*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**P...18*
"Aunty Khairat! Yanzu menene mafita? wlhy Ni yanzu dik wata Idea da nake tak'ama da ita ta k'are musamman idan assirin mu ya tonu wlhy ban san yanda zamu yi ba!."
"Hmm kina ganin Ni zan yi shiru ne in zurawa abin ido ba tare da na nema muna mafita ba? ai tunda na ce sai nayi to sai nayi d'in Ni dai abin da nake so a gare ki shi ne, ki kwantar da hankalin ki kar wannan d'an k'aramin abin ya razanar da ke Ni nasan abin da zan yi, bara ma kiga na kira Ammie ta.!"
"To" kawai Aunty Intisar ta iya cewa da ita, tare da komawa gefe ta tsaya kamar wajen da aka dasa Icce, dan ita dik tashin hankalinta bai wuce na dukan da zata sha a wajen Ya Abir ba domin bata tab'a kawo abin a ranta ba sai da mai afkuwa ta afku.
Kira guda kafin ta kaiga tsinkewa Ammie ta d'auki wayar, cike da shagwab'a ta shiga gaida mahaifiyar ta kafin ta soma fad'a mata cewa,
Yanzu ta kashe wata!Tsaki Ammie ta fara yi kafin ta soma ce mata wani abu cikin nuna halin ko in kula, ba tare da ta tsaya tambaye yanda abin ya ke ba, ta ce "To miye a ciki dan kin kashe wata marar amfani, lokacinta ne ya yi, Idan iyayen yarinyar sun buk'ace a biya su Diya su zo a shirye muke da mu biya, shin tukunna ma ita 'yar gidan uban waye ko kuma ita 'yar gidan wanne shege ne a fad'in k'asar nan?"
Ta ce "Ba kowa bace illa Agolar da Mummy'n Ya Abir ta d'auko daga wajen Mahaifiyar su.!"Tsaki kawai Ammie ta iya ja kafin ta ce "Ki kwantar da hankalin ki kici gaba da harkar da ta shafeki kibar ni da shegunan banza.!"
Tana gama fad'in hakan, kit ta yanke kiran~~~~~
Yana isa Asibiti, direct aka wuce da ita a Emergency room tare da bata wata kyakkyawar kulawa sai dai ko kad'an abin bai zo da sauk'i kamar yanda ake fata ba.
....
Bayan Gwaggo Talatuwa ta taimaka mata taje d'aki kai tsaye ta ce "Dan Allah Talatu taimaka ki miko man salula ta na kira Maman Fadil"
(cewa da Mummy Balkisu),
Bugu guda ta d'auka tare da yin sallama, bayan sun gama gaisawa ne harda su Yumra cikin farin ciki ba tare da wata damuwa ba wanda hakan ba k'aramin kwantar mata da hankali Ya yi ba sai dai lokaci guda kuma taji hankalin ta ya k'ara tashi tunawa da bata ji muryar Fatima a tare da su ba, nan take ta tambaye Mummy Balkisu Fatima, ta ce mata ai tana gida sun barta kwance tana bacci dan ba yanda ba tayi da ita ba akan ta biyo su ta ce ita tafi son ta zauna gida, sai a sannan Kaka taji hankalinta ya d'an kwanta, bayan sun ida k'ark'are wayar anan wajen da take tad'an gincira daga nan kuma sai ga wani hatsabibin b'arawon bacci ya kwankwasa mata k'ofa ta wangale mashi ita
Cike da mamaki Gwaggo Talatuwa ke kallonta ganin lokaci guda bacci ya zo ya yi awon gaba da ita ba tare da ta tsaya yi mata bayanin komai ba.A b'angaren Mummy kuwa kamar Kar Kaka ta mata maganar Fatima taji alamun jikinta na bata ba lafiya ba, lokaci guda ita ma taji gabanta ya soma fad'uwa, hankalin na bid'ar tashi, jikin ta na rawa kamar ta sulale k'asa anan wajen da take, nan take ta ce ma Direba ya koma da su gida............
Follow me on wattpad and vote—Smat_Feenert
#Be smart
Pls shere
![](https://img.wattpad.com/cover/215007905-288-k317588.jpg)
STAI LEGGENDO
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...