nuna halin rashin damuwa ta ce "Ai ba komai wlhy Hajiya, shi ma ya ce mu dinga zuwa muna gaisawa sabida zumunci.!"  Kaka ta ce "Eh lallai kam zumunci! amma wai k'afafuwanku basa ciwo.?!"  Sai da Ammie ta kalle Khairat da ita ma tun d'azu ita take kallo sannan tayi murmushin k'arfin hali na son bid'ar share zancen wanda hakan bai ma Kaka dad'i ba ko kad'an  zata sake bud'e baki ta k'ara cewa wani abu Mummy tayi hanzarin tare ta da cewa "Hajiya kinga goron da Sani direba ya kawo maki kuwa?.!" Cike da mugun jin haushin katse mata hanzarin wajen ci gaba da tambayoyin da take k'ok'arin yi wa Ammie kamar wata 'yar jarida  tayi zubun ta mik'e tsaye a hasale ba tare da ta bata amsa ba hunga-hunga tayi d'akinta, da kallo dikkansu suka bita cikin mamakin irin wannan halin na rashin mutumci da Kaka take tak'ama da shi, Ammie kam da ikon Allah dik ya cika mata ido ta ce "Iyyee! Yau ni naga ikon Allah kuji man wannan komud'ad'd'iyar tsohuwar ita bata ga nata abin kunyar ba sai dai na wani, ta dawo gidan suruki tayi nashe-nashe har tana da bakin yi ma wasu magana dan rashin kamun ka..........!" Maganar Mummy ce da taji ta katse mata hanzarin wajen ci gaba da zancen zucin da take wanda hakan yasa ta saki wata nannauyar ajiyar zuciya tare da hamdala ga Ubangiji da yasa maganar bata fito fili ba tukunna, Mummy ta ce "Bara na je na kawo maku abin sha Hajiya! sai dai dan Allah kuyi hak'uri kin san halin tsufa yanda yake.!" Ammie ta ce "ai babu komai wlhy da ma kin bar ruwan dan daman wucewa ne za muyi kuma munga mun biyo ta wajenku ne shi ya sa na ce bara mu biyo mu k'ara ganinku.!" Tana gama fad'in hakan ta mik'e tsaya tare da Khairat suna batun wucewa Mummy da kanta dik ya zama wani K'ato akan kunya dan ta san maganar da Kaka tayi masu ce ta b'ata ma su rai, ta ce "Haba Hajiya ai da kun tsaya ko ruwa ne kusha tukunna kafin ku wuce.!" Ammie ta ce "Ba komai fa! Ki barshi kawai wlhy mun gode.!" Tana gama fad'in hakan suka bar Palour'n da hanzari  rai dik a b'ace. bayan sun isa wajen da suka yi Parking suka shiga cikin motar Khairat ta zauna seat d'in driver Ammie kuma ta zauna kujerar gaba (Front seat) Ba tare da Khairat ta tada motar ba ta ce "Ammie inaga wannan tsohuwar fa ya kamata mu fara yin maganinta tun wuri dan naga alamun rawar Kanta ya yi yawa.!" sai da Ammie tad'an sake murmushi k'arfin hali sannan ta ce "Ki barni da shegiya kawai! dani take zancen! tada mota mu tafi.!"  Direct wajen Boka suka nufa inda suka bashi dik wasu bayanan da suke ganin makami ne a gare su sannan shi ma ya kara saita su a hanya tare da cewa "su zuba mashi ido ko ma mene ne zasu gani nan bada jimawa ba." Haka dai suka koma gida zuciya k'al da farin ciki.  bayan sati guda ranar Assabar muka fara zana Waec Kuma Alhmdu lillah an samu ci gaba sosai a exams d'in har muka kai matakin k'arshen gama waec d'in watanmu guda muka fara Neco kamar yanda muka fara lafiya haka Allah ya gwada muna karshenta lafiya inda sakamako kad'ai muke zaman jiran ganin fitowarshi kuma muna saka ran shi ma za muga alkhairi a gare shi. a wata ranar juma'a ce muka tashi tunda safe muna shirya-shiryen dawowar su Ya Abir daga wajen karatu dan su ma dik sun ida k'ark'arewa inda gabadai suka hallara a U.K. wajen da Ya Abir yake da niyyar  dawo Nigeria tare harda Ya Fadil. Ammie ce durk'ushe ita da Khairat a gaban wata kwarya dake kusa da Boka inda yake mik'awa Khairat wani kullin magani a cikin wata takarda inda ya bata umarnin ta runtse idanuwanta ta kira sunan Ya Abir sau ukku sannan ta d'ibi wannan maganin a bayan Faratan hannunta na haggu ta zuba a cikin bak'ak'en ruwan dake cikin wannan kwaryar, bayan tayi kamar yanda ya ce nan take wani hayak'i ya turmuk'e wajen cikin wani mugun mamaki mai cike da ban al-ajabi ya dubeta ya ce ta sake yin yanda tayi d'azun ba tare da wani b'ata lokaci ba ta sake yin hakan kuma against wannan hayak'in ya k'ara tashi a wajen, nan hankalin Boka ya d'an tashi kad'an wanda su ma su Ammie'n sun ji nasu ya d'an tashi ganin halin da Bokansu yake ciki, kai tsaye ya ce masu "Lallai wannan babban abu ne dan ya wuce dik inda nake tsammaninshi! amma ba komai zanyi maganin abin, ku ajiye tukwicin kuje sai na neme ku.!" Cikin damuwa Ammie ta ce "A kwai wata matsala ce Boka?.!" Ya ce mata "Eh gaskiya a kwai sai dai ba wata babba ba ce wadda zata iya gagara ta wajen shawo kanta, a kwai wani D'an K'arunan aljani dake son hana ni yin aikin amma na tura D'an-duk'usulu yaje ya tafo man da shi zanyi maganin k'aramin d'an iskan ai, kuje bayan ya dawo idan an saka ranar Auren  daren biki sai ku zo ku same ni dan yana dawowa ba za'a wani b'ata lokaci ba za'ayi maganar auren kuma lokaci d'an k'ank'ane za'a saka ma auren.!" Murna kam a wajen su Ammie ba'a cewa komai kamar su hira sama su fad'oma Allah, haka dai suka tashi ransu fess da farin ciki tare da hucin d'aukar fansa idan komai ya kammala. K'arfe2 tayi ma su Ammie a gidan dik da tun lokacin da Kaka tayi masu wannan maganar suka d'auke k'afafuwansu da zuwa gidan. Kaka kam ko ta kansu bata tsaya bi ba sai famar sintiri take bata nan bata can d'auko wannan ajiye wancen haka aka dinga ta yi har dai aka gaji aka koma d'aki aka sake wani wankan sannan ta dawo palour  ta zauna tare sauke gajiyar aikin da suka darza, Su dai su Ammie kamar wasu bak'i haka suka koma sai kalle-kallen mutane suke sun kasa sakin jiki da su harda Intisar d'in wanda dik yana d'ai daga cikin tsarinsu sabida gudun sa'idon da Kaka ke ta famar yi masu. bayan kowa ya yi wanka ya shirya harda su Ammie su ma suka sake yin wani wankan inda kowa ya fito d'agwas da shi abin gwanin burgewa da ka kalle kalar wankan kai kanka kasan talaka bai isa ya yi irinshi ba dan tsayawa ma fad'in irin had'uwar da suka yi b'ata lokacin mai k'aratu ne. misalin 6:00pm jirginsu Ya Abir ya sauka sai dai wannan lokacin daga Abba sai Daddy suka je airport suka d'auko su, bayan sun iso gidan kuwa aka zunduma cikin shagulgulan murnar dawowarsu abin dai gwanin burgewa, sai wajajen 8:30pm su Ammie suka koma gida dan wannan karon Khairat ba anan ta zauna ba. Daddy ne da Abba tare da Ya Abir da Ya Bikhram da kuma Mummy zaune a  katafaren Palour'n Daddy dake cikin b'angarenshi, suna tattauna batun Auren Ya Abir da Khairat inda aka saka ranar aurensu nan da wata d'aya, wanda hakan yasa nan da nan Ya Abir yaji kamar an buga mashi wani gundumemen abu a tsakiyar kai nan take ya ji numfashin shi na bid'ar d'aukewa wanda hakan ya jawo hankalin kowa a gare shi da mamaki shimfid'e a fuskokinsu dan su a tunaninsu farin ciki ne zasu ga yana yi ba bak'in ciki ba  koda kuwa bai nuna hakan a zahiri ba yanayinshi zai nuna. Abba ne ya yi murmushi cikin kula ya ce "Abir a kwai wata matsala ne?.!" Cike da jin nauyin iyayen nashi ya d'an sosa k'eyar kanshi yana murmushin k'asa-k'asa ya ce "Abba ba komai!."  Abba Ya ce "Ban sanka da haka ba Abir idan a kwai wani abu ne ka fad'a muna tun wuri karka zo daga baya kana danasanin rashin fad'a muna damuwarka da ba kayi ba domin mu masu iya share ma hawayenka ne a ko wanne irin lokaci idan ka kawo muna kukanka.!" Su Daddy kam sai kallonsu suke sun kasa cewa ko uffan suna sauraren abinda zasu ji ya fad'a d'in kai tsaye Ya Abir ya ce "Abba dan Allah ku gafarce ni idan abinda zan fad'a  zai b'ata maku rai wlhy ko kad'an bada nufin na b'ata maku rai zan fad'i hakan ba.!" Cikin Mummy ne ya ce "K'ulululuuu." dan ita babban bak'in cikinta da jin kunyarta dik bai wuce ya ce ya fasa wannan auren ba. Daddy ya ce "Kayi magana mana muna saurarenka, amma ka sani idan har ya shafe wannan auren ne to ka k'addara kamar ma ba ka fad'i zancen ba ne domin babu fashi sai anyi shi.!" Cikin murmushin k'arfin hali irin nasu na manya Abba ya ce "Ba komai Abir ni kuma nayi maka alk'awarin koma mene ne za'ayi maka shi da yardar Allah.!" Ya Abir ya ce "Dan Allah ku gafarce ni Daddy wlhy ta wata fuskar ko kad'an bai shafe wannan auren ba amma ta wani fannin kuma kamar ya shafe wannan auren ne.!" Hantar Abba ce ta kad'a kamar zata fito waje dan ko shi baya son yaji ya ce wani abu game da wannan had'in da suke fatan yi masu ganin tsawon lokacin da aka kwasa ana jiran tafowar wannan lokacin, sannan Ya Abir ya k'ara da cewa "ba zance bana son Khairat ba! Ina sonta ko dan zumuncin dake tsakaninmu kasan cewar anyi wannan had'in ne tun bamu ida mallakar hankalin kanmu ba har ya zo izuwa yanzu wanda da hakan nake neman alfarma a gare ku da ku yafe man.!" sai da ya yi k'asa-k'asa da murya cikin kad'awar hanta sannan ya ce " dama  akwai wadda nake so na auren ne bayan Khairat kuma.............!" Tatassss yaji Daddy ya d'auke shi da wani wawan mari wanda sai da ya kai ga durk'ushewa k'asa, a fad'ace Daddy ya ce "Har ka isa! Ni zaka watsa ma k'asa a ido Abir! Ni!! da mutumci na a gari kana k'ok'arin zubda man shi a banza a wofi, to wallahi ka sani wannan auren ko kak'i ko kaso sai anyi shi kuma ba wanda ya isa ya hana faruwar hakan sai Allah.!"  Ran Abba shi ma ya kai mak'ura wajen b'aci sai dai bai yadda ya nuna hakan a fili ba cikin sassauta murya can k'asa-k'asa kamar mai mura ya ce "Abir mene ne dalilinka na son a fasa wannan auren?.!"  cikin duk'adda kai k'asa ya ce "Abba ba fasawa nake son ayi ba ina son a bani dama ne na aure wadda nake so Ita ma Khairat idan aka bincike ta watak'il tana da wanda take so ba ni ba dan Allah kar ayi muna au........! Mummy ce ta rufe shi da fad'a tun kan ya ida k'arasa zancen da yake, ta ce "Ashe kai baka da hankali ko kad'an! yanzu k'asa kake son ka watsa mana a idon duniya kenan! anya Abir! anya kuwa ka d'auke mu a matsayin iyayen da suka haife ka? anya  kana son ka gama da duniya lafiya Abir?.!" Cikin k'arfin hali Abba ya ce "Dik wannan bai kai ga hakan ba dan haka ku bawa zuciyarku salama, amma sai dai ina da tabbacin Khairat ba wani wanda take so sama da kai Abir amma idan na fahimce ka so kake a had'a maka aurensu gabad'ai su biyun ko ba haka ba?". a fusace Daddy ya ce "Me! Kana nufin kai har ka kai munzalin da zaka iya rik'on mata biyu ne? To wlhy ban yarda ba dan ba zai tab'a yuwa ba wl.....!" Abba ne ya yi hanzarin katse masa hanzari wajen cewa "Karka rantse Mukhtar  mu bi komai a sannu dan Allah idan har muka ce muyi wa yaronnan hakan zamu cutar da shi ne kuma mu mun zalince kanmu domin dik abinda ya biyo baya mu ne za muyi fama.!" Daddy ya ce "ai gwara ya cutu da wannan bak'in fentin da yake son ya shafa muna a fuska.!" Abba ya ce "Ba wani bak'in Fenti ai ba haramun ba ne ko? sannan kuma shi yaga zai iya! fatanmu dai Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakaninsu! daman shi auren gida ya gadi hakan fatanmu a koda yaushe wannan auren ya zamo allhairi ne a gare mu baki d'aya sannan kai yarinyar da kake so 'yar ina ce?.!" shiru Ya Abir ya yi ba tare da ya ce da su ko k'ala ba yana nazarin yanda zai basu wannan amsar Daddy ya daka mashi tsawa ya ce "wai ba da kai ake ba ne.?"  A d'an firgice ya ce "Anan gidan take.!" Cikin Ya Bikhram ne ya mird'a wanda sai a sannan yaji ya neme abinda ke ma ranshi dad'i ya rasa. Daddy ya ce "Yaushe ka haukace haka Abir? cikin k'annen naka ne wad'anda kuke uwa d'aya uba d'aya kake so?.!"  a ladafce ya ce "a'a Daddy daman Fatima nake nufi!."  Nan take d'akin ya d'auki shiru na d'an wani lokaci ba wanda ya iya cewa komai domin jin wannan babban al'amarin dake son fasa masu kunnaye, da mamaki Abba ya ce "Daman kun dad'e da sasanta junanku ne?.!" Ya ce "a'a Abba bata ma san ina sonta ba.!" Daddy ya ce "Ok auren dole kake son ayi mata kenan?." Ya ce "ba haka ba ne Daddy amma ina da tabbacin idan aka gaya mata ba zata k'ini ba.!" Daddy ya ce "Waye d'an aiken naka?." shiru Abir ya yi baice komai ba Mummy ta ce "ita da bakinta ne ta gaya maka hakan?." Abba ya ce "Shi ke nan Allah ya kai mu lokacin sai a gama gabad'ai ayi komai lokaci guda idan ya so sai a kira Kakarta a sanar mata domin na san ba zata k'i amincewa da wannan buk'atar ba.!" sannan ya dubi Ya Abir ya ce "bayan wannan kuma sai me.?" cikin mugun jin nauyinshi  da yake jin yana taso mashi ya ce " Taimakon da nake nema a gare ku dan Allah kar a sanarwa da kowa wannan zancen.!" Abba ya ce "Ko mene ne dalilinka?." Ya ce daman ina gudun abinda zai biyo baya ne.!" Daddy ya ce "ai koma mene ne zai biyo bayan ya riga ya faru sai dai Allah yasa hakan shi yafi alkhairi amma ka sani ba wai na k'yale ka ba ne tukunna ka jira hukuncin da zan maka.!" Abba ya ce "shi ke nan, Allah ya kai mu  lokacin.!" kowa ya amsa da Amin sannan aka watse taron da addu'a kowa ya tashi rai a jagule musamman Abba da yake ganin kamar anci mutumcin d'iyarshi ne, sai kuma Daddy da yake jin dan d'e ba yanda ya iya ne dan ba zai iya cewa a'a ba ko dan sabida Mummy da kuma kunyar dake tsakaninshi da Kaka Ya Bikhram kuma tunda ya baro wajen bai sake cewa ko uffan ba jiri ne kawai ke famar d'aukarshi kamar wanda ya shawu da Barasa wanda yana shiga d'akinshi ya saka key ya kulle daganan ya fad'a saman lallausan gadonshi zuciyarshi na bid'ar zazzagowa waje, a b'angaren Mummy kuwa farin ciki ne k'all a cikin zuciyarta sai dai bata nuna hakan a fili ba domin ta dad'e tana fatan hakan sai dai bada Ya Abir ba sabida ta san maganar aurenshi da Khairat na nan bata mutu ba amma ko da hakan dai tayi fatan wannan abin ya zamo alkhairi a gare su baki d'aya har ta isa part d'in Kaka farin ciki take. Ya Abir kuwa har Nafila raka'a biyu ya yi  ya godewa Allah akan farin cikin kasancewar wannan abin. Ko da Mummy ta isa part d'in Kaka ta cimma Fatima zaune a saman K'afafuwanta tana mata tausa, da murmushi irin nasu manyan mata Mummy ta ida karasawa ciki tana dariya ta ce "Yanzu tausar ma dan za'ayi ma Kaka sai an hau k'afafuwanta.?" Kaka kam daman an tab'o mata inda yake mata k'aik'ayi ta ce "Ke ko dik ba cikin salon shairi ba ne! a dai karya ni a kaini a baro dan an gaji da ganin ina tafiya da su! ko a dorin ma ya aka k'are balanta yanzu da tsufa ya fara kama ni.!"  Mummy dariya kawai take tana kallo na da dik na wani tamke fuska dan na gaji sosai kuma Kaka tak'i bari na tashi Mummy ta ce "Kinga d'iya ta tashi kiyi tafiyarki kinji k'yale Kaka.!" ai ko daman a matse nake nayi zubun na mik'e a hanzarce na bar d'akin ina yiwa Kaka gwalo, saki da baki ta bini da kallo har na wazge ta ce "Kinga wata hauka kuma? hmm Allah dai ya shirya min ita dan har yanzu wlhy ta kasa hankali.!" Mummy tayi dariya ta ce "ai shi ne yarintar Hajiya.!" sannan ta neme waje ta zauna a dai-dai lokacin da take cewa "Daman Hajiya wata magana ce nazo mud'an tattauna mai muhimmanci.!"  cikin bada aron kunnayenta biyu a wajen Mummy kai tsaye ta ce "To ina jinki.!" nan dai Mummy ta kwashe komai ta sanar da ita sannan ta k'ara da cewa "Yanzu mene ne shawara Hajiya?." Kaka ta ce "shi ke nan ba wata shawara Allah yasa hakan shi yafi alkhairi amma ni dai naso abarta har ta gama karatun tukunna idan maganar auren za'ayi ko bayan ta samu aiki ne ba sai ayi ba.?" Mummy ta d'anyi murmushi sannan ta ce "ai Hajiya ko bayan anyi auren ne zata iya ci gaba da karatunta sannan ni a gani na ai auren gida yafi na waje ko.?" Kaka ta ce "Eh to maganarki gaskiya ce musamman ma idan ya yi dad'i! amma kuma kina ganin hakan za'ayi auren ita bata ma sani ba kina ganin ba wata matsala?." Mumny ta ce "Gaskiya ni ma nayi tunanin hakan amma za muyi tunani akan hakan.!" Kaka ta ce "To Allah ya yarda.!" Mummy ta ce "Ameen.!" bayan sun gama shawarwarinsu Mummy ta baro wajen Kaka ta barta cike da zancen zucin da take, a zahiri Kaka ko kad'an bata ji dad'in wannan had'in ba sai dai babu yanda ta iya illa ta aminta da hakan domin ko banza duka jikokinta ne idan hakan ta kasance zata fi kowa jin dad'i dan ba'abar gida ba kamar yanda Mummy ta fad'a, kuma tana mugun jin nauyin Daddy dan ya gama mata komai a duniya, haka dai tayi ta tunane-tunanenta har dai ta godewa Allah. b'angaren su Ammie kuwa farin ciki a wajensu kam baya misiltuwa har an fara kiran k'awaye ana sanar da su batun auren  nan da wata d'aya ne. wajensu Mummy  su ma ba abinda ake sama da farin cikin sai dai har yanzu ba wanda aka bari yasan da batun aure Fatima haka kowa ya dake ya zurawa sarautar Allah ido. Ya Bikhram kuwa yau ciwo gobe lafiya an kasa gane inda kan matsalar take domin yak'i nunawa balantana ayi gaggawar kai shi asibiti. a wata ranar talata ce kowa yana zaune a Palour'n ana tattauna batun auren Ya Abir saura sati d'aya ya rage inda dik wani shirye-shiryen da ya kamata ayi an gama harda lefen da za'a kai nan da kwana hud'u masu zuwa domin za'a biya sadakin ne a ranar d'aurin auren, akwatuna set biyu aka sayo sannan dik abinda ke cikin set d'aya akwai shi a cikin d'ayan, wanda hakan yasa set d'ayan ba a bari kowa ya ganshi ba kai tsaye d'akin Mummy aka ajiye shi. Ya Bikhram ne zaune a saman d'ayar kujerar dake cikin jerin had'ad'd'in kujerun dake cikin babban palour'n, ya d'an gincira kanshi kad'an a saman kan kujerar yana tunanin damuwar da ta gagara ya yiwa kanshi maganinta, nan take yaji numfashin shi ya fara sarkewa wanda kai tsaye yaji ya fara twari a fujajun jini na fitowa ta hancinshi da cikin bakinshi wanda hakan ba k'aramin tashin hankali ya jefa kowa a gidan ba, aka kinkime shi aka nufi Asibiti da shi inda kai tsaye aka shiga bashi taimakon gaggawa bayan kamar 3hour's aka samu nasarar shawo kan matsalar sannan aka canza mashi d'aki da zaya zauna. Office d'in Doctor Daddy da Abba suka bayya anan Doctor yake shaida masu Ya Bikhram na fama da matsalar ciwon zuciya ne sannan jininshi ya hau sosai wanda da ace basu yi saurin kawo shi Asibitin ba da tuni an rasa shi............!"
"Ina yi ma d'aukacin al-ummar musulmi barka da sallah Allah Ubangiji ya maimaita muna Ameen ya rabbi.!"
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*#Be smart*
*^Pls shere^*

'YAR BALLAJJA'UTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang