*—•@••«•»•@•«•»••@•—*
*'YAR BALLAJJA'U👩🏻🎤*
*—•«Start, on 23/2/2020»•—*
*Wattpad @Smart_Feenert*
*—•«•Be smart•»•—**_{🌺Yahoo- smartfeenert@yahoo.com🌺}_*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🍀BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM🍀*
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*—•@••«•»•@•«•»••@•—**P...25*
Bayan na baro wajen Kaka aguje anan babban Palour'n muka tashi yin kabra Ni da Aunty Khairat da shigowar ta kenan a cikin gidan
Wani wawan kallo ne ta fara jifa na da shi mai had'e da ruwan harara kamar wadda aka yi wa wani mugun abu
Ni ma yanda tayi man haka nayi mata tare da tab'e d'an k'aramin baki na na koma saman d'ai daga cikin kujerun alfarmar dake cikin Palour'n na zauna tare da aza k'afa d'aya saman d'aya ina karkad'awa had'i da bud'e waya ta ina dannar ta a hankali kamar mai tausayin screen d'in wayar kai tsaye what's app na ziyarta daganan na soma chatting da k'awaye na.
Wani irin k'ololon bakin ciki ne taji ya fara tokare mata a mak'ogoro wanda har take jin wahalar had'iye yawu,
cikin ran ta ta ce
"Wannan kuma tantiriyar fa daga ina?" Cikin sark'ewar numfashi ta ce "Fatima! Anyaa! daman haka ta koma? Ko dan na kwana biyu ne banzo gidan ba? butaddumen lallai wannan shegiyar yarinyar ta wuce dik yanda Intisar ke man misalin ta a waya ko idan mun had'u a skull! Indai haka ne kam wlhy ya zama dole in nema ma kaina mafita akanta domin idan har nayi wasa zata gama da ni ne bada jimawa ba! Ohni Allah taya za'ayi na iya samun kwanciyar hankali a yanzu ina ganin ta a raye tana yand............!"
Wata raki'ar dariya ce da taji na b'arke da ita lokaci guda ya sake dawo da hankalin ta wajen dik da tun d'azun idanuwan ta na a kai na kamar ta had'iye ni.
Tsaki ta fara ja kafin ta ce "hohohoo! Dad'in abin dai arzikin uban wani ne ake ci ana moruwa! Lallai kam ni naga k'ok'arin su da har suka iya maida bak'auyen mutum wanda in banda bolin kwance da k'azantar bacci cikin datti da k'azamtar rashin wanka da wanki da kuma cin k'azamin tuwon dawa da miyar daddawa mai kama da kashin Jak......!"
Maganar da taji a bayanta ne tayi hanzarin dak'ile mata dik wani kuzarin da take tak'amar tana da shi wajen ci gaba ba zancen da take ganin dan ta isa ne take yin shi
Kaka ce tsaye rik'e da zangarneniyar bulalar dokin ta a hannu wanda daman ta biyo baya na ne da niyyar idan ta samu nasarar kama ni ta auna man ita a jiki kamar yanda take k'ok'arin bani tsoro da ita a dik sanda nayi wata tijara sai dai ko da hakan kuma ba duka na ake yi da ita ba hasali ma zance ko farcen hannu na wannan bulalar bata tab'a tab'awa ba domin da zarar ta biyo ni da ita a guje taga na shige cikin d'aki na kulle to daga wannan lokacin an wuce wajen, su Mummy suyi ta dariya
Tsaye take tun lokacin da Khairat ta fara cin mutumcin ta tana sauraren dik abin da take fad'a har aka kai lokacin da taga ba zata iya daurewa ba ta tamka mata da cewa
"Ke kuma baiwar Allah da ke da waye haka? kin shigo ma mutane gida ko sallama babu!."
Wata irin mugunyar dariya ce Khairat ta fara kecewa da ita kafin ta soma d'aga hannun ta guda sukutun sama tana nunawa Kaka da shi cikin wata arniyar dariya mai cike da soyayyen raini tank'il a cikin ta take cewa "Su waye masu gidan?. A ina suke? Ni fa banga kowa ba! aww srry fa ko kece sabuwar 'yar aikin da aka d'auko masu ban sani ba, sai dai nayi mamaki da har aka samu ballagazar tsohuwa irin ki wadda taga jiya taga yau wajen kawalc..........!"
Wani irin wawan Mari ne da taji anyi k'arfin halin d'auke ta da shi wanda taji zuwan shi a bazata har sai da ta tashi fad'uwa k'asa akan azaba tare da ganin wani kafurin haske b'auuu a cikin kwayar idanuwanta mai had'e da shaud'in walk'iyar bulalar shed'an a cikin shi aiko bata san lokacin da ta sake wata irin razananniyar k'ara ba wadda sai da tayi sanadiyyar fitowar mutanen gidan gabad'ai a wajen dan ganin abin da ke faruwa kasan cewar sun razana sosai da jin wannan irin ihun.
Mummy ce da taga Kaka tsaye a sandare imani dik yabi ya addabi rayuwar ta sannan ta dubi wajen da Fatima ke tsaye kusa da Khairat da har yanzu bata sauke hannun ta a k'asa daga marin da tayi mata ba
Kafin Ammie ta soma tambayar abin da ke faruwa tuni Na soma magana cikin mugun d'aga murya nake cewa "Ya kika ji ne Khairat? Da zafi ko? ko babu zafin ne? Ina fatan yanzu dai kinji yanda rainon k'auye yake ko? Kuma kinji yanda tuwon dawan da miyar daddawa ke da matuk'ar amfani a jikin bak'auye! Ba zan damu ba dan kin ce nazo gidan uban wani ina cin arziki ba tunda ni dai nasan ba shegiya ba ce ta hanyar sunna aka same ni kuma dik yanda mahaifina yake ina matuk'ar alfahari da shi a hakan sannan warning d'ina na k'arshe da zan maki anan shi ne! Wlhy! wlhy! dik ki ka sake zagar min Kakar da take tamkar mahaifiya a gareni wlhy summa tallahi girman ki ko matsinyin ki na babba a gare ni ba zasu tab'a bani tsoro ba.!"
Ina gama fad'in hakan naja komotstse na na koma d'aki na a zuciye na saka key na kulle nayi kwanciya ta a saman lafiyayyen gado na ina furzar da wani zazzafan iska a baki.
Kaka kam tsaye kawai take tana matsar kwalla maganganun da Khairat ta gaya mata sai dawo mata suke a kai ta kasa mantawa da su.
A fusace Mummy tayo wajen Khairat tana mata fad'a ta ce "A she ba kya da kirki Khairat! Mahaifiyar tawa ce abin zagi? Yaushe kika zama haka Khairat?.!"
Ba tare da ta tsaya jim amsar da Khairat zata bata ba taja Kaka suka koma part d'in ta a hasale tana lallashin ta
Yumra kam tsaki kawai ta iya ja kafin tayi yunk'urin komawa cikin d'akin su a fusace, Yubra kuma dariya ta fara kecewa da ita sannan ta shiga kwaikwaiyon ihun da Aunty Khairat tayi a d'azun tare da yi mata gwalo sannan ta rufa ma su Mummy baya
Aunty Intisar kuwa wajen da Khairat ke tsaye rik'e da kunce a tafin hannu ta nufa tare da nuna zallar damuwar ta ga abin
Murmushi mai cike da kunar zuciya Khairat tayi kafin ta shafo fuskar ta da tafin hannunta ta ce "Hmmm! Fatima ba dai ni kika Mara da wannan k'azamin hannun naki ba ko? lallai kin isa har ma kin wuce! sai dai wlhy ni kuma nayi maki alk'awarin yau-yau dinnan sai kinyi nadamar abin da ki ka aikata a gare ni kuma sai kin gane cewa ruwa ba sa'ar kwando ba ne.!"
Cikin isa ta dubi wajen da Intisar ke tsaye ta ce "Intisar!"
Ta ce "Na'am Aunty.!"
Ta ce "Ki zama shaida! idan har yau ban lalata ma wannan k'azamar yarinyar rayuwa ba ni ban cika 'yar halak ba.!"
Aunty Intisar ta ce "Ina bayan ki d'ari bisa d'ari wlhy.!"
Ba tare da Khairat ta sake cewa da ita ko k'ala ba ta nufi hanyar barin d'akin gabadai kai tsaye wajen da tayi parkin d'in Motarta ta nufa.Ta b'angaren Kaka kuwa lallashi ba irin wanda Mummy bata mata ba amma fir tak'i hak'ura ta ce ita lalala azimun anci mutumcin ta dana jikar ta dan haka yau Sokoto zasu kwana ba zasu sake waiwayar su ba tun da aka zage ta aka yi ma jikarta gori, da k'yar dai da walahaula tare da saka bakin Daddy wajen dannar zuciyarta har aka samu aka shawo kan al'amarin sannan ta hak'ura.
Ni ma tun lokacin da na kwanta a saman lafiyayyen gado na ban san lokacin da babban b'arawonnan bacci ya yi awon gaba da ni baAunty Khairat kuwa bayan ta koma gida ta kwashe komai ta gayawa Ammie dik abin da ya faru har da marin da nayi mata
Fushi kam ba'a ma maganar irin wanda Ammie tayi sosai har na fitar arziki sannan daga baya ta bawa zuciyarta ruwan sanyi ta yanke shawarar lalabo wayar ta domin ta kira Mummy ta bata hak'uri akan abin da ya faru wanda hakan yana d'ai daga cikin shirin ta da take k'ok'arin aikatawa
Kira guda Mummy ta d'auka bayan sun yi sallama mai cike da gaisuwa Ammie ta shiga bata hak'urin abin da Khairat tayi wa Mahaifiyar ta, sosai dai Mummy ta gamsu da hak'urin da Ammie take bata wanda har tana jin ita komai ya wuce a gurin ta dan ya yi matuk'ar gamsar da ita sosai
Bayan sunyi sallama ne Ammie ta kashe wayar cikin murmushin ta na mugunta ta mayar da hankalin ta ga 'yarta dake k'ok'arin kiran waya tun d'azu
Ta ce "Yanzu kinga na gama da wannan babbar munafukar ko da wani abu marar kyau ya faru ba zata tab'a zargin mu ba domin hankalin ta kwata-kwata ba zai kawo mata mu a rai ba! Yanzu abin da ya rage muna shi ne mu tashi muje wajen su Bobi kiji yanda wasar zata fara.!"
Cike da wani hamshak'in farin ciki Khairat ta ce "Ammie kinga fa hankali na dik bai kawo su a rai ba.!"
Ammie ta ce "Ai hankalin babba da yaro ba guda ba Baby.!".......
A wata babbar Majalisar su ta tantiran 'yan daba suka samu wasu 'yan iskan gayu zazzau a saman wata babbar tabarma ko wannen su ya sha mugun askinnan har ga mugun waje irin na tantiran 'yan iska ajin farko, wasu daga cikin su kuwa sai famar zuk'ar Sigari suke suna fidda hayak'i ta ko ina daga cikin bakin su da kuma cikin hantunan su inda kuma wasu daga cikin su su kayi likimo a kwakkwance a wajen domin giyar da suka sha har tafi k'arfin jikin su.
Gefe guda su Ammie suka samu suka tsaya suna kallon su ido da ido lokaci guda d'ai daga cikin su wanda ake tunanin shi ne babban gabad'ai a wajen ya taso ya yo wajen da su Ammie suke fuskar shi d'aure babu alamun rahama a cikin ta Kai tsaye ce masu ya yi "Me ke tafe da ku?.!"
Ba tare da wani b'ata lokaci ba Ammie ta ce "wani gagarumin aiki ne nake son kuyi man a cikin daren nan idan kuna da lokaci dan bana son ya wuce yau-yau d'innan!."
_Gare ku my What's app fan's wlhy rashin ganin cmments d'in ku kamar yanda ya kamata shi ke dak'ile man dik wani kuzarin yi maku Typing kullum ina fatan zaku gyara Fan's idan har kuna son ni ma na gyara maku_
Na gode!!!
*Follow me on wattpad and vote—Smart_Feenert*
*#Be smart*
*^Pls shere^*

YOU ARE READING
'YAR BALLAJJA'U
FantasySai da na kyakyace ko waccen su tayi muii da bakin ta alamun bacci yadan fara satar su Ni kuma sun barni da haushin su a rai. Na sauko daga saman gadon a zuciye da niyyar barin dakin tun da an bata man rai, sai jin nayi Kaka na fadin...